Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA

 

A KAN

 

KOYARWAR ALKUR’ANI DA SUNNAH

 

BISA

 

 

FAHIMTAR MAGABATA NA KWARAI

 

 

Littafi na daya (bugu na biyu)

 

Na

 

SHAIKH ABDULWAHAB BIN ABDILLAH

Majalisin Ahlus-Sunnah Wal-Jama’ah

Masallacin Ibn Taymiyyah

Sharada Phase II, Kano-Nigeria

mimbarilislam.tripod.com

 

FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA

 

A KAN

 

KOYARWAR ALKUR’ANI DA SUNNAH

 

BISA

 

 

FAHIMTAR MAGABATA NA KWARAI

 

 

Littafi na daya (bugu na biyu)

 

Na

 

SHAIKH ABDULWAHAB BIN ABDILLAH

 

 

Majalisar Koli ta tabbatar da Shari’a a Nijeriya

ta dauki nauyin bugawa

 

ABUBUWAN DA KE CIKI

MuKaddimar bugu na biyu

MuKaddimar bugu na daya

1. Tambaya: Menene ma’anar Hajji?

2. Tambaya: Menene falalar aikin Hajji?

3. Tambaya: Yaushe aikin Hajji yake wajaba a kan mutum?

4. Tambaya: Shin wajibi ne ga wanda Allah Ya bai wa damar zuwa aikin Hajji ya gaggauta tafiya ko kuwa zai iya jinkirtawa zuwa wani lokaci?

5. Tambaya: Menene hukuncin wanda Allah Ya ba shi damar zuwa aikin Hajji, amma ya yi sakaci bai je ba?

6. Tambaya: Shin wanda ya mutu bai samu damar yin aikin Hajji ba, za a iya yi masa?

7. Tambaya: Shin ya halatta a biya wa jama'a Hajji da kudin da aka sata daga aljihun gwamnati ko kudin haram, kamar riba ko kudin giya?

8. Tambaya: Me ya kamata maniyyaci ya fara yi kafin tafiya?

9. Tambaya: Mutumin da Allah Ya ba shi ikon zuwa Hajji, amma iyayensa ba su yi ba, shin zai fara gabatar da su ne ko kuwa shi zai fara zuwa?

10. Tambaya: Mutumin da ya dauki adashi zai iya zuwa aikin Hajji da shi kafin ya biya sauran zubin da yake kansa?

11. Tambaya: Shin mace mai takaba ko iddah za ta iya zuwa aikin Hajji?

12. Tambaya: Yaushe ne maniyyaci zai dauki niyyar aikin Hajji, kuma a ina zai dauka?

13. Tambaya: Menene ma’anar talbiyya?

14. Tambaya: Shin mata za su yi talbiyya?

15. Tambaya: Menene sunnonin ihrami?

16. Tambaya: Me ya kamata mai ihrami ya guji aikatawa yayin da yake cikin ihrami?

17. Tambaya: Wadanne miKatai ne Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya iyakance wa mutanen duniya?

18. Tambaya: Menene hukuncin wanda ya Ketare miKatinsa ba tare da ya yi niyya ba?

19. Tambaya: Aikin Hajji ya kasu kashi nawa ne?

20. Tambaya: Yaya ake yin Umrah?

21. Tambaya: Menene aikin Hajji ya Kunsa?

22. Tambaya: Daga ina ake fara dawafi? Kuma a cikin Kusurwoyin Ka’aba ina ne ake sumbanta, kuma ina ne ake shafa?

23. Tambaya: Shin ko akwai addu’ar da aka kebance mai dawafi ya yi?

24. Tambaya: Idan mutum ya yi kokwanton adadin dawafinsa, yaya zai yi?

25. Tambaya: Shin akwai wani dawafi da ake kira bakwai sau bakwai domin neman biyan buKata?

26. Tambaya: Idan mutum ya yi salla raka'a biyu a bayan maKama Ibrahim, sai ya tuna dawafinsa bai cika ba, yaya zai yi?

27. Tambaya: Idan aka fara salla alhali mutum yana dawafi yaya zai yi?

28. Tambaya: Menene hukuncin wanda alwalarsa ta karye alhalin yana dawafi?

29. Tambaya: Wadanne addu'o’i ne suka tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yayin Safa da Marwa?

30. Tambaya: Wace irin ibada ce ya kamata mahajjaci ya shagaltu da ita ranar Arfa?

31. Tambaya: Wace irin ibada ya kamata a shagaltu da ita a Muzdalifa?

32. Tambaya: wadanne irin ayyuka a ke yi a ranar idi, bayan an bar Muzdalifa zuwa Mina?

33. Tambaya: Wace irin ibada ya kamata mahajjaci ya yi a kwanakin Mina bayan salla? Kuma me ya kamata mahajjaci ya nisanta?

34. Tambaya: Menene hukuncin matar da ba ta yi dawaful Ifadha ba saboda wani uzuri ga shi kuma jirginsu zai tashi?

35. Tambaya: Wane tanadi Shari’a ta yi game da ziyarar Madina, birnin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam)?

36. Tambaya: Menene hukuncin wanda ya isa Jidda, amma hukumar Sa’udiiyya ta hana shi shiga Makka, saboda wani dalili ko kasancewar garinsu ana annoba?

37. Tambaya: wadanne irin nasihohi za a yi wa hukumomin alhazai da su kansu alhazai?

 

 

MUKADDIMAR BUGU NA BIYU

Bismillahi, Wassalatu wassalamu ala Rasulillah, wa ala Alihi wa Sahbihi wa man Walahu.

Bayan haka:

Tun lokacin da aka buga littafin Fatawowin aikin Hajji da Umrah da Ziyara na babban malaminmu Shaikh Abdul-Wahhab ibn Abdillah ibn Muhammad, mutane sun yaba da zurfin binciken da aka yi da salon amsa tambayoyi da aka bi wajen ba da fatawoyin. Wannan ya sa buKatuwar littafin ga jama’a ta yawaita.

Kasancewar watan Zul-Hijjah na wannan shekarar na Kara kusantowa ne, muka ga dacewar a sake buga littafin don amfanin al’ummar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

Maimakon a buga shi kamar yadda yake a bugun farko, an ga dacewar a sake bibiyarsa don Kara kyautata shi. Wannan ya sa aka gyara tsarin rubutun da kurakuransa, ta yadda zai dace da salon rubutu na Hausa, kuma aka Kara wadansu mas’aloli, tare da tahaKiKin littafin baki daya.

Muna roKon Allah Ya sanya wa littafin albarka, kuma Ya Kara wa malam lafiya da sararin yin bincike da karantar da al’umma sahihiyar Sunnar Ma’aiki (Sallallahu alaihi Wasallam) bisa fahimtar magabata na Kwarai. Kuma Allah Ya albarkaci rayuwarsa da zuriyarsa da mu dalibansa, kuma Ya yafe mana kurakuranmu baki daya, amin.

Daga Karshe, muna godiya ga `yan’uwa da suka taimaka ta kowace hanya wajen tabbatar da wannan aiki, musamman Ahmad Bello Dogarawa da Imam Khidir Muhammad Bello da Kasim Muhammad Aminu da suka taimaka wajen bitar littafin da tsara rubutun Hausa da gyare-gyaren da suka dace a cikinsa.

daliban malam

Zul-Ka’adah 7, 1425

 

 

MUKADDIMAR BUGU NA dAYA

Dukan yabo da girmamawa sun tabbata ga Allah Ubangijin halitta. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam), wanda ya ce: "خذوا عني مناسككم" "KU RIKI (AYYUKAN) HAJJINKU DAGA GARE NI", da alayensa da sahabbansa, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka, wannan dan Karamin littafi ne da ya Kunshi fatawoyi game da aikin Hajji da Umrah, da Ziyarar masallacin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) da ke Madina. Littafin ya samu ne sakamakon KoKarin da Sheikh Abdul Wahab bn Abdallah bn Muhammad ya yi na amsa mana wadannan tambayoyi. Ganin fa’idar wannan aiki yasa muka ga muhimmancin mai da shi littafi, saboda buKatar da ake da ita ta fahimtar wannan ibada KarKashin koyarwar AlKur’ani da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bisa fahimtar magabata na Kwarai.

Muna roKon Allah (Subhanahu Wata’ala) Ya kyautata niyyarmu, Ya karba mana wannan aiki, Ya amfanar da al’ummar Musulmi da abin da ke cikinsa, kuma Ya yafe mana kura-kuran da muka yi na tuntuben harshe ko tuntuben alKalami, Amin.

 

Wassalamu Alaikum Warahmatullah

 

 

daliban malam

Shawwal 1424 A.H

December 2003 A.C

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

بسم الله الر حمن الر حيم و صل الله على النبي الكريم

1. Tambaya: Menene ma’anar Hajji?

Amsa: Ma’anar Hajji a harshen Larabci shi ne nufin wani abu. Amma ma’anar Hajji a shari’ance shi ne nufin ziyarar dakin Allah (ka’aba), bisa girmamawa, da wasu kebantattun ayyuka (na ibada), a kebantaccen lokaci, kuma a wani kebantaccen wuri

 

2. Tambaya: Menene falalar aikin Hajji?

Amsa: Aikin Hajji yana da falala da yawa. Kadan daga ciki shi ne:

· An karbo Hadisi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Aikin Umrah zuwa wata umrar, yana KanKare zunuban da ke tsakaninsu. Haka kuma Hajji Mabrur , ba shi da sakamako sai aljanna".

· Haka kuma an karbo Hadisi daga Ma'iz (Allah Ya yarda da shi) ya ce: An tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa: Wadanne ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce: "Imani da Allah Shi kadai, sa’an nan yaKi don daukaka addinin Allah, sa’an nan Hajjin da ya kubuta daga sabo, tsakanin Hajji mabrur da sauran ayyuka kuma, kamar tsakanin mahudar rana ce da mafadarta".

· A cikin wani Hadisin kuma, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Mai yaKi fisabilillahi, da mai aikin Hajji da mai Umrah dukaninsu tawagar (baKin) Allah ne. Allah ne Ya kira su, kuma suka amsa ma Sa, kuma suka roKe Shi, Ya ba su"

· Haka nan, an karbo daga Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: Na tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam): Ya Ma’aikin Allah, shin ko Jihadi ya wajaba a kan mata? Sai ya ce: "Na'am, Mata suna jihadi, sai dai babu kisa a cikinsa; shi ne aikin Hajji da Umrah."

 

3. Tambaya: Yaushe aikin Hajji yake wajaba a kan mutum?

Amsa: Aikin Hajji yana wajaba ne a kan mutum, idan Allah Ya ba shi dama. Damar ita ce: dukiya, lafiya, amincin hanya da guzuri. Saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce:

ولله على النا س حج البيت من ا ستطا ع اليه سبيلا

Ma’ana: "Ubangiji ya wajabta Hajji ga mutane ga wanda ya samu ikon zuwa a gareshi"

 

4. Tambaya: Shin wajibi ne ga wanda Allah Ya ba shi damar zuwa aikin Hajji ya gaggauta tafiya ko kuwa zai iya jinkirtawa zuwa wani lokaci?

Amsa: HaKiKa wanda Allah Ta’ala Ya ba shi damar aikin Hajji, wajibi ne ya gaggauta tafiya matuKar babu wani uzuri da zai hana shi. Kuma ko da yake an samu sabanin malamai a kan haka, amma wannan shi ne abin da mafi rinjayen malamai suka tafi a kai. Daga cikin sahabbai da suka tafi a kan haka akwai Abdullahi bn Abbas da Abdullahi bn Umar (Allah ya yarda da su). Haka ma Imam Malik da Imam Ahmad da Imam Abu Hanifa da Abu Yusuf duk sun tafi a kai. Ko da yake Imam Malik yana da fatawoyi guda biyu, amma wannan ita ce mafi rinjaye. Dalili kuwa shi ne fadin Allah Ta'ala:

"Ku yi gaggauwa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku …" Da kuma fadarSa: "Kuma ku yi tsere ga ayyukan alheri ,,,"

Kuma Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn Abbas (Allah Ya yarda da shi) daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Wanda duk ya yi nufin tafiya Hajji, to ya gaggauta. HaKiKa rashin lafiya zai iya samunsa ko wata buKata ta bijirro masa." A cikin wata ruwayar, Ibn Abbas ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Ku gaggauta zuwa Hajji (na farilla); haKiKa daya daga cikinku bai san me zai bijiro masa ba."

Wadannan Ayoyi da Hadisi da muka kawo ne ke nassanta gaggauta zuwa Hajji, musamman lafazin, ta yadda ya zo da umurni tare da kwadaitarwa.

 

5. Tambaya: Menene hukuncin wanda Allah Ya ba shi damar zuwa aikin Hajji, amma ya yi sakaci bai je ba?

Amsa: Wanda ya yi sakaci bai je aikin Hajji ba, bayan Allah Ta’ala Ya ba shi wadata, haKiKa ya saba wa Allah, kuma ya yi sakaci a kan rukunin da Allah Ya wajabta masa. Saboda haka, akwai narko a kansa idan har ajali ya zo masa a wannan hali. Dalili kuwa shi ne fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin littafinSa:

"… Kuma wanda ya kafirta, to lallai Allah Mawadaci ne daga barin talikai."

