Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Ramadan

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

DA SUNAN ALLAH MAI GAMAMMIYAR RAHAMA MAI JIN KAI.

MAUDU’I- Khutba (Fassara) Ramadan

K/ WATA - 5/10/1424 H 28/11/03 M

MALAMI- Sheikh Ja’far M. Adam

 

Ya ‘yan uwa, Ramadan ya riga ya tafi ya juya baya, kwanakinsa masu dimbin albarka sun shude tare da shi, haka dararensa masu falala ba su tsaya ba, ballantana a wuni da mintinan da watan Ramadan ya kunsa.

Wannan ita ce Sunna Allah a cikin rayuwa babu abin da yake dawwama, duk abin da ya zo zai tafi, shudewar kwanaki, wucewar darare, shela ce Ubangiji (M) kewa bayi cewa, duniya fa farau ce kuma karau, rayuwa dole za ta shude zango bayan zango.

Da kana ciki a matsayin jariri aka haifeka a matsayin sabuwar haihuwa har ka far zama har ka fara tafiya, har ka balaga har ka girma har ka tsufa, to kuma zaka mutu, kila ma ba sai ka tsufa din ba.

" CIKINKU AKWAI WANDA YAKE MUTUWA (TUN YANA YARO) CIKIN KU AKWAI WANDA SAI ANA MAISHE SHI ZUWA KASKANTACCIYAR RAYUWA, YA JAHILCI AL’AMURRAN DA DA YA SANSU, YA MANTA DIMBIN AL’AMURRAN DA DA YANA SANE DA SU SABODA TSUFA, YA RIKICE YA DIMAUCE". (suratul Hajji: aya ta 5)

Ubangiji (M) ya rubuta mana lada dangane da abin da muka azimta na Ramadana, ya rubuta mana ladan tsayuwar da muka yi ta dare, ya gafarta mana gajiyawar da aka samu daga bangaren mu, ko ketare iyakokinmu.

Ya ‘yan uwa bai kamata mu bari Ramadan ya shude haka kawai yadda girgije ke bi ta saman kawunan mu ba tare da mun fa’idantu da wadansu darussa muhimmai a cikinsa ba, wanda akwai darussa masu dimbin yawa wanda ya kamata a ce musulmi yaka ya kalata a cikin watan Ramadan ko a cikin ibada ta azumin watan Ramadan mai dimbin albarka, daya daga cikin muhimman darussan shi ne TAKAWA.

Ubangiji (M) ya nassanta ta cikin littafinsa ya ce:

(suratul Ba]arah: aya ta 183).

Daya daga cikin hikimomin da suka sa aka shar’anta azumi a kanmu, don mu zamto masu takawa.

Shi lafazin takawa abin da yake nufi (اتخاذ الوقاية ) bawa ya riki garkuwa, ya ri]i shamaki, ya sanya karo tsakaninsa da azabar Ubangiji, tsakaninsa da fushin Allah, tsakanin shi da wuta, wannan ita ce hakikanin takawa.

Takawa na nufin lura da abin da zan fada shin zai jawo min yardar Allah ne ko fushinsa kafin in fada, lura da abin da zan aikata shi abu ne na lada zunubi lura abin da zanci a cikin dukkan ruyuwata.

Wani daga cikin magabata an tambayeshi dangane da takawa, ya ce: "Wane hali za ku samu kanku a ciki, yayin da ka ganka a cikin wata gona da ke cike da daya, kuma dole ka yi tafiya tafarka babu takalma". Sai wanda aka tambaya ya ce : " Duk lokacin da na daga kafa ta zan duba in hanga, in hararo har kafin in dora ta inda ya dace, ta yadda ban taka daya ko tsidau ba, ya ce to wannan shi ne hakikanin takawa".

