Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

SHEIKH MUHAMMAD NAZEEF INUWA

   An haife shi a unguwar dandago cikin birnin Kano, a shekara ta 1970.Mahaifinsa shine Alhaji Inuwa wanda aka fi sani da Alhaji Inuwa dan mabudi. Yayi karatun Allo a dandago, sannan Islamiyya a unguwar Hausawa. Makarantar Abdulllahi Sika. Sannan yayi karatun Karamar Sakandire a garin Hadejia. Bayan mallam ya haddace alkur'ani sai ya tafi Sudan, yayi babbar Sakandire a Islamic African Centre dake khartoum, anan ne yayi karatun shaidar NCE.
  Bayan Mallam ya dawo gida, sai ya fara aikin gwamnati da ma'aikatar ilmi har na tsawon shekaru biyu, sai ya tafi karo karatu a jami'ar musulunci ta Medina, a can ne yayi digirinsa na farko a fannin koyar da kira'o'in alkur'ani da ilmansa. bayan ya dawo gida, ya tafi hidimar kasa wato NYSC. Daga nan kuma ya tafi Jami'ar Bayero ta Kano don yayi digirinsa na biyu. Yayi diriginsa na biyu ne akan Tafsir bangaren karatu mai zurfi na addinin Musulunci.
  Yanzu haka Mallam yana koyarwa a makarantar sakandire ta Usman Bin affan dake gadon kaya, limancin juma'a na Masallacin Al-muntada dake dorayi cikin birnin Kano kuma shine shugaban makarantar Ruwais Model Primary school.
  Mallam yana da iyali da 'ya'yaye.