Wannan shi ne abin da Allah Ta’ala Ya fada, bayan Ya yi bayani a kan wajibcin aikin Hajji.

 

Haka kuma an karbo Hadisi daga Abdullahi bn Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Ku nemi jin dadin (bauta wa Allah) da wannan dakin: haKiKa an rushe shi sau biyu, kuma a na ukun za a dauke shi."

 

6. Tambaya: Shin wanda ya mutu bai samu damar yin aikin Hajji ba, za a iya yin masa?

Amsa: Na'am, haKiKa za a iya yin masa, ba tare da wani sharadi ba, ko ya bar wasiyya ko bai bari ba. Dalili kuwa shi ne an karbo Hadisi daga Abdullahi bn Abbas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: HaKiKa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa: "Labbaika an Shubrumah", wato yana daukar niyyar Hajji ga dan’uwansa da ya mutu, mai suna Shubrumah. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Wanene Shubrumah? Sai ya ce: dan’uwana ne ko Makusancina ne. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya sake tambayarsa: Kai ka taba yin Hajji? Sai ya ce: ban taba yi ba. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Ka fara yi wa kanka, sa’an nan ka yi wa Shubrumah."

Wannan Hadisi ya nuna cewa, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai tambaye shi ko Shubrumah ya bar wasiyya ko bai bari ba. Sharadin kawai shi ne, lallai ne wanda zai yi wa mamaci aikin Hajji, ya kasance ya fara yi wa kansa.

Haka nan, duk mutumin da ba shi da lafiya ko tsufa ta zo masa, kuma ya samu dama ta dukiya, amma ba zai iya yin aikin Hajji ba, kuma ba zai iya zama a kan abin hawa ba, za a iya yin masa. Dalili kuwa na cikin Hadisin da aka ruwaito daga Abdullahi bn Abbas (Allah Ya yarda da su) cewa wata mace ta zo tana tambayar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) a kan aikin Hajji. A cikin Hadisin, ta ce: An farlanta aikin Hajji alhalin tsufa ta zo wa babana, kuma ba zai iya tabbata a kan abin hawa ba, shin ko na iya yin masa? Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: Eh! Za ki iya yin masa."

Wannan na nuna sauKin Musulunci da tausayawarsa ga wadanda tsufa ko rashin lafiya ya hana su aikin Hajji.

 

7. Tambaya: Shin ya halasta a biya wa jama’a Hajji da kudin da aka sata (kamar daga aljihun gwamnati) ko kudin haram (kamar riba ko kudin giya)?

Amsa: Bai halasta ba, saboda fadin Allah Ta’ala:

يا ايها الذين ءامنوا كلوا من طيبت ما رزقنا كم واشكروا لله ان كنتم ايا ه تعبد ون

"Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga dadadan (abubuwan) da Muka azurta ku (da shi), kuma ku gode wa Allah idan kun kasance Shi kuke bauta wa."

Haka kuma an karbo daga Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "HaKiKa Allah Ta’ala Mai tsarki ne, ba Ya karba, sai mai tsarki. HaKiKa Allah Ya umurci Muminai da abin da Ya umurci Manzanni da shi; Ya ce: "Ya ku Manzanni! Ku ci daga dadada, kuma ku yi aiki nagari… A Karshen Hadisin, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ambaci wani mutum matafiyi, yana daga hannayensa (zuwa) sama, (yana addu'a), alhali abincinsa (daga) haram ne, abin shansa (daga) haram ne, tufafinsa (daga) haram ne, kuma an ciyar da shi da haram." Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Ya ya za a karbi addu’arsa."

HaKiKa addu'ar matafiyi karbabbiya ce. Amma a cikin wannan Hadisi Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya nuna ba za a karbi addu’arsa ba saboda cin haram. Domin haka, idan mutum ya yi aikin Hajji da dukiyar haram, Hajjinsa ba karbabbe ba ne. Wallahu A'alam.

Amma akwai wadansu malamai, da son zuciya ya sa suke ba da fatawar cewa, mutum zai iya satar kudin hukuma, ya yi aikin alheri da shi. Wadannan malamai ba su da wani dalili a cikin littafin Allah ko Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

Sai dai kuma shugaba mai adalci, wanda baitul-mali ke hannunsa, zai iya amfani da wani bangare na kudin da aka tanada don tsaron shugaba ko alawus ko sallamar baKi ko daga cikin albashinsa, ya biya wa wadanda suka cancanta. Zai yi haka ne, ba tare da ya tauye haKKin talakawa ba, kamar yadda wadansu hukumomi ke barnatar da dukiyar al’umma wajen biya wa wadanda ba su cancanta ba, saboda manufa ta siyasa.

Ya kamata malamai su riKa fadakar da shugabanni game da hadarin amfani da dukiyar da Allah Ya sanya a hannunsu, ta hanyoyin da ba su dace ba. Malamai su tuna cewa ilmi da karantar da shi amana ce da Allah zai tambaye su a ranar Kiyama. Don haka, wajibi ne su zamanto masu fadin gaskiya ba tare da la’akari da jin dadi ko rashin jin dadin wani ba. Kuma lallai ne su tsare mutuncinsu, ba tare da yawon bin ofis-ofis don neman kujerar zuwa aikin Hajji ba.

8. Tambaya: Me ya kamata maniyyaci ya fara yi kafin tafiya?

Amsa: Abubuwan da maniyyaci ya kamata ya fara yi su ne:

1. Kyautata niyyarsa da ikhlasi, watau, ya Kudurta cewa zai je ya yi wannan ibada ce don neman yardarm Allah, ba don riya ko neman duniya ko son a sani ba.

2. Ya tabbatar dukiyar da zai yi aikin Hajji da ita ta halal ce.

3. Lallai ne ya nemi ilmin wannan ibada ta Hajji, domin ba a bauta wa Allah a cikin rashin sani.

4. Haka kuma lallai ne mutum ya nemi afuwa daga duk wanda ya san ya shiga haKKinsa, na mutunci ko na dukiya. Idan ana binsa bashi, ya yi KoKarin biya, ko ya nemi a yafe masa, ko kuma a yi masa lamuni har sai ya dawo.

5. Idan akwai abin da yake son yin wasiyya da shi, ya hanzarta yin hakan kafin ya tafi.

6. Sa’an nan kuma lallai ne ya nemi abokan tafiya na gari, wadanda zai koyi kyawawan dabi'u da ilmi daga gare su, domin kuwa zama da madaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.

7. Kuma ya sani cewa dukan mutanen da zai hadu da su a wajen aikin Hajji `yan’uwansa ne Musulmi. Domin haka, sai ya yi mu’amala mai kyau da su, tare da tausasawa da haKuri da rahama da afuwa gare su.

9. Tambaya: Mutumin da Allah Ya ba shi ikon da zai je aikin Hajji, amma iyayensa ba su yi ba, shin zai fara gabatar da su ne, ko kuwa shi zai fara zuwa?

Amsa: Shi zai fara sauke nauyin da ke kansa, saboda shi ne Allah Ya ba ikon, kuma Allah Ya wajabta aikin Hajji ne ga wanda ya samu iko. Bayan wannan, a cikin rukunan Musulunci guda biyar, babu wanda aka ce a fara gabatar da iyaye. Allah Ta’ala Ya ce:

ولله علي النا س حج البيت من استطا ع اليه سبيلا

"Kuma Allah Yana da haKKi a kan mutane na yin Hajjin daki, ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi…"

Saboda haka, idan mutun ya sauke farillarsa, babu wanda ya fi cancanta ya biya wa, kamar iyayensa. Amma idan Allah Ta’ala Ya ba shi halin tafiya tare da iyayensa, to sai su tafi gaba daya. Yin hakan, shi ya fi alheri.

 

10. Tambaya: Mutumin da ya dauki adashi, zai iya zuwa aikin Hajji da shi kafin ya biya sauran zubin da yake kansa?

Amsa: Na'am, zai iya zuwa aikin Hajji da shi, idan abokan adashin sun lamunce masa, kamar dai hukuncin wanda ake binsa bashi. Dalili shi ne, fadin Allah Ta’ala cewa ‘sai wanda yake da iko’ shi kuwa ba zai samu iko ba, har sai ma su binsa adashi ko bashi sun lamunce masa.

 

11. Tambaya: Shin ko mace mai takaba ko idda za ta iya zuwa aikin Hajji?

Amsa: A'a, bai halasta ba ga mace mai idda ko takaba ta tafi aikin Hajji, domin Shari'a ta umurce ta da lazimtar dakinta. Saboda haka, ba za ta fita ba, sai da larurar da Shari’a ta yarda da ita (kamar zuwa asibiti don neman magani, yin sana’a idan babu wanda ke daukar nauyinta, ko ziyarar iyaye da `yan’uwa).

Dalili kuwa shi ne abin da ya tabbata cewa Sayyadina Umar bn Khaddab da Uthman bn Affan (Allah Ya yarda da su) suna mayar da mata wadanda suka yi nufin tafiya Hajji, alhali suna cikin takaba, daga wurin da ake kira Baidaa., (don su koma) Madina. Haka nan, a cikin tabi’ai, Sa’idu bn Musayyib ya ba da fatawa da haka.

Amma akwai magana ta biyu da ake dangana ta ga Sayyidina Aliyu da Ibn Abbas da Jabir bn Abdullah da A’isha (Allah Ya yarda da su) cewa mai takaba ko idda za ta iya tafiya aikin Hajji ko Umrah. Har ma an samu cewa Nana A’isha ta fita zuwa Umrah tare da Kanwarta Ummu Kulthum, wadda ke yin takaba.

Shi kuwa Kasim bn Muhammad ya ce: "Mafi yawan sahabbai sun yi wa A’isha inkari a kan wannan. Ibn Abdul-Barri ma ya bayyana cewa mafi yawancin malaman zamaninta sun yi mata inkari. Ya Kara da cewa: "Magana mafi rinjaye ita ce fatawar Umar da Uthman da Sa’idu bn Musayyib (Allah Ya yarda da su), kuma ita ce muka rinjayar."

Amma malamai sun ce idan ta fita zuwa aikin Hajji ko Umrah, sai ta samu labarin mutuwar mijinta, alhali tana kusa da gari (kamar filin jirgi a nan Nijeriya), to sai ta dawo. Idan kuwa ta yi nisa, sai ta ci gaba da aikin Hajjinta ko Umrah.

 

12. Tambaya: Yaushe ne maniyyaci zai dauki niyyar aikin Hajji, kuma a ina zai dauka?

Amsa: Maniyyaci zai yi niyya ne a miKati yayin da ya daura ihraminsa, kuma zai Kudurta niyyarsa ne tare da talbiyya. Amma ba zai furta lafazin niyyar ba. Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn Umar (Allah Ya yarda da su) cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance idan ya daidaita a kan abin hawansa, bayan ya kammala nafila a masallacin Zul Hulaifah, yana daga murya da talbiyya.

A wannan lokacin ne zai yanke niyyar irin nau'in Hajjin da zai yi a zuciyarsa.

 

13. Tambaya: Menene ma’anar talbiyya?

Amsa: Da farko ga yadda lafazin talbiyya ya ke:

لبيك اللهم لبيك لبيك لآ شر يك لك لبيك, إ ن الحمد و النعمة لك والملك لآ شريك لك

Malamai na da fahimta dabam-daban dangane da ma’anar wannan lafazi, kamar haka:

· Wasu malamai sun ce ma’anar talbiyya shi ne: "Na yi nufin zuwa gareKa ya Allah, na yi nufinKa, kuma na fuskanceKa ya Allah."

· Wadansu malaman kuma suka ce ma’anar talbiyya shi ne: "Soyayya ta zuwa gareKa ya Allah"

· Amma ma fi rinjayen malamai sun tafi a kan cewa ma’anar talbiyya shi ne: "Amsa kira zuwa gareKa ya Allah, kuma ni mai tsayuwa ne a kan bautarKa, ba Ka da abokin tarayya. HaKiKa dukan godiya da girmamawa da ni’ima sun tabbata a gareKa. Mulki kuma ya tabbata a gareKa, ba Ka da abokin tarayya."

 

14. Tambaya: Shin mata za su yi talbiyya?

Amsa: Na'am, mata za su yi talbiyya, amma za su yi gwargwadon yadda za su jiyar da kansu ne. Ma’ana, ba za su boye ba, kuma ba za su daga murya da Karfi ba. Haka hukuncin yake idan za su cudanya da maza. Idan kuwa su kadai ne, za su daga muryarsu.

Domin yin talbiyya tare da daga murya, umurni ne daga Allah Subhanahu Wata’ala. Dalili kuwa shi ne Hadisin da Khalid bn Sa'id al al-Ansari ya karbo daga babansa ya ce: HaKiKa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Jibrilu ya zo mani, ya umurce ni, da in umurci Sahabbai na (ko wanda ke tare da ni) su daga muryarsu a wajen talbiyya."