Kada ka ce, kada ka aikata, sai ka tabbatar da cewa abin da zaka aikata din, da abin da za ka ce din zai jawo maka yardar Allah ne ba fushinsa ba. Wannan shi ne hakikanin takawa, kuma daya daga cikin muhimman darussan da Allah ya ce, ya wajabta mana azumin Ramadan irin yadda ya wajabta shi, a kan wa[anda suke kafin mu don mu zama masu takawa : "لعلكم تتقون ".

Darasi Na Biyu - Ciyarwa

A cikin ibadar azumi ta watan Ramadana, akwai koyar da ciyarwa, tun Karon farko lokacin da aka shar’anta azumi a farkon musulunci ko a farkon shar’anta azumi an bayar da za\i wanda ya ga dama ya yi azumi, wanda ko ya ga dama, ya ciyar, shi Allah yake nufi da " وعلى الذين يطيقونه فدية طعام مسكين " (Suratul Bakarah aya ta : 184).

" Wadanda azumi za yi musu wahala to su ciyar da miskini".

Wannan fadakarwa ne dangane da muhimmacin ciyarwa, tun a farkon musulunci kafin a zo a shafe wannan za\i, a mayar da azumi din ya zama tilas ba tare da bada zabin ciyarwa ba.

Tare da haka a cikin azumi kuma Manzon Allah ya ce : " Dukkan mutumin da ya ciyar da mai azumi, to, za a bashi lada na adadin mutanen da ya ciyar abincin buda baki, ba tare da an tauye ladan su ba.

Haka kuma cikin wannan hadisin an nuna cewa ashe ciyarwa na daya daga cikin muhimman darussa da za a koya a cikin Ramadan, sannan kuma Manzon Allah (M) ya wajabta kaffara ga mutumin da ya sadu da mace da rana, kuma ya sanya daya daga cikin ababen da ake yin kaffara da shi guda uku: -

Daya daga cikinsu, ciyar da miskini sittin Bukhari ne ruwaito, haka dai duk a cikin wannan zamu kalaci cewa ashe ciyarwa na daya daga cikin muhimman darussa da ake son mai azumi ya koya a cikin watan Ramadana, ta yadda idan ya iya sai ya ci gaba da ciyarwa ko da a wajen Ramadana.

Sannan kuma akwai nau’ikan mutane da basa yin azumi, a madadin ramuwa, sai aka ce su ciyar, duk wannan shela ce, da koyarwa, da kiran mutane zuwa ga muhimmacin ciyarwa, don haka dai ciyarwa na da matukar muhimmanci ta yadda takai matsayi, yana daga cikin abin da za atuhumci kafirai, don me ba su yi shi ba a ranar tashin kiyama? Doriya a akan su kafirai ne, su mushrikai ne, sai kuma a caje su, an tuhumce su, don me bakwa ciyar da miskini kuma bakwa kwadaitarwa a kan ciyar da miskini? Ubangiji (M) ya ce:

" Ku kama shi, ku daure shi a cikin wata sar]a wadda tsawonta ya kai zira’I saba’in". Zira’i saba’in nawa? Na Mala’iku ko na dan Adam? To zira’I saba’in dai ko da na mutumin da ya fi kowa gajarta a duniya ne, ai sar]ar za tai tsawo, da ita za a sa mala’ikun su daure mutum a ranar tashin kaiyama ballantana kuma kila zira’I saba’in a awon mala’iku.

" ku kama shi, ku daure shi, ku jefa shi cikin wuta".

Sai Ubangiji (M) ya kawo jumla "تعليلية " kamar mai tambaya ya yi tambaya, Me ya sa za a yi masa wannan u]uba, da wannan dauri na tamau, a jefa shi cikin wuta? Sai Allah ya ce :

" saboda ya kasance baya imani da Allah mai girma, sannan kuma ya kasance, baya kwadaitarwa (baya zaburarwa) wajen ciyar da miskini". Wato wajen ciyar da gajiyayye) sannan kuma za a tambayi ‘yan wuta bayan an jefa su cikin wuta :

" Me ya shigar da ku cikin wuta?". Sai su yi bayanin laifukansu :

Za su ce : " Mun kasance ba ma yin sallah, mun kasance bama ciyar da miskinai, mun kasance muna tsoma baki yayin da mutane ke yin izgili wa addinin, muma sai mu sa bakinmu cikin, mun kasance muna karyata tashin kiyama har mutuwa ta zo mana". (suratul Muddasir aya ta 43-46).

