Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Sheikh Abdulwahab Abdallah
Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

SHEIKH ABDULWAHAB ABDALLAH -
            IMAM AHLUS-SUNNAH WAL JAMA'A
 Sheikh Abdulwahab bin Mika'il bin Abdullahi bin Muhammad. An fi saninsa da Abdulwahab bin Abdullahi. An haifeshi a ranar 28 ga watan 8 shekara ta 1956 wanda ya dace da ranar Juma'a; 1373 hijirah watan 12 (Babbar Sallah, 17).
Yayi karatu a wajen wan mahaifinsa Alhaji Yahaya dan Imam Abdullahi, ya fara littafan su fikihu, har zuwa risala, a wurin babban almajirin kakansa Alhaji Tahir, wanda yayi karatu a kasar Saudiyya . Sai gidan malam Shamsu a kabara wajen Malam Muhammad Ghali Inuwa, yayi littafan nahawu, ishiriniyya, dasu tafsiril jalalaini da littafan Adab da Madahu. A wajen Liman dan Amu ya karanta Riyadhussalihin. Waraqatul Uslul fiqihu, Nahawul wadhi; 1 dana 2 a wajen Malam Nasiru Kabara. Malam Shehu Mai hula ya karantar dashi Askari amma bai kare ba tafiya ta kama shi zuwa Saudiyya, Jami'ar Islamiyya, a darul hadith Makiyyah a shekara ta 1976, ya fara Mutawassitah (junior) daga nan ya shiga sakandare a jami'ar daga nan kuma kulliyat hadith (degree).
A cikin Malamansa akwai Sheikh Abdul Muhsit Abbad, malamin da yake karatu a Masallacin Madina, Bukhari shekara 4, Muslim 3. Zamansa a Makkah suka haddace karatun Sheikh Uthaimin tafsir, muhaddarorin bin ta wanda yakeyi lokacin Ramadan. Kuma Malami daya karanta Tirmizi da Nahawu. A wurin sa shine Uztaz Sa'id Al - ethiopi, ya nutu yanzu Allah yaji kansa amin, mazaunin Makkah ne, wanda yake bada karatu arewacin ka'aba. Akwai Ustaz Malam yayi karatun Bukhari, Allah yaji kansa, amin.
 Bayan Malam ya dawo Kano 1991 ya cigaba da da'awa a kasar nan, ya bude majalisan karatu a birnin Kano. Yana bada karatun, Bukhari, ranar asabar da lahadi, missalin karfe 10:na safe, mafi yawancin masu halartar yan book ne da yan kasuwa wadanda basa samun zuwa kullum. Akwai Tirmizi kuma wanda akeyi ranar litinin, la'asar zuwa magriba, wadanda daliban ilimi ne suke zuwa a Massalachin gidansa. Ranar talata kuma akwai karatun Subulus - salam da misalin karfe 5:00 na yamma zuwa magariba, a Massalachin Usman bin Affan, wanda daliban ilimi ne suke halarta. Daga magriba kuma a ranar talata din yana bada karatun Abu - Dawud daga magri zuwa Isha'I, ana Usman bin Affan, akwai karatun Buluqul Maram, a Massalachin dake makarantar Ansarul - la - dake unguwar 'yankaba ranar alhamis daga magrib zuwa Isha'I.
 Sai unguwar Gwagwarwa, Massalachin Mu'assasa Abubakar Sadiqu shi kuma ana yin Umdatul Ahkan, tsakanin m,agriba da Isha'I, ranar Asabar.
 Dukkanin wadannan littatafan an tarjamar su zuwa Hausa da turanchi. Amma a halin yanzu ana rubuta na Hausa, banda Ummatul Ahkan da Subus-salam.
 Malam yana nan zaune a unguwar sabuwar Sharada a birnin Kano, yana da 'ya'yaye 15. Haka kuma daya daga cikin matayensa wato Mallama Halima Shitu Musa wadda tayi karatu a Jami'atu Ummul Qura a kasar Saudiyya, yanzu itace shugabar 'yan hisba mata, kuma tana da makarantu guda biyu, akwai Badariyya Islamiyyah (dake unguwar Dan Agundi) da wata a unguwar Gadon Kaya (inda Mallam ya fara zama) wadda aka sanya sunan Mallam, mai dalibai sama da 200. kuma tana gabatar da tafsirin kur'ani a Masallacin Usman bin Affan a watan Ramadan da safe. yana da yaya 15 (maza shida (6) mata (9).