Wannan Hadisi ya nuna daga murya umurni ne, ba zabi ba. Domin haka, muke yin nasiha ga mutanen da suke yin sakaci wajen yin talbiyya, musamman wasu matan da ba su yin talbiyya a boye, ko a sarari, da wasu mazajen ma. Saboda haka, ya wajaba a ji tsoron Allah, a yi KoKarin koyi da umurnin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

Ana lazimtar talbiyya ne, a yi ta maimaita ta. Amma idan an gaji, sai a huta. Amma duk da haka, akwai wuraren da ake so mutum ya cigaba da yin talbiyya: kamar idan ana hawa tudu, ko ana gangarowa, a cikin tafiya, a mota ne ko a jirgi, ko kuma yayin da aka idar da sallar farilla, da lokacin da dare yake gabatowa, da kuma lokacin da rana take fitowa. Haka za a yi ta yin talbiyya har a yi Dawaful Kudumi.

Amma yayin da ake dawafi da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa, ba za a yi ba, saboda Hadisin da ya tabbata daga Abdullahi bn Umar (Allah Ya yarda da su) cewa ya kasance yana yin talbiyya, kuma ba ya dainawa sai lokacin da zai yi dawafi ko Sa’ayi. Kuma ya kasance yana cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) haka yake aikatawa.

Ko da yake akwai magabatan da suke ganin ko da ana dawafi ma, za a iya yin talbiyya, kamar su Abdullahi bn Abbas da Imam Ahmad. Amma magana mafi rinjaye ita ce maganar Abdullahi bn Umar (Allah Ya yarda da su), domin ya danganta Hadisin zuwa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

Haka kuma mutum zai ci gaba da yin talbiyya daga fitarsa zuwa Mina, da zaman Mina, da zuwa Arfa, da tasowarsa daga Arfa zuwa Muzdalifa, daga Muzdalifa kuma zuwa wurin jifa ranar idi. Idan ya yi jifa ranar idi, zai daina yin talbiyya.

Dalili kuwa shi ne Hadisin da ya tabbata daga Fadlu bn Abbas (Allah Ya yarda da su) ya ce: "Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai gushe ba, yana talbiyya, har sai da ya yi jifar Jamratul AKaba.."

 

15. Tambaya: Menene sunnonin ihrami?

Amsa: Yana daga sunnonin ihrami:

§ Yin wanka kafin a sanya ihrami, domin haka Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya aikata.

§ Ana so mutum ya yanke farcensa, ya aske gashin hammatarsa da na mararsa, domin ka da ya buKaci yinsu bayan ya daura ihrami.

§ Haka kuma yana daga Sunna ta Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) mutum ya shafa turare a jikinsa kafin ya sanya ihrami. A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: "Na kasance ina sanya wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) turare (a jikinsa), yayin da zai sanya ihrami, da kuma yayin da ya fita daga ihrami, kafin ya yi dawafi."

§ Haka kuma ana son a sanya ihrami da daura niyya, bayan sallar farilla ko nafila. Amma ba ana yin sallar domin ihrami ba ne, kasancewar babu wata kebantacciyar nafila domin sanya ihrami. Saboda haka, idan mutum ya zo miKatinsa ba a lokacin sallar farilla ba, kuma an hana nafila a wannan lokaci, to zai dauki niyya ce kawai, daga nan sai ya cigaba da yin talbiyya, ba tare da ya jira sai lokacin sallar farilla ko nafila ba. Amma idan ya jinkirta har zuwa lokacin salla, to wannan zabinsa ne kawai, ba Shari’a ce ta kallafa masa ba.

Haka kuma mai jinin haila ko biKi za ta yi wanka ta sanya ihraminta, sa’an nan ta dauki niyya da yin talbiyya, ba tare da ta yi wata nafila ba. Amma ka da ta kuskura ta Ketare miKatinta ba tare da ta daura ihrami da daukar niyya ba. Domin yin hakan, saba wa Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ce, kasancewar ya umurci Nana Asma'u bint Umais (Allah Ya yarda da ita) da ta yi wanka, ta sanya ihraminta, alhali tana cikin jinin haihuwa. Haka nan, kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umurci Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita) da ta yi wanka ta sanya ihraminta, alhali tana cikin jinin haila.

Babu laifi ga wanda ke cikin ihrami ya yi wanka ko ya wanke ihraminsa idan ya buKaci haka, amma ba da sabulu mai Kamshi ba, domin a cikin wani Hadisi mai tsawo, Abu Ayyubal Ansari (Allah Ya yarda da shi) ya tabbatar da cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance yana yin wanka alhali yana cikin ihrami.

Haka nan, mutum zai iya sosa kansa idan ya ji KaiKayi, kuma ko gashi ya fado a sanadiyar haka, babu komai, domin an yi wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Kaho, yana cikin ihrami. Kuma babu wani nassi da ya hana wanda ke cikin ihrami ya yi susa idan ya ji KaiKayi ko kuma ya kwanta a kan matashin kai ko katifa.

Haka kuma babu laifi mutum ya daura jakar kudi a Kugunsa saboda larura, ko ya daura abin da zai riKe masa ihrami idan da buKata. Kamar yadda babu laifi mutum ya sanya tabarau ko tozali idan yana da larura a idonsa. Sayyidina Uthman (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana ba da fatawa a kan sanya tozali saboda larura, kuma yana dangana hakan ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Bayan wannan, wanda ke cikin ihrami zai iya riKe lema, domin Hadisi ya tabbata cewa an sanya wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) hema a ranar Arfa.

Haka kuma za a iya yi wa yaro ihrami, kuma a yi masa talbiyya, watau niyyar Hajjin da ake son ya yi, idan ba zai iya yi da kansa ba. Idan kuwa zai iya, sai a fada masa abin da zai ce, domin shi ma ya fada.

§ Mata kuma za su iya sanya kowane launin tufa da zai rufe masu jikinsu gaba daya, a matsayin ihrami, amma ban da niKabi (abin rufe fuska), da safar hannu da ta Kafa. Amma kasancewar mafi yawancin maza na sanya farin ihrami ne, ya kamata mata su sanya tufa wacce ba fara ba, domin ka da su yi kamanceceniya da maza.

 

16. Tambaya: Me ya kamata mai ihrami ya guji aikatawa yayin da yake cikin ihrami?

Amsa: Ya kamata mai ihrami ya guji aikata abubuwa kamar haka:

1. Ya guji saduwa da iyali yayin da yake cikin ihrami. Idan ya sadu da iyalinsa kafin tsayuwar Arfa, malamai sun yi ijma’i a kan ba shi da Hajji. Idan kuwa bayan Arfa ne, kafin ya yi jifa da yanka da aski, malamai sun yi sabani a kan haka. Duk da haka, zai kammala aikin Hajjinsa, amma kuma zai rama wannan Hajjin a shekara mai zuwa.

2. Ba zai nemi aure ba, kuma ba za a aura masa ba, ko da kuwa a garinsu ne za a daura masa auren, matuKar dai yana cikin ihrami. Haka nan kuma, shi ba zai aurar wa wani ba. Idan aka daura wa mutum aure alhali yana cikin ihrami, an saba wa Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

3. Ba zai aske gashin kansa ko na mara ko na hammata ba. Haka nan, ba zai yanke farcensa ba. Idan rashin lafiya ya same shi, har aka yi masa aski ko aka yanke masa farce, alhali yana cikin ihrami, to sai ya yi fidiya (yanka dabba). Dalili kuwa shi ne fadin Allah Ta’ala:

"… to wanda ya kasance mara lafiya daga cikinku, ko kuwa akwai wata cuta a kansa, sai (ya ba da) fansa (fidiya) na azumi (na kwana uku kafin ya dawo gida) ko sadaka (ciyar da miskinai guda shida) ko yanka (akuya) …"

Kuma Hadisi ya tabbata daga Ka’ab bn Ujrah (Allah Ya yarda da shi) ya ce: An dauke ni zuwa wajen Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), alhali KwarKwata na gangarowa a kan fuskata. Sai ya ce: "Ban san rashin lafiyarka ya tsananta haka ba: za ka iya yanka akuya?" Sai na ce: A’a. Sai ya ce: "Ka yi azumi na kwana uku, ko ka ciyar da miskinai guda shida; kowane miskini (ka ba shi) rabin sa’i (wato mudun-Nabi guda biyu)."

4. Ya guji cin ko shan duk wani abu mai wari ko mai sanya maye, kamar taba (sigari) ko tafarnuwa ko giya, domin wannan warin yana nisanta shi daga mala’ikun rahama, kuma yana cutar da `yan’uwansa da yake tare da su.

5. Haka nan, an hana shi yin farauta ko ya sanya a yi masa ko ya taimaka a yi. Amma zai iya kashe abubuwan da ke cutar da dan Adam, ko da yana cikin ihrami, kamar maciji, kunama, mahaukacin kare, da sauransu. Kuma zai iya kamun kifi (a cikin kogi) idan yana buKatar haka.

6. Ya guji maganganun batsa da jidali mara amfani

7. Namijin da ke cikin ihrami ba zai sanya dogon wando, ko takalmi sau ciki (mai rufi) ko hula ko safar hannu ko safar Kafa ko kamfai ba, kuma ba zai rufe kansa da mayafi ko rawani ko wani abu ba. Amma idan ya rasa ihrami, zai iya sanya dogon wando, kamar yadda wanda ya rasa takalmin da zai sanya (mara rufi), sai ya sanya sau ciki, amma ya yanke shi daga Kasan idan sawu.

 

17. Tambaya: Wadanne miKatai ne Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya iyakance wa mutanen duniya?

Amsa: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya iyakance wadannan miKatai ga mutanen duniya, kamar yadda ya zo a cikin Hadisin Abdullahi bn Abbas (Allah Ya yarda da su):

Zul Hulaifah: Mutanen Madina

Juhfah: Mutanen Afrika, da Sham da Misra, da Syria, da Oman, da Palestine, da Lebanon

Karnul Manazil: Mutanen Najad

Yalamlam: Mutanen Yaman

Zatu IrK: Mutanen IraKi

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya bayyana cewa wadannan wurare na mutanen Kasashen da aka ambata ne, da kuma wanda duk ya biyo ta wurin a yayin da zai tafi Hajji ko Umrah. Amma wadanda ke gaban miKati, za su yi ihrami ne daga inda suke, su kuma mutanen Makka, za su dauki harami daga gidajensu.

Sai dai kuma, kasancewar Juhfa, watau miKatin mutanen Afrika da Sham da sauransu, ruwa ya cinye ta, ana daukar ihrami ne daga wurin da ake kira Raabig, da ke daura da Juhfah, a kan hanyar Madina. Kuma wannan wuri na arewacin Makka ne, sa’an nan akwai kilomita 186 a tsakaninsu.

Raabig ne wurin da ya kamata maniyyata daga Nijeriya da sauran Kasashen Africa da Masar da Sham da Oman da Falasdinu da Syria da Lebanon su dauki ihrami, ba Jidda ba. Amma idan sun samu wucewa Madina tun farkon isansu Saudia, shi ke nan, sai su dauki ihrami daga Zul Hulaifah, a kan hanyarsu ta zuwa Makka. Wadanda za su hau jirgi, daga Madina zuwa Makka, sai su yi wanka, su sanya ihrami, da zarar jirginsu ya tashi, sai su daura niyya. Dangane da mutanen Nijeriya da ba za su samu wucewa Madina ba, za su iya yin wanka su daura haraminsu tun daga gida ko a filin jirgi ko a cikin jirgi (gwargwadon yadda ya samu), sa’an nan idan an kusa isa miKati, sai su daura niyya.

daukar Jidda a matsayin miKati ba daidai ba ne, domin ba miKatin kowa ba ce, face mutanen Jidda. Malaman duniya sun yi Ijma’i a Rabidatul alamil Islami a kan cewa, wadanda ruwa ya cinye miKatinsu, ba za su dauki Jiddah a matsayin miKati ba, kamar yadda yake Kunshe cikin Fatawa mai lamba (142) wacce aka yi a 9/11/1407 AH. A wannan zama, malamai biyu ne kawai suka saba wa sauran malaman duniya, wato Shaikh Mustafa ZarKa da Shaikh Abubakar Mahmud Gumi. Sai dai kuma ba su kawo wata hujja da za a dogara da ita ba.

 

18. Tambaya: Menene hukuncin wanda ya Ketare miKatinsa ba tare da ya yi niyya ba?

Amsa: Bai kamata mutum ya Ketare miKatinsa ba tare da ya daura ihraminsa ba. Idan ya yi haka, ya saba wa Sunnar Manzon Allah (Sallalahu alaihi Wasallam), kuma mafi yawan malamai sun ce zai yi yanka.

 

19. Tambaya: Aikin Hajji ya kasu kashi nawa ne?

Amsa: Aikin Hajji ya kasu kashi uku: Tamattu'i, Kirani da Ifradi

1. Tamattu'i: Shi ne mutum ya fara gabatar da Umrah a cikin watannin Hajji, sa’an nan, ya zauna a cikin birnin Makka har zuwa takwas ga watan Zul Hijjah, daga nan ya yi Hajjinsa. Watannin Hajji su ne: Shawwal, Zul Ka’adah da Zul Hijjah.

2. Kirani: Kirani shi ne nau’in aikin Hajji da ake daukar ihrami a miKati da niyyar aikin Umrah da Hajji a hade.

3. Ifradi: Shi ne mutum ya dauki ihrami a miKati da niyyar Hajji kadai.

 

20. Tambaya: Yaya ake yin Umrah?

Amsa: Ayyukan Umrah su ne:

· Sanya ihrami da daura niyya a miKati

· Daga nan sai dawaful Kudumi, wanda a cikinsa ne ake yin sassarfa a kewaye ukun farko, ragowar kewaye hudun kuma a yi tafiya sosai a cikinsa. Amma mata ba su yin sassarfa.

· Daga nan sai a yi raka’a biyu a wurin MaKama Ibrahim, idan an samu dama. Idan kuwa ba a samu dama ba, sai a yi salla a duk inda aka samu.

· Daga nan, sai a sumbanci Hajarul Aswad, sa’an nan, a tafi rijiyar ZamZam a sha ruwa, a zuba a kai, idan an samu hali.

· Daga nan sai a yi Sa'ayi (Safa da Marwa). Ana fara shi ne daga dutsen Safa, a yi tafiya zuwa dutsen Marwa. Za a yi haka sau bakwai: idan an je Marwa daga Safa, an yi daya; idan an dawo Safa, an yi biyu kenan. Za a Kare sa’ayin ne a dutsen Marwa.

· Sa’an nan, sai maza su yi saisaye, su kuma mata su yanke kadan daga gashin kansu (gwargwadon gabar yatsa).

· Daga nan sai a cire ihrami. Da zarar an yi haka, to dukan abin da ake da buKatar yinsa, daga cikin abubuwan da aka haramta wa mutum a lokacin aikin Hajji, ya halasta ga mai tamattu’i.

· Idan an daura niyyar yin Kirani ne, ba za a yi saisaye ko aski ba, haka nan, ba za a cire ihrami ba. Kuma duk abin da ya haramta ga mai aikin Hajji, ya haramta gare shi. Amma idan harami ya yi dauda, babu laifi a cire don wankewa, sa’an nan a sake sanyawa.

 

21 Tambaya: Menene ayyukan Hajji ya Kunsa?

Amsa: Ayyukan Hajji na da matakai kamar haka:

§ A ranar takwas ga watan Zul Hijjah za a dauki niyya, a sanya ihrami daga gidan da ake zaune a nan Makka, tare da kiyaye sunnonin ihrami da aka ambace su a baya, da niyyar yin aikin Hajji.

§ Sa’an nan sai a nufi Mina. Yana da kyau Azahar ta riski mai aikin Hajji a can, domin a nan ne za a yi sallar matafiyi (watau Kasaru), kuma a hada sallar Azahar da La’asar.

§ Yana da kyau Alhaji ya kiyaye irin ibadar da ya kamata a ce ya yi su a lokacin zaman Mina. Abubuwan sun hada da:

1. Yawan yin talbiyya, da tilawar AlKur'ani, da Istigfari, da Salatin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) da Hailala.

2. Idan an wayi gari kuma, sai a tafi filin Arfa. Yana da kyau a riski sallar Azahar a can, inda za a hada sallar Azahar da La'asar (Kasaru) a masallaci tare da Liman. Idan ba a samu sallar tare da liman ba, ko kuma ba a samu wuri a cikin masallaci ba, sai a yi sallar a hema. Haka nan, za a cigaba da ibada a filin har sai rana ta fadi, sa’an nan a bar filin.

3. Daga nan sai a tafi Muzdalifa a hada sallar Magriba (raka’a uku) da Isha (raka’a biyu). Kuma a kwana a nan Muzdalifa.

4. Idan gari ya waye, sai a yi addu'o’i daf da fitowar rana, sa’an nan a nufi Mina don yin jifa.

5. Daga nan sai a yi yanka (ga wanda ke yin tamattu’i ko Kirani), a yi aski, mata kuma su yanke gashin kansu gwargwadon gabar yatsa.

6. Daga nan sai a tafi garin Makka, a yi dawaful Ifadha da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa, kamar yadda aka bayyana a can baya. Amma wanda ya daura niyyar yin Ifradi ko Kirani, ba dole ne ya sake yin Sa’ayi bayan dawaful Ifadha ba, tun da ya gabatar a lokacin da ya yi dawaful Kudum. Wanda ke yin Kirani na da zabi na ya yi Sa’ayi a dawaful Kudum ko a dawaful Ifadha, amma wanda ke yin Ifradi, ba a buKatar ya sake yin Sa’ayi tun da ya gabatar a dawaful Kudum.

7. Bayan wannan, sai a dawo Mina, don cigaba da zama na kwana uku ko biyu, tare da yin jifar jamrori.

 

22. Tambaya: Daga ina ake fara dawafi? Kuma a cikin Kusurwoyin Ka’aba ina ne ake sumbanta, kuma ina ne ake shafa?

Amsa: Ana fara dawafi daga Kusurwar da Hajarul Aswad yake (wajen shan mama), wajen da yanzu aka ja layi. Idan aka kewayo, aka dawo dai dai gurin da aka fara, an yi daya kenan. Haka za a yi har sau bakwai. Kuma Hajarul Aswad shi ake sumbata a kowane zagaye in an samu iko. Idan kuma ba a samu iko ba, sai a sa hannu a ciki a dawo da shi baki, a sumbance shi. Idan kuma ba a samu dama ba, sai a daga hannu dai dai in da yake a nuna shi a ce: "Allahu Akbar" a wuce.

A wannan gurin, bai kamata a yi kokawa ko a cutar da wasu ba. Domin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya fada wa Sayyidina Umar (Allah ya yarda da shi.) cewa: "Ya Umar kai mutum ne mai Karfi, kar ka cutar da mutanen da ba su da Karfi wajen sumbatar Hajarul Aswad. In ka samu dama ka yi, in ba ka samu ba, ka daga hannu ka wuce."

Wurin da ake shafa kawai, shi ne Rukunul Yamani: ba a sumbatarsa, kuma idan an yi nisa da shi, ba za a daga masa hannu ba. In ban da wadannan wurare, babu wani wuri da ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa ya shafa ko ya yi umurni a shafa domin neman tabarruki ko makamancin haka. Amma Multazim (wurin da yake tsakanin Kofar Ka’aba da Hajarul Aswad), za a iya rungumarsa, a yi addu'a. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa ya rungume shi ne, ya yi addu’a. Kuma haka mafi yawan Sahabbai, kamar Abdullahi Ibn Abbas da Urwatu bn Zubair, suka aikata. Saboda haka duk wanda ya shafi wuraren da ba a umurce shi ba, kamar MaKama Ibrahim, domin neman tabarruki, kamar yadda wasu suke yi, to ya saba wa Shari'ah. Mahajjaci ya sani cewa ya tafi aikin Hajji domin neman yardar Allah ne, saboda haka ya kamata ya guji abin da zai bata aikin Hajjinsa.

 

23. Tambaya: Shin ko akwai addu'ar da aka kebance mai dawafi ya yi?

Amsa: A gaskiya babu wata addu'a da ta tabbata daga bakin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) wanda aka kebance wa mai dawafi. Sai dai akwai wata addu’a da aka ruwaito cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yana yi a tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad kamar haka:

ربنا اتنا فى الدنيا حسنة وفى ا لآ خرة حسنة وقنا عذاب النار

Ma’anarta: Ya Ubangiji Ka ba mu kyakkyawa a nan duniya, kuma Ka ba mu kyakkyawa a ranar lahira, sa’an nan kuma Ka tseratar damu daga azabar wuta.

Wannan ita ce addu’ar da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ke yi a tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad.

Amma sai ga shi an buga littafai da dama dangane da addu'o’in da ake cewa wai na dawafi ne, ana sayar wa mutane. Sai ka ga an ce ga addu'ar dawafin farko, ga kuma addu'ar dawafi na biyu har a gama dawafin. Irin wadannan littafai su ne ke Kara sanya jama’a su kasa fahimtar yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya aikata wani aiki. Wadannan addu’o’i ba su da wani asali daga cikin littafin Allah ko kuma koyarwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Ya ‘yan’uwa masoya Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), wajibi ne a guji afkawa cikin Kagaggun al’amura, domin ka da a yi aikin baban giwa. Saboda haka, ya kamata a nisanci irin wadannan littafan, sa’an nan a daure a tambayi irin yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi. HaKiKa yin hakan shi ne tsira, kuma shi ne cikakkiyar soyayya da miKa wuya ga Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

Domin haka, ya kamata maniyyaci ya san abin da ya kai shi aikin Hajji, kuma me yake buKata a wajen Allah. Sai ya yi tunanin buKatunsa ga Allah, Ya roKe Shi, da fatan ya samu biyan buKatarsa. Muhimmin abu ga mahajjaci shi ne ya san cewa ya je aikin Hajji ne domin neman yardar Allah, kuma domin a nemi gafarar zunuban da aka aikata. Saboda haka, sai a duba addu'o’in da suka tabbata daga cikin ayoyin AlKur’ani da Hadisan Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

Haka kuma, buKatun da ake da su na duniya da lahira, a tabbata sun dace da koyarwar littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Amma idan ba a jin larabci, watau ba za a iya yin addu’a da larabci ba, to sai a roKi Allah Ta’ala buKatun alheri da suke cikin ran Alhaji da harshen da zai iya fahimtar abin da yake roKo. Domin ka da a je ana addu'a da larabci, ba tare da an san abin da ake fada ba. Haka kuma a riKa KoKarin yin iKrari da zunubai, ana yawaita tuba ga Allah Madaukakin Sarki (watau Istigfari). Haka nan, ka da a manta da iyaye da `yan`uwa da suka mutu, a riKa tunawa da su, ana yi musu addu'a, tare da roKon kyakykyawan Karshe ga mai aikin Hajji, da iyaye da ‘yan’uwa da zuriyarsa da ke raye.

 

24. Tambaya: Idan mutum ya yi kokwanton adadin dawafinsa, yaya zai yi?

Amsa: Idan mutum yana kokwanton dawafinsa ya cika ko bai cika ba, sai ya gina shi a kan yaKini. Watau, idan yana kokwanton hudu ko biyar, sai ya mayar da shi hudu, don shi ne yaKini. Idan kuma yana ganin ya yi Kari ne, sai ya bar shi haka, ya yi salla. Wannan ita ce fatawar Imam Malik.

 

25. Tambaya: Shin akwai wani dawafi da ake kira bakwai sau bakwai, domin neman biyan wata buKata?

Amsa: A gaskiya babu wani dawafi a shari’a da ake kiransa bakwai sau bakwai. Domin irin wannan dawafi bai tabbata ba a cikin littafin Allah ko kuma koyarwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Sai dai akwai dawafin nafila wanda za a iya yi. Amma shi dawafin nafila, ba a Kayyade adadi da za a yi ba. Illa iyaka idan an yi dawafi bakwai, sai a yi nafila, idan an Kara yin wani bakwai, sai a yi nafila. Haka za a yi, gwargwadon yadda aka samu dama, domin neman kusanci da Allah. An tambayi Imam Malik cewa: Mutum zai iya yin dawafi sau saba’in, ba tare da ya yi raka’a biyu a kowane bakwai ba? sai ya ce: "Ba na son wannan aikin, kuma ba shi daga cikin ayyukan magabata."

Abin da yake rudar mutane shi ne Hadisin Hisham bn Urwa wanda ya karbo daga Babansa wanda ya zo a cikin Muwadda cewa: "Babansa yana hada dawafinsa ne kawai, ba tare da ya rarrabe bakwai-bakwai ba."Saboda haka, wadansu mutane ke kafa hujja da shi.

To amma haKiKa, aiki mafi kyawu shi ne aikin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), kuma shiriyarsa ita ce fiyayyar shiriya.

Sa’an nan, lallai ne a yi hattara da malaman da ke karbar kudi a wurin jama’a, da nufin wai za su yi musu dawafi bakwai sau bakwai, domin biyan wata buKata. HaKiKa yin hakan, kauce wa umurnin Allah, da na Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da kuma na magabata na Kwarai ne.

 

26. Tambaya: Idan mutum ya yi sallah raka'a biyu a bayan MaKama Ibrahim, sai ya tuna dawafinsa bai cika ba, yaya zai yi?

Amsa: Idan haka ta faru, sai ya koma ya cika dawafin, sa’an nan ya zo ya sake yin raka'a biyu, domin ita raka'a biyun ba ta tabbata sai bayan dawafi.

 

27. Tambaya: Idan aka fara salla alhali mutum na dawafi, yaya zai yi?

Amsa: Idan haka ya faru, sai ya tsaya ya bi liman sallah. Idan aka idar da salla, sai ya ci gaba da dawafinsa daga inda ya tsaya. Amma idan sallar Jana'iza ce, to mutum yana da zabi: ko dai ya tsaya, ko ya ci gaba da dawafinsa.

 

28. Tambaya: Menene hukuncin wanda alwalarsa ta karye alhalin yana dawafi?

Amsa: HaKiKa malamai sun Kara wa juna ilmi a kan hukuncin wanda alwalarsa ta warware, alhali yana cikin dawafi. Wasu malaman na ganin ya sake jaddada alwala, sa’an nan ya Karasa dawafinsa, saboda suna ganin cewa alwala, mustahabbi ne, ba sharadin ingancin dawafin ba. Dalilinsu shi ne Hadisin da aka karbo daga Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita) cewa: "Farkon abin da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya fara yayin da ya zo Makka shi ne alwala kafin dawafi." Wannan yasa wadannan malaman suka ce, wannan Hadisin ya nuna cewa alwala mustahabbi ne, ba wajibi ba, tun da yake babu wani umurni a ciki.

Amma Imam Malik da Imam Shafi’i da Imam Ahmad, a daya daga maganganunsu guda biyu, suna ganin alwala sharadi ne na ingancin dawafi, tun da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya aikata hakan, kuma ya ce:

خذ وا عنى مناسككم

Ma’ana: "Ku riKi ibadun aikin Hajjinku daga gareni", kuma alwala tana daga cikin ayyukan Hajji.

Dalilinsu na biyu shi ne, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce wa mai jinin al’ada ta yi kowace irin ibada ta Hajji, amma ban da dawafi. Wadannan malamai na ganin cewa rashin alwala ya sa aka hana ta.

Suka Kara da cewa: sahabbai suna ganin cewa dawafi salla ne, sai dai shi ana magana a cikinsa, saboda Hadisin Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da shi) cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "dawafi a daki (Ka’aba), salla ne, sai dai ana magana a cikinsa."

Daga bayanan da suka gabata, muna rinjayar da cewa idan hakan ya faru ga mai dawafi, mustahabbi ne ya sake alwala, sa’an nan ya cigaba da dawafinsa. Wallahu A’alam

 

29. Tambaya: Wadanne addu'o’i ne suka tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yayin Sa'ayi?

Amsa: Shi dai Sa'ayi an yi bayaninsa a can baya, saboda haka yanzu za a yi bayanin irin addu’ar da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi a lokacin da yake yin Sa’ayi. Da farko dai ana fara yin Sa’ayi ne daga Safa, domin haka idan mutum ya dumfari dutsen Safa, sai ya karanta:

ان الصفا والمروة من شعا ئر الله فمن حج البيت اواعتمر فلا

جنا ح عليه ان يطو ف بهما ومن تطوع خيرا فا ن الله شا كر عليم

Ma’ana: "Lallai ne Safa da Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to wanda ya Hajjin daki ko kuwa ya yi Umrah, to, babu laifi a kansa da ya yi dawafi gare su. Kuma wanda ya Kara yin wani aikin alheri, to, lallai ne Allah Mai godiya ne, Masani."

Sa’an nan, idan an hau kan dutsen, sai a fuskanci Ka'aba a ce:

الله اكبر الله اكبر الله اكبرلآ اله الآ الله وحده لآشريك له, له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قد ير

لآاله الآ الله وحده لآشر يك له أنجز وعده ونصر عبده وهزم الأحزاب وحده

Ma’ana: "Allah Shi ne mafi girma! Allah Shi ne mafi girma! Allah Shi ne mafi girma! Babu wanda ya cancanta a bauta maSa sai Allah, Shi kadai Yake, ba Shi da abokin tarayya, dukan mulki da dukan godiya naSa ne, kuma Shi Mai iko ne a kan kome. Babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, Ya zartar da alKawarinSa, kuma Ya taimaki bawanSa, kuma Ya ruguza rundunar (kafirci) Shi kadai."

Bayan ya gama wannan, sai ya roKi Allah gafara da alherin duniya da lahira. Haka zai yi har sau uku.

Idan ya gama wannan addu'o’i, sai ya gangaro zuwa dutsen Marwa. Idan ya iso wurin da aka sanya koriyar fitila a sama, a tsakanin Safa da Marwa, sai ya yi sassarfa (amma mata ba sa yi). Idan ya kusa hawa Marwa, sai ya karanta irin addu'ar da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi a lokacin da ya dumfari Safa. Idan ya hau kan Marwa, sai ya sake fuskantar Ka'aba ya yi kabbara sau uku, sa’an nan ya Kara yin irin addu'o’in da aka ambata ana yi a kan dutsen Safa.

Haka za a yi ta yi har sau bakwai. Ma’ana, idan aka fara daga Safa zuwa Marwa, daya kenan; idan aka dawo daga Marwa zuwa Safa, biyu kenan. Tsakanin Safa da Marwa kuma babu wata kebantacciyar addu'a da ake yi, sai dai mutum zai iya yin Tasbihi, Istigfari, Hailala, Salatin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam), da sauransu.

Shi Sa'ayi, wanda ke yin aikin Hajji ko Umrah ne kawai yake yinsa. Amma ba za a iya yinsa da niyyar nafila, kamar yadda ake yin dawafi na nafila ba.

 

30. Tambaya: Wace irin ibada ya kamata mahajjaci ya shagaltu da ita ranar Arfa?

Amsa: Filin Arfa, fili ne babba wanda aka iyakance shi, aka kuma sanya masa alama gabas da yamma, kudu da arewa. An yi rubutu a wurin da harshen Hausa da Larabci da Turanci. Domin haka, bai kamata a tsaya a wani wuri dabam, ba inda aka iyakance ba. Ko ina aka tsaya a cikin wannan filin da aka iyakance, ya yi daidai. Haka kuma, ba a hawa kan dutsen, domin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai hau kan dutsen ba. Ya tsaya ne a bayan dutsen, daga gabas, ta yadda ya sanya dutsen tsakaninsa da Makka, alhali yana kan raKuminsa. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Na tsaya a nan, kuma duk filin Arfa wurin tsayuwa ne."

Ana fara addu’a a ranar Arfa da zarar an idar da Sallar Azahar da La'asar wadanda ake yinsu a hade, watau a farkon lokacin Azahar. Ana son a tsaya a kan abin hawa, ana fuskantar AlKibla. Idan ba a samu abin hawa ba, sai a tsaya a bisa kan dugadugai, a fuskanci AlKibla, a cigaba da addu’a. Idan kuma babu hali, sai a zauna, a fuskanci AlKibla, a yi ta addu’a. Domin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) a kan raKumarsa ya zauna. Haka kuma, ana son a kasance cikin alwalla, ana son a daga hannuwa sama a yayin da ake yin addu'a.

Addu'ar da aka fi so a wannan ranar kuwa ita ce:

لآ اله الآالله وحده لأشر يك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قد ير

Ma’anarta: "Babu wanda ya cancanta a bauta masa sai Allah Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, mulki gare Shi yake, kuma godiya ta tabbata gare Shi, kuma Shi Mai iko ne a kan kome."

Ita za a yi ta maimaitawa, sa’an nan, a yi ta neman gafarar duk abin da aka yi na sabo, wanda aka sani da wanda ba a sani ba. Kuma a roKi dukan buKatu na duniya da lahira, da neman kyakkyawan Karshe, a nema wa iyaye da suka mutu gafara. Haka nan, a hada da `ya`ya da `yan’uwa a cikin addu’a, kuma ka da a manta da `yan’uwa musulmi da ke cikin gwagwarmaya da jihadi a kowane bangare na duniya, da wadanda ake zalunta, suna yaKin Kwatar kai daga hannun kafirai.

Haka nan, zai yi matuKar fa’ida idan aka hada da wannan zikiri:

سبحا ن الله و الحمد لله ولآ اله الآ الله والله اكبر ولآحو ل ولآقوة إ لآ بالله العلىالعظيم

Ma’ana: "Tsarki ya tabbata ga Allah, dukan godiya ta tabbata ga Allah. Kuma babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Allah Shi ne mafi girma. Kuma babu dabara, babu Karfi sai ga Allah, Madaukaki, Mai girma."

Kuma a yi KoKarin yawaita salatin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam). Daga cikin salatin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) da addu’o’in da suka tabbata a cikin Sunna, akwai:

اللهم صل على محمد وعلى ال محمد كما صليت على ابرهيم وعلى ال ابرهيم فى العلمين انك حميد مجيد وبا رك على محمد وعلى ال محمد كما باركت على ابرهيم وعلى ال ابرهيم فى العلمين انك حميد مجيد.

Ma’ana: "Ya Allah Ka yi salati ga Muhammad da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin talikai, haKiKa Kai abin godewa ne, abin girmamawa. Ka yi albarka a bisa Muhammad da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi albarka a bisa Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin talikai, haKiKa kai abin godewa ne, abin girmamawa."

اللهم انى اعوذ بك من الهم والحزن ومن العجز والكسل ومن الجبن والبخل ومن المأثم والمغرم ومن غلبة الدين وقهر الرجال واعوذ با لله من البرص والجنون والجزام ومن سوء الأسقا م اللهم انى اسألك العفو والعا فية في الد نيا و الآخرة

Ma’ana: "Ya Allah, ina neman tsarinKa daga bacin rai da baKin ciki da gajiyawa da kasala, da tsoro da rowa da sabo da bashi da rinjayar bashi da rinjayar mazaje (abokan gaba). Kuma ina neman tsari wurin Allah daga kuturtar da ke zubar da miki, da hauka, da kuturta (mara zubar da miki), da miyagun cututtuka. Ya Allah, ina roKonka afuwa da lafiya a duniya da lahira."

لآ اله الآالله ولآ نعبد الآ اياه له النعمة وله الفضل وله الثناء الحسن لآاله الآالله مخلصين له الدين ولو كره الكفرون لاحول ولآ قوة الا بالله, اللهم أصلح لى دينى الذى هو عصمة امرى, وأ صلح لى دنياى التى فيها معا شى, وأ صلح لى اخرتى اللتىاليها معا دى, واجعل الحياة زيا دة لى فى كل خير, والموت راحة لى من كل شرأعوذ بالله من جهد البلاء ودرك الشقاء وسوء القضاء وشما تة الأعداء

Ma’anarta: Babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah. Kuma ba mu bauta wa kowa sai Shi kadai; ni'ima da falala da kyakkyawan yabo duk sun tabbata a gare Shi. Babu wanda ake bauta wa bisa cancanta sai Allah. Muna masu tsarkake addini a gare Shi, ko da kafirai sun Ki. Babu dabara, babu Karfi, sai ga Allah. Ya Allah Ka kyautata mani addini na, wanda shi ne kariyar al’amura na. Ka kyautata mani duniya ta, wadda a cikinta ne abubuwan rayuwa ta suke. Ka kyautata mani lahira ta wadda a cikinta ne makomata take. Ka sanya rayuwa ta zama Kari a gare ni cikin dukan alheri. Ka sanya mutuwa ta zama hutu ne a gareni daga dukan sharri. Ina neman tsarin Allah daga tsananin bala’i da afkawa cikin tabewa, da mummunar Karshe, da dariyar Keta ta abokan gaba.

Haka nan, ka da a Kosa wajen roKon Allah ana KasKantar da kai, ana komawa zuwa ga Allah, ana roKonSa, ana furuci da dukan abin da aka aikata na laifuffuka, sa’an nan kuma ana neman gafararSa.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya tsaya a kan raKumarsa, tun bayan sallar Azahar, yana roKon Allah Madaukakin Sarki, har faduwar rana, har ana zaton ma ko azumi yake yi. Saboda haka, idan Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) zai dage a kan raKumarsa, yana roKon Allah Ta’ala, to ina kuma ga mu, wadanda ba mu san yadda makomarmu za ta kasance ba?

Abin takaici shi ne sai ka ga wadansu mutane suna yawo a cikin filin Arfa, wasu suna barci, wasu suna surutu ko hira, wasu kuma suna KoKarin su je su hau dutsen Arfa, wadansu kuwa ba su yin komai, sun gafala da yin addu'a.

Wadansu kuma ka ga sun tara mata suna karanta musu addu'o’in da ba su da asali a shari’a, su kuma matan suna amshi; alhali kuwa hakan cutarwa ce ga matan, tun da dai ba a bar su sun roKi Allah buKatunsu ba. Sa’an nan kuma mafiya yawansu ba su san ma’anar abin da ake karanta musu ba. Irin wannan dabi’a ita ce hasara kan hasara, domin shi mai koyarwar bai tsaya ya yi tasa addu’ar ba, sa’an nan kuma bai bar su matan sun yi ta su addu’ar ba.

Haka kuma za ka ga wadansu da suka fitini kawunansu, har taba (sigari) suke sha a filin Arfa, ba su ko damuwa da cewa warinta yana damun jama’a, sa’an nan kuma yana nisanta su daga Mala’ikun rahama.Wadansu kuwa, sai ka ga suna gaggawa, domin su bar wannan fili na Arfa kafin faduwar rana.

HaKiKa yin wadannan abubuwa sun saba wa Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da aikin Magabata na Kwarai. Domin Hadisi ya tabbata daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Lallai Allah Yana shaida wa Mala'ikunSa a yammacin Arfa, Yana cewa: "Ku kalli bayiNa sun zo maNi, alhalin gashinsu ya yi Kura. Allah Madaukakin Sarki zai ce: "Na gafarta musu."

Haka nan, Hadisi ya tabbata daga Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita) daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce "Babu wata rana da Allah Ya fi `yanta bayinSa daga wuta kamar ranar Arfa."

Bayan wannan, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai bar filin Arfa ba, sai bayan faduwar rana, ga shi kuma ya ce: "Ku riKi ibadun aikin Hajjinku daga gare ni."

Saboda haka, babu wanda Shari’a ta yi wa uzuri ya bar wannan fili kafin faduwar rana sai mara lafiya. Shi ne wanda za a iya kawo shi filin Arfa a wani yanki na yini, kamar rabin rana ko kuma wani bangare na dare. Haka kuma wanda ya makara bai zo da rana ba, saboda wani uzuri, zai iya tsayawa da daddare matuKar alfijir bai keto ba. Hadisi ya tabbata cewa akwai wani Sahabi da ake kira Urwatu bn Mudarris bai samu Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) a Arfa ba, sai Muzdalifa, sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce masa: "Shin ka samu tsayuwar Arfa a wani yanki daga rana ko dare"? Sai ya ce: Eh! na samu wani yanki na tsayuwar Arfa a cikin dare. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Wanda ya samu tsayawa a wani yanki na dare ko rana, haKiKa Hajjinsa ya cika." Kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Arfa ita ce Hajji." Wannan yasa malamai suka yi ijma’i a kan cewa tsayuwar Arfa tana Karewa daga ketowar alfijir na ranar Idi ne.

Muna roKon Allah Ya ba mu dacewa, Ya karba mana Hajjinmu da sauran ibadarmu, Amin.

 

31. Tambaya: Wace irin ibada ya kamata a shagaltu da ita a Muzdalifa?

Amsa: Farkon ibadar da ta wajaba a kula da ita da zarar an isa Muzdalifa it a ce hada sallar Magrib (raka’a uku) da Isha (raka’a biyu), kuma ba tare da an yi nafila a tsakaninsu ba. Jabir bn Abdullah (Allah Ya yarda da shi) ya ce: "Farkon abin da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi a Muzdalifa shi ne hada sallar Magriba da Isha."

Bayan wannan, babu abin da ya kamata a yi, sai a kwanta a huta. Sa’an nan da zarar alfijir ya keto, sai a yi sallar Asuba a farkon lokaci. Idan an idar da salla, sai a Karasa Mash’arul Haram, idan an samu dama. Idan ba a samu dama ba, sai a tsaya a ko’ina cikin Muzdalifa, a fuskanci AlKibla, a yi ta yin Hailala da Hamdala da Tasbihi da Salatin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam). Za a daga hannuwa a yi ta yin addu’a har gari ya waye sarai. Daga nan, sai a tafi Mina don yin jifar Jamratul AKabah.

Ya kamata a sani cewa, kwana a Muzdalifa da yin sallar Asuba a wurin Sunna ce ta Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), kuma yana daga cikin wajiban aikin Hajji. Domin haka, ba wanda zai bar Muzdalifa kafin gari ya waye, sai raunana da Kananan yara da marasa lafiya da masu larura. Su ma ba za su bar Muzdalifa ba, sai wata ya bace (watau zuwa tsakiyar dare) sai su tafi Mina, idan sun je kuma ba za su yi jifa ba, sai bayan fitowar alfijir. Wannan ita ce magana mafi rinjaye.

Lallai ne a nisanci wadannan kurakurai:

1. Kin kwana a Muzdalifa ba tare da larura ba. Maganar da ake yi cewa ba wajibi ba ne a kwana a Muzdalifa bisa koyarwar mazhabar Malikiyya, ba haka ba ne, Kage ne kawai aka yi. Domin abin da ya tabbata a Hadisin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da aikin magabata na Kwarai shi ne mazahabin Imam Malik. Da’awar cewa ana sauka a Muzdalifa gwargwadon Shafa’i da Wuturi ne, bayan sallar Isha, wannan na nufin masu uzuri ne kawai, amma ba wadanda ba su da wani uzuri ba. Masu uzurin ma, sai dare ya raba, kamar yadda Hadisi ya tabbatar.

2. Wadansu kuma sai su wuce Mina a wannan daren, su je su yi jifa, ba tare da sun tsaya a Muzdalifa ba. Kuma ba su da wani dalili da suka dogara da shi a kan haka. Ana wa irin wadannan mutanen tsoron ka da aikinsu ya tafi a banza.

Allah Ya kiyaye mu, Ya bamu ikon ji da aiki da shi.

 

32. Tambaya: Wadanne irin ayyuka a ke yi a ranar Idi, bayan an bar Muzdalifa zuwa Mina?

Amsa: Ayyukan da ake yi a ranar Idi bayan an bar Muzdalifa zuwa Mina su ne:

1. Za a tsinci tsakuwa (gwargwadon girman yatsa) guda bakwai a kan hanyar Muzdalifa zuwa Mina, kuma ba sai an wanke su ba. Idan aka zo Mina, sai a jefi Jamratul AKabah. Za a iya yin jifa a wannan rana tun daga fitowar rana, har zuwa dare.

· Idan aka zo yin jifa a wannan rana, za a tsallake Jamra ta daya da ta biyu, sai a yi jifa a Jamra ta Karshe wacce take kusa da Makka.

· Ana son a yi kabbara a yayin da za a jefa kowace tsakuwa.

· Ana son a jefa kowace tsakuwa ita kadai.

· Sa’an nan ana son kowace tsakuwa ta shiga ramin da aka kewaye.

· Idan aka jefi wannan Jamrah, sai a daina yin talbiyya.

2. Daga nan, sai mahajjaci ya je ya yi yanka, kuma an fi son Alhaji ya yanka dabbarsa da kansa. Idan bai samu dama ba, sai ya wakilta wani amintacce ya yanka a maimakonsa. Ana son ya ci wani abu daga cikin naman hadaya, idan ya samu dama. Sa’an nan, ana so a yayin yankan ya ce: "Bismillahi Wallahu Akbar Allahumma Inna Haadha Minka Walaka, Allahumma TaKabbal minnee."

· Idan Mahajjaci bai samu damar yanka ba a ranar Idi, to dukan ranakun Mina, ranakun yanka ne. Domin Hadisi ya tabbata Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Duk ranakun tashriK (watau ranakun Mina) ranakun yanka ne."

· Wanda ya yi Hajjin Kirani ko tamattu’i ne kawai zai yanka hadaya, kamar yadda bayani ya gabata a can baya. Amma wanda ba shi da hali, an yi masa rangwame. Sai dai kuma zai yi azumi na kwana uku a cikin kwanakin Hajji, kuma ya yi bakwai idan ya dawo gida. Amma zai yi kyau a tuna cewa mutune bakwai za su iya hada kudi su sayi saniya ko mutane goma su sayi raKumi domin su yanka a matsayin hadayarsu.

3. Bayan yanka, sai a yi aski. Maza ne kawai ke yin aski, ban da mata. Yin aski shi ne ya fi, domin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kwadaitar da yin hakan. Idan ba a samu dama ba, sai a yi saisaye.

4. Daga nan, mahajjaci yana da zabi: ko dai ya cire ihraminsa, ya sanya kayan gida, ko kuma ya bar shi a jikinsa.

Lallai ne mahajjaci ya fahimci cewa ba a yanka hadaya, ba tare da an yi aski ba. Aski kuwa ba a yinsa sai ranar Idi, bayan an yi jifa. Wannan shi ne abin da ya tabbata a cikin Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da aikin Magabata na Kwarai. Bayan wannan, Allah (Madaukakin Sarki) Ya ce: "… kuma ka da ku aske kawunanku har sai hadaya ta isa wurinta (watau Mina a ranar Idi) …" Kuma sanannen abu ne cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) shi ne mai fassara mana AlKur'ani; shi kuwa bai yi yanka ba, har sai ranar Idi, haka nan ma, sahabbansa suka yi. Don haka, ka da mahajjaci ya kuskura ya yi yanka kafin ranar Idi, kamar yadda wadansu suke yi.

Sai dai kuma akwai wadanda suke dogaro da maganar Imam Munziri a cikin Mukhtasar Khalil cewa, za a iya yanka hadaya kafin ranar sallah. To haKiKa wannan maganar ko a mazahabar mu ta malikiyya, ba ta da rinjaye. Haka nan, wadanda ke kafa hujja a kan yanka hadaya kafin ranar Idi, da rangwamen da Manzon Allah (sallallahu alaihi Wasallam) ya tabbatar wa wadanda suka gabatar da aski kafin yanka, ko suka gabatar da dawafi da Sa'ayi kafin aski, su ma hujjarsu mai rauni ce. Domin wadannan abubuwa sun faru ne a cikin rana daya, watau ranar salla, ba wai kafin wannan rana ba. Saboda haka, a yi hattara wajen saba wa irin yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi umurni da aikata wani aiki.

Amma Fidiya (watau dabbar da ake yankawa saboda wata larura da ta hana maniyyaci aikata wani abu daga cikin aikin Hajji), za a iya yanka ta kafin ranar Idi. Domin Hadisi ya tabbata cewa wani sahabi da yake fama da larura a kansa, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umurce shi da ya aske kansa, ya yi azumi ko ya ciyar da miskinai ko ya yanka fidiya, ba tare da ya Kayyade masa da ranar salla ba.

5. Bayan an yi aski, sai a je a yi dawaful Ifadha, wanda yake shi ma rukuni ne daga cikin rukunan aikin Hajji. An fi son a yi shi ranar Idi, kuma shi ba a yin sassarfa a cikinsa. Haka kuma mai yin Hajjin tamattu'i zai iya hada dawaful Ifadha da Sa'ayi a lokaci daya, ko kuma ya yi su dabam-daban. Idan ba a samu damar yin dawaful Ifadha a ranar idi ba, ana iya yinsa daga wannan rana har zuwa Karshen kwanakin Mina. Amma an fi son a kasance cikin ihrami har zuwa lokacin da za a samu damar yin dawafi. Domin Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa: "HaKiKa wannan ranar rangwame ne a gareku: idan kun yi jifar Jamrah, komai ya halasta a gareku, ban da mata (watau ba za ku sadu da su ba tukuna). Idan kuka kai yammaci ba ku samu yin dawafin wannan dakin ba, (watau har rana ta fadi), haramci ya sake komawa a gareku kamar yadda kuke da farko kafin ku yi jifar Jamrah." Ke nan, za a sake mayar da ihrami.

33. Tambaya: Wace irin ibada ya kamata mahajjaci ya yi a kwanakin Mina, bayan salla, kuma menene ya kamata ya nisanta?

Amsa: Ibadar da ya kamata mahajjaci ya yi a kwanakin Mina bayan salla su ne kamar haka:

Ø Jifar Jamraat: A rana ta daya da ta biyu da ta uku bayan salla (watau 11-13 ga watan Zul Hijjah) ana jifar jamrori guda uku da ke Mina. Ana yin jifar ne bayan rana ta yi zawali. Ba a yinsa da safe, domin babu wani dalili a cikin littafin Allah ko Hadisan Manzon Allah (Sallahu alaihi Wasallam) ko ayyukan magabata na Kwarai da ke nuna halascin yin jifa da safe ko da hantsi kafin rana ta yi zawali. Amma wanda yake da uzuri, ko wadanda suke da rauni, ko masu gudun cunkoso, za su iya jifar jamrorin da yamma ko da daddare, matuKar dai alfijir bai keto ba.

Dalili a kan haka na cikin Hadisin da ya tabbata daga Abdullahi bn Abbas (Allah Ya yarda da su) ya ce: "Manzon Allah (Sallahu alaihi Wasallam) ya kasance ana yi masa tambayoyi a cikin Mina ranar Idi: Wani ya ce na yi aski kafin in yi yanka, sai ya ce babu komai, wani ya ce na yi jifa bayan yammaci, sai ya ce babu komai."

Wannan Hadisi yana nuna mana cewa yin jifa da yamma ya halasta, domin haka, mara lafiya, da duk wani mai uzuri, za su iya jira, har sai da yamma, sa’an nan, su je su yi jifa.

Haka nan, Hadisi ya tabbata a cikin Muwadda Malik daga Nafi’u ya ce: "Akwai wata mace `yar dan’uwan Safiyya bint Abi Ubaid da ta haihu a Muzdalifa, ba ta samu isowa Mina ba, sai bayan hudowar rana ita da Safiyya. Sai Abdullahi bn Umar ya umurce su da su yi jifa bayan faduwar rana, kuma ba komai a kansu." Haka nan Hadisi ya tabbata daga Nafi’u daga Abdullahi bn Umar (Allah Ya yarda da su) yana cewa: "Ka da ku yi jifa a ranaku uku (na Mina) sai bayan rana ta yi zawali."

Ibnu Abdil-Barr, a cikin sharhin wannan Hadisin ya ce: "Wannan fatawa (ta Ibn Umar) ita ce Sunna a wurin dukanin malamai; babu wani sabani a kanta." Ya Kara da cewa: "Menene hukuncin wanda ya yi jifa kafin zawali a wadannan ranaku? Sai ya ce: "Malamai sun tafi a kan cewa ya sake maimaita wannan jifar bayan rana ta yi zawali. A cikinsu akwai Imam Malik da Shafi'i, da mabiyansu, da Imam at-Thauri, da Imam Ahmad, da IshaK.

Haka nan, Imam Malik ya ruwaito daga Adaa’u bn Abi Rabah cewa ya ji an yi rangwame ga masu kiwon dabbobi wadanda suke da uzuri, da su yi jifa da daddare.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai yi jifa a ranaku uku na Mina ba sai bayan zawali, ga shi kuwa Hadisi ya tabbata daga Jabir bn Abdullah (Allah Ya yarda da su) cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Ku riKi ayyukan Hajjinku daga gare ni …" Kuma haka sahabbansa suka aikata, ba tare da an samu wani sabani a kan haka ba.

Sanannen abu ne kuwa cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Wanda duk ya aikata wani aiki da ba shi cikin al’amarinmu (na addini da muka karantar), to za a mayar masa (watau ba za a karba ba)." A cikin wata ruwayar: "Wanda duk ya Kaga wani abu a cikin al’amarinmu (na addini) da babu shi a ciki, za a mayar masa." Don haka, lallai ne mahajjata su nisanci yin jifa kafin zawali a cikin wadannan ranaku.

 

Yin jifa bayan zawali shi ne abin da ya tabbata a cikin Muwadda ta Imam Malik, kamar yadda ya gabata. Amma abin mamaki shi ne, wani lokaci sai ka ga wadanda ke da’awar cewa su ne masoya Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), kuma wai su ne suka fi kowa bin mazhabar malikiyya suna jifa da safe. Idan ka tambaye su, sai su ce wai malamai sun ba da fatawa da halascin haka, kuma wannan ita ce maganar Imam Abu Hanifa. Irin wadannan mutane ba su san cewa malaman ba su da wata hujja ba, kuma shi kansa Abu Hanifa, manya-manyan almajiransa guda biyu, watau Abu Yusuf da Muhammad as-Shaibani sun saba masa, kasancewar babu dalili sahihi a kan fatawarsa.

Ya kamata duk masoyin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wasallam) na haKiKa a gan shi yana aiki da karantarwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) sau da Kafa, gwargwadon iko. Haka nan, cikar bin mazhabi shi ne a ga mutum yana KoKarin bin abin da Imam Malik ya yi fatawa matuKar bai saba wa AlKur’an da Sunnar Manzon Allah (Sallallau alaihi Wasallam) ba.

Saboda haka ana kira ga mahajjata da su yi hattara da irin wadannan fatawoyi. Idan kuwa suna da'awar uzuri ne, to ya kyautu a fahimci irin fatawar da magabata suka yi a kan masu uzuri. Watau an halasta masu yin jifa bayan faduwar rana ko kuma da daddare, kamar yadda hujjoji suka tabbata a can baya.

Ø Idan aka zo wajen jifa a rana ta biyu, sai a fara da Jamra ta farko, wacce take kusa da Mina. Za a yi addu’a bayan jifar, sa’an nan a Karasa wurin wacce ke binta, watau ta tsakiya, a yi irin yadda aka yi a ta farko. Daga nan, sai a Karasa wajen Jamra ta uku, watau babbar Jamra, wacce ke kusa da Makka, a yi jifa. Amma ba a tsayawa a wurin don yin addu’a, bayan an yi jifar. Yadda aka yi a rana ta farko kashegarin sallar idi, shi ne za a yi a sauran ranakun Mina.

Ø A kowace Jamra ana yin jifa da tsakwankwani guda bakwai ne kawai. Kenan idan aka hada su za a samu tsakuwa ashirin da daya (21) a kowace rana.

Ø Bayan an yi jifa, ana son a yawaita yin zikiri da hailala da hamdala da Salatin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam), musamman bayan idar da salla. Haka nan, ana son a yawaita fadin

الله اكبر الله اكبر لآاله الآالله الله اكبر الله اكبر ولله الحمد

Haka kuma a rinKa yawan godewa Allah bisa ni'imar da Ya yi, ta kammala aikin Hajji lafiya; sa’an nan a rinKa sa rai da kyautata tsammanin ko Allah Ya karbi aikin Hajjin ko Bai karba ba. Watau a kasance (بين الخوف والرجاء). HaKiKa yin haka shi ne siffofin Annabawa a cikin ibadarsu

Haka kuma ana son a zauna a Mina na tsawon kwanaki uku, tare da cewa idan an kwana biyu kawai, ya wadatar. Amma yin kwana ukun shi ne ya fi. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da sahabbansa kwana uku suka yi, ba kwana biyu ba., kuma babu shakka, yin hakan shi ne ya fi cika wajen tsoron Allah, kamar yadda AlKur’ani ya bayyana.

Amma a halin yanzu mafi yawancin mutane sun manta da wannan Sunnar, kai ka ce wadannan kwanaki ukun ma babu su kwata-kwata. Abin da ya fi daure kai shi ne, da wuya ka ga manyan malamai da ake koyi da su, kuma ake sauraren maganarsu, sun cika kwana ukun. Don haka, ko da yake Shari’a ba ta zargi wanda ya bar Mina bayan kwana biyu ba, ya kamata, musamman malamai su rinKa dagewa wajen cika kwanakin Mina, don su ba da kyakkyawan misali.Allah Ya sa mu dace.

Dangane da abubuwan da mahajjata ya kamata su nisanta a kwanakin Mina, wajibi ne su nisanci duk wani nau’i na sabon Allah, da ayyukan zubar da mutunci. Amma idan mutum ya dubi abubuwan da wadansu suke aikatawa da bai dace ba a Mina, akwai ban tsoro, musamman ga wanda bai taba zuwa ba. Domin za ka ga wadansu mutane, musamman mutanen Afrika ta yamma, suna yin fito na fito da Allah Ta’ala, suna saba masa a sarari, kai ka ce ba aikin Hajji suke yi ba. Wani lokaci sai ka ga mace ta caba ado da kwalliyar da ke jawo hankalin maza. Abin bai tsaya ma a nan ba, har da dauke-dauken hotuna a cikin hemomi, da cakuduwa tsakanin maza da mata, ta yadda hakan zai haifar da fitinar zina. An sha kama irin wannan laifin, ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Hakan kuwa na faruwa ne, ta wajen musamman karuwai da suke zaune a Jidda da wadansu takari da ba su samun dammar yin fasadi a birnin Makka. Wani lokaci sai ka ga karuwan sun dungumo sun zo Mina, suna jan hankalin mahajjata, domin su yi fasadi da rashin mutunci a wannan wuri mai albarka. Haka nan, wani lokaci ana samun wadansu marasa tsoron Allah da suke biye wa barayi, su yi ta sace-sace a wannan Kasa mai tsarki.

To, muna kira da babbar murya ga hukumomin alhazai da su yi aiki tuKuru wajen magance wannan fasadi. Lallai ne su dauki mataki mai karfi a kan haka. Domin babu wanda ya fi Karfin doka. Idan kuma ba za a iya daukar mataki a can Kasa mai tsarki ba, to sai a bari idan an dawo gida, a hukunta su daidai gwargwadon irin laifin da suka yi.

34. Tambaya: Menene hukuncin matar da ba ta yi dawaful Ifadha ba saboda wani uzuri, ga shi kuma jirginsu zai tashi?

Amsa: dawaful Ifadha (watau dawafin Hajji), na daga cikin rukunai ko wajibai na aikin Hajji. Don haka, mace za ta iya canza jirgi saboda ta samu damar yin wannan dawafi. Wajibi ne hukumar alhazai ta taimaka mata, don ganin ta samu cikakken aikin Hajji. Dalili a kan haka, na cikin Hadisin da ya tabbata daga Nana Aísha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: "Na ce wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam): HaKiKa Safiyyah bnt Huyayy tana cikin (jinin) aláda. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Shin za ta tsare mu kenan? Shin ba ta yi dawafi (na Ifadha) da ku ba? Sai suka ce: Eh (ta yi). Sai ya ce: "To mu tafi …."

Saboda haka, matan da suka samu irin wannan larura, su yi hattara wajen gaggawar zuwa Jidda domin neman tafiya gida, ba tare da sun yi dawaful Ifadha ba. Idan kuwa dawaful Wadaa’ (watau dawafin ban kwana) ne ba su samu yi ba, saboda wannan larura, to an yafe masu.

Tare da cewa akwai wata ruwaya cikin fatawar Imam Ahmad da Abu Hanifa, wacce Ibn Taimiyyah ya Karfafa, cewa mace za ta iya yin dawaful Ifadha, alhalin tana cikin jinin al'ada. Dalilinsu kuwa shi ne fadin Allah Ta'ala:

فا تقو ا الله ما استطعتم

Ma’ana: "… Ku ji tsoron Allah gwargwadon ikonku ..."

Suka ce: tun da wannan shi ne abin da za ta iya kawai, babu laifi a kanta idan ta yi dawafi a cikin wannan hali.

Haka nan, sun kafa hujja da abin day a tabbata a Sunna cewa duk mutumin da ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, wajibi ne ya gaggauta barin Makka da zarar ya kammala ayyukan da suka kawo shi, domin mutuwar muhajiri a Makka, na da hadari game da cikar ladar hijirarsa. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya hana muhajiri ya zauna a Makka fiye da kwana uku, bayan dawowa daga Mina. Saán nan kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi alhinin Saád bn Khaulah (Allah Ya yarda da shi) saboda mutuwar da ya yi a Makka bayan ya yi hijira.

Don haka, Imam Ahmad ya ce: Idan ta yi dawafi a cikin wannan hali, sai ta yanka rago. Imam Abu Hanifa kuwa ya ce: Idan ta yi dawafin, sai ta yanka raKumi."

Tare da wannan bambancin fatawa, maganar jumhur cewa ba za ta yi dawafi ba har sai ta samu tsarki, ita ce ta fi rinjaye.

35. Tambaya: Wane tanadi Shariá ta yi game da ziyarar Madina, birnin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam)?

Amsa: Farkon abin da ya kamata a yi idan an isa garin Madina shi ne:

· Ziyarar masallacin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Wannan ziyara Sunna ce, ko da kuwa ba lokacin aikin Hajji ne ba. HaKiKa an kwadaitar da mu cewa, ana iya niKar gari a tafi dayan masallatai guda uku: masallacin Makka da masallacin Madina da masallacin AKsa domin yin ziyara. Saboda haka, idan an samu ikon zuwa Madina, farkon abin da mutum zai yi shi ne alwalla, ya shiga cikin masallacin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cikin ladabi da natsuwa. Ya yi adduár shiga masallaci kamar haka: اللهم أفتح لي أبواب رحمتك . Daga nan, sai ya yi nafila ta gaisuwar masallaci, domin yin salla a cikinsa ya fi salla dubu a waninsa, idan dai ba masallacin haramin Makka ba ne. Dalili kuwa shi ne Hadisin da ya tabbata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Sallah a masallaci na, ya fi salla dubu a sauran masallatai in ban da masallacin harami (Makka)." Haka nan, Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi) ya ce: "Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) shi ne Karshen Annabawa, kuma masallacinsa shi ne Karshen masallacin Annabawa."

Amma Imam al-Kadhi Iyadh na ganin cewa Kasar Madina ta fi Kasar Makka, sai dai masallacin Makka ya fi masallacin Madina falala, domin Kabarin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) a Madina yake. Ya Kara da cewa: "Malamai sun hadu a kan cewa wurin da aka bizne Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya fi kowane wuri a duniya, daga nan sai Makka, daga nan sai Madina." Domin haka, idan mutum ya je Madina sai ya shiga masallacin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) cikin ladabi, sai ya fara Tahiyyatul Masjid (watau sallar nafila raka'a biyu ta gaisuwar masallaci).

Ana son idan mutum ya samu iko, ya yi nafilar a wurin da ake kira Raudhah, saboda Hadisin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da ke cewa: "Tsakanin gidana da mimbari na, dausayi ne daga cikin dausayoyin aljanna, kuma mimbari na yana kan tafkina."

Allah Ya sa mu daga cikin wadanda za su ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), kuma su sha ruwan tafkinsa a ranar Kiyama, amin

· Daga nan, sai a Karasa wajen Kabarin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) don a yi masa sallama da salati, ana tafiya cikin ladabi. Idan an kusanci Kabarin, sai a sassauta murya, ba tare da hayaniya ba, kuma a tafi cikin natsuwa. Domin daga murya a wajen da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yake, rashin ladabi ne. Kuma Allah Ya hana mu daga murya sama da ta Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Idan an isa wurin sai a yi sallama gare shi, a ce: السلام عليك يا رسول الله, kuma a yi salati a gare shi kamar haka:

اللهم صلى على محمد وعلى ال محمد كما صليت على ابرهيم وعلى ال ابرهيم انك حميد مجيد وبا رك عل محمد وعلى ال محمد كما با ركت على ابرهيم وعلى ال ابرهيم انك حميد مجيد

Daga nan sai a matsa dama kadan, daidai Kabarin Sayyidina Abubakar SiddiK (Allah Ya yarda da shi), a ce:

السلآم عليك يا أبا بكرالصد يق جزاكم الله عنا وعن الإسلام خيرا

Daga nan sai a Kara matsawa dama kadan, daidai Kabarin Sayyidina Umar (Allah Ya yarda da shi), a ce:

السلآم عليك يا عمر الفا روق جزا كم الله عنا وعن الإسلام خيرا

Daga nan, an kammala ziyara a masallacin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Sai dai a yi KoKarin lazimtar salloli a masallacin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam), matuKar ana cikin birnin Madina, a cikin Koshin lafiya.

Yana daga cikin ladabi rashin shafar Karafunan da aka kange Kabarin da su. Domin shafar ta su ba shi daga cikin Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Kuma a sani cewa ana iya fadawa ga halaka, musamman idan aka Kudurta cewa wadannan Karafuna za su iya jawo wa mutum alheri ko su kawar masa da wani sharri.

Babu shakka, ana neman tabarruki da jikin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), da gashinsa, da guminsa, da jininsa, da tufafinsa, da duk wani abu da ya danganci jikinsa mai albarka (Sallallahu alaihi Wasallam). Kuma babu shakka jikin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya fi jikin kowane irin dan Adam. Domin Hadisi ya tabbata daga Nana Asma'u (Allah Ya yarda da ita) ta ce: "Mu kan wanke rigar Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam), mu ba mara lafiya ruwan ya sha, kuma ya warke da izinin Allah. Haka nan, mata sukan zuba gumin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) a cikin turarensu, sai ya zama ya fi turaren almiski Kamshi." Wannan kadan ne daga cikin Hadisan da ke bayani dangane da neman tabarruki da gangar jikin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).

To, menene ya hada wadannan Karafuna da jikin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) tsarkakakke? HaKiKa, wadanda suke kwadaitarwa da shafa jikin Karfen da sunan nuna Kauna ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), ba su da wata hujja. Hasali ma, yin hakan, ba alama ce ta son Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ba. Saboda haka, lallai ne a yi hattara.

Lallai ne a nisanci fuskantar Kabarin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da na sahabbansa don yin adduá ta neman biyan buKata. HaKiKa, Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ba ta karantar da yin haka ba. Sahabbai da sauran magabata na Kwarai ba su kasance suna yin haka ba. Hasali ma, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya hana fuskantar Kabari domin yin salla ko neman biyan buKata.

· Bayan kammala yi wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da sahabbansa sallama, sai a ziyarci maKabartar Shahidai a Uhud, inda Kabarin sayyidina Hamza da sauran manyan sahabbai yake. Idan mai ziyara ya je, sai ya yi masu sallama, kuma ya nema masu gafara, da irin lafazin da ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam), kamar haka:

السلآم عليكم أهل الديا رمن المؤمنين وا لمسلمين وانا ان شاء الله بكم لآحقون أسأ ل الله لنا ولكم العا فية

· Daga nan kuma sai a tafi maKabartar BaKiáh, inda mafi yawan Sahabbai suke kwance, don yin adduá a gare su, kamar yadda aka yi a Uhud.

· Daga nan sai mai ziyara ya nufi masallacin Kuba. Ana son a yi alwala a gida (watau a masauki) da safe, domin a isa can a daidai lokacin sallar walha. Kuma an fi son a je a ranar Asabar idan akwai ikon yin hakan. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance yana zuwa masallacin Kuba duk ranar Asabar don yin ziyara.

Idan aka je, sai a yi salla raka'a biyu a natse, kuma a roKi dukanin buKatu a cikin sallar (lokacin sujuda ko tahiya).

Wadannan ziyarce-ziyarce su ne suka tabbata a cikin Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da aikin Magabata na Kwarai. Ban da su, ba a zuwa wani wuri da sunan ziyara ta ibada, sai dai kawai don tarihi ko bude ido.

Amma mutum zai yi matuKar mamaki idan ya dubi yadda mutane ke yin hanKoro wajen zuwa wadansu wurare da sunan ziyara ta ibada, ban da wadanda aka bayyana a sama. Ziyarar irin wadannan wurare ba da sunan tarihi ko bude ido ba, ba shi da asali kwata-kwata a cikin karantarwar Musulunci. Hasali ma, kuskure ne babba ga mutum ya yi takakkiya zuwa wadannan wurare don yin salla ko adduá, da sauransu.

Daga cikin irin wadannan wurare akwai:

1. Wani wuri da ake kira masallatai bakwai wanda ake zuwa a yi raka'a biyu a kowane daya daga cikinsu.

2. Wata rijiya da ake cewa wai zoben Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya fada ciki. Mutane na zuwa shan ruwa a cikinta, alhalin ruwan gonakin 'yan Kauye ne da suke zubawa, suna ba mutane. Wadansu mutanen ma har zobbansu suke jefawa a cikin rijiyar. Duk wadannan abubuwa ba su da asali daga Allah ko ManzonSa (Sallallahu alaihi wasallama) ko aikin magabata na Kwarai.

3. Masallacin da mutane ke kiransa Kiblataini. Suna zuwa can don yin sallar nafila da adduóí na neman biyan buKata. Abin mamaki ma, har da wadanda ke daáwar ilmi, tare da cewa hakan bai tabbata ba a cikin Sunna. Hasali ma, tarihi na tabbatar da rashin gaskiyar haka. Sanannen abu ne cewa babu wani masallaci mai suna Kiblataini in ban da masallacin Kuba. Hadisi ya tabbata a cikin sahihul Bukhari cewa masallacin Kuba shi ne Kiblataini.

4. Wani kogo da ake ziyara a cikin dutsen Uhud, wanda wadansu ke riyawar cewa wai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya boye a cikinsa yayin da yaKin Uhudu ya yi zafi. Wannan Kissa ce maras asali da tushe, wadda jahilai suka KirKiro. Lallai ne a sani cewa bai kamata mutum ya fadi haka ba, ballantana har ya kai ziyara wurin, domin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai ja da baya a fagen yaKi ba, ballantana ya buya. Kudurta hakan ma, kafirci ne.

Bayan wannan, akwai wata magana da aka KirKiro cewa sai mutum ya yi kwana takwas (8) a Madina, domin ya samu damar yin salloli guda arbaín. Aka Kara da cewa yin salloli guda arbaín din na da wata falala ta musamman.Wannan iyakancewar ba ta da wani asali, domin kuwa an ciro ta ne daga wata magana mara asali da ake dangana wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Tabbataccen abu shi ne mutum zai iya yin sama da kwana takwas ko Kasa da haka, gwargwadon yadda Allah Ya ba shi iko.

36. Tambaya: Menene hukuncin wanda ya isa Jidda, amma hukumar Saudiyya ta hana shi shiga Makka, saboda kasancewar garin da ya fito ana annoba ko saboda wani dalili?

Amsa: Wanda hukumar Saudiyya ta tsare shi a Jidda saboda wata doka ko annoba a Kasarsu, sai ya yi aski, ya cire ihraminsa, idan dai ya daura haraminsa a cikin jirgi, kuma ya yi niyyar ramuwar wannan Hajjin a shekara mai zuwa idan Allah Ya ba shi ikon zuwa. Amma wadanda ba su dauki ihraminsu ba, sai sun isa Jidda, ba wani abu a kansu, kasancewar ba su riga sun shiga aikin ibada na Hajji ko Umrah ba, ballantana a ce su yi aski ko su cire kayansu.

Idan kuwa zai samu wucewa Madina kai tsaye, ta yadda zai dauki ihraminsa a miKatin mutanen Madina a kan hanyarsa ta zuwa Makka daga Madina, to babu komai a kansa tunda bai riga ya fara ibada ba.

 

37. Tambaya: Wadanne irin nasihohi za a yi wa hukumomin alhazai da su kansu alhazai?

Amsa: Nasihohin da za mu yi wa hukumomin alhazai da su kansu alhazai su ne:

1. Da farko, ya kamata hukumomin Alhazai su riKa ba da gamsasshen ilmi ga mahajjata tun daga nan gida har zuwa Kasa mai tsarki a kan karantarwar AlKuráni da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bisa fahimtar magabata na Kwarai. Wannan shi ne zai bai wa kowane Alhaji damar yin aikin Hajji cikin ilmi da basira. Haka kuwa ba zai yiwu ba, sai an samu malamai masu ilmi da tsoron Allah, wadanda suka san yadda ake aikin Hajji. Kuma lallai ne idan za a zabi malaman, ya kasance ba tsarin alfarma ko son zuciya aka bi ba, watau a zabi wadanda za su bayar da wannan amanar da aka dora masu yadda ya dace.

2. Sa'an nan kuma ya kamata wadanda aka dora wa nauyin kula da jin dadin alhazai su kasance masu kyawawan halaye da hakuri, da sanin ya kamata. Kuma su kasance sun san garin Makka da Madina da sauran wuraren ibada sosai, domin rashin sanin wadannan wurare na daga dalilan da ke sanya mahajjata su wahala a wajen aikin Hajji. Wani lokaci sai ka ga mahajjaci, musamman sabon Alhaji, ya bata a cikin gari, har ma ka ji ana cewa ya yi kwana da kwanaki yana garari, ya rasa inda masaukinsa yake. A dalilin wannan, sai Alhaji ya tagayyara saboda yunwa da wahala, wani lokacin ma, hakan ya kai shi ga rasa rayuwarsa, ko kuma ya kamu da cututtukan da za su kai shi ga halaka.

3. Haka nan, yana da matuKar muhimmanci hukumar jin dadin alhazai su fitar da taswirar Kasa mai tsarki a wajen bita, domin su nuna wa mahajjata wuraren ibada a cikin Makka da Madina da Mina, da Arfa, da Muzdalifa da sauran wurare, tare da hanyoyin unguwannin Makka da Madina wadanda za su kai Alhaji harami, musamman ma manyan titunan da ke kewaye da masallaci mai alfarma, ta yadda duk inda suka bi, ko sun bata, za su iya gane hanyarsu ta komawa masauki.

4. Yana da kyau a samu Kwararrun likitoci da za su riKa gaya wa mahajjata hanyoyin da za su kula da lafiyarsu tun daga nan gida har zuwa Kasa mai tsarki, musamman a wuraren cunkoso da wajen cin abinci ko abin sha.

5. Ya kamata hukumomin alhazai su rinKa tace matan da za su dora wa kula da walwalar mata `yanúwansu, ta yadda za su samu mata masu mutunci, ba wadanda za su je su riKa bata mutuncinsu da mutuncin Kasarsu a Kasa mai tsarki ba.

6. Kuma yana da matuKar muhimmanci hukumomin alhazai su riKa tuntubar hukumomin alhazai na Kasashen Musulmi, kamar Indonesia, Malaysia da sauran Kasashen da ke da kyakkyawan tsarin gudanar da alhazansu, domin su duba yiwuwar koyi da su.

7. Sa'an nan ya kamata hukuma ta ji tsoron Allah, ta duba kamfanonin jirage masu amana da cika alKawari, wadanda jiragensu suke da lafiya da nagarta, ba wadanda za su riKa wahalar da al'umma ba, ko da ba za su samu riba mai yawa ba. Saboda mafi yawan kamfanonin jirage suna Kyale alhazai ne a Jidda, bayan an gama aikin Hajji. Za ka ga a irin wannnan hali alhazai na tagayyara, wadansu ma, a nan suke kamuwa da rashin lafiya, wadansu kuma sai sun sayar da kayansu, sa’an nan su samu dan abin da za su ci. A gaskiya idan aka duba za a ga cewa ba wani abu ne ya jawo haka ba, sai rashin amana da rashin cika alKawari, irin na wadannan kamfanonin jirage.

8. Su kuma alhazai ya kamata su zama masu biyayya da ladabi ga hukumar alhazai, da kuma bin tsarin da hukumomin suka tsara masu. Ka da su je su rinKa rigima da junansu, ko su zo filin jirgi kafin lokacin da aka sanya masu. HaKiKa yin hakan, ba halin Musulmin Kwarai ba ne.

9. Kuma alhazai su ji tsoron Allah, su cire siyasa a cikin aikin Hajji, domin cimma wani buri nasu.

Wannan shi ne Karshen abin da Allah Ta’ala Ya nufa muka yi bayaninsa dangane da aikin Hajji da Umrah da ziyarar Madina. Muna roKon Allah Madaukakin Sarki Ya karba mana ibadarmu, Ya sa aikin Hajjinmu ya zama karbabbe, amin. Kuma abin da muka yi daidai wajen bayaninsa, Allah Ya ba mu ladarsa, wanda muka yi na kura-kurai Allah Ya y afe mana.

Wasallallahu ala Nabiyyina Muhammad wa'alihi wasahbihi wasallam

Enter content here

                                                Wannan shafi babu ruwansa da abinda yake sama