Ka ga cikin laifukansu, akwai rashin ciyarwa, ashe ciyarwa na daya daga cikin muhimman al’amurra da ya kamata mai azumi ya koya a cikin watan Ramadan, saboda ayoyi da muka yi ishara zuwa gare su.

Darasi na hu[u daga cikin muhimman darussa, rayar da dararen mu da ibada.

Sallar dare mustahabbi ce a kowane dare ba sai cikin watan Ramadana ba abin kwadaitarwa ne, wajibi ce cikin hakkin Annabi (s.a.w) mustahabbi a kan mu Ubangiji ya ce da shi:

(Suratul Isra’i: aya ta 79)

" Mutumin da duk ya rayu cikin Ramadana ya zamto cikin wadanda Allah ya azurta da halartar sallahr dare, a cikin masallacin da ake samun limamai gwanaye wajen karanta Alkur’ani, da bashi hakkinsa wajen karanta shi, da tsawaita tsayuwa da tsawaita ruku’I da sujada, tsawon wata daya sai ya zamto kamar mutum ya shiga wuta makaranta ne ta horo ta yadda zai koyi kiyamul laili a ragowar kwanaki bayan shudewr Ramadana a ragowar watanni bayan shudewar Ramadana. Mutum ya dinga kokawar a sa shi cikin rijista ta:

" Bayin da suke kwana suna masu sujada da tsayuwa domin Ubangiji". Ramadan na koyar da mu wannan da mutum ya kasance cikin bayin da Ubangiji (s.a.w) ya daukaka ambatonsu, ya yabe su da siffar su ba da sunayen su ba.

"Wadanda suke yin nesa da inda ake dora hakarkari, da su tsaya cikin dare, suna bautar Ubangiji, suna masu kaskantar da kai a gare Shi".

Ko shakka babu kiyamullaili abu ne na gari, kiyamullaili ibada ce mai falala, Manzon Allah (s.a.w) ya ce: " نعم الرجل عبد الله لو كان يصلي من الليل ". (Bukhari ne ya ruwaito) ya ce: Madallah da mutum Abdullahi dan Umar, wannan jumla ce mai zaman kanta, zance ya cika, Abdullahi dan Umar ya sami yabo, sai kuma Manzon Allah ya kara kawo wata jimlar, ya ce: " لو كان يصلي من الليل" " Ina ma yanayin ]iyamul laili". Abdullahi dan Umar da ya ji wannan maganar sai ya ce, bai ]ara fashin ]iyamul laili ba har ya zuwa lokacin da ya fadi hadisin, ya ce kuma har ya zuwa lokacin mutuwarsa in sha Allah, saboda falalar da take cikin kiyamul laili wadda tana daga cikin darussa da ake koya a Ramadan.

Na hudu, kulla alaka tsakaninka da Alkur’ani mai girma wajenka karanta shi da kanka ko ka saurara, da yawan mu bana samun sukunin karanta Alkur’ani ko sauraronsa a cikin wadansu kwanaki na daban, ko watanni na daban, ba watan Ramadana ba, ba kwanaki Ramadana ba, Alkur’ani ko mai ceto ne, Alkur’ani haske ne, Alkur’ani shiriya ne, Alkur’ani rahama ce Alkur’ani waraka ce, Alkur’ani hujja ce :

(Suratu Yunus: aya ta 57).

Wannan duk sifofi ne Alkur’ani, wa’azi, waraka, shiriya, rahama ga muminai.

(suratun Nisa’i: aya 174)

Alkur’ani Burhani ne, hujja, sannan kuma nur ne, haske ne :

(suratut Taghabun: aya ta 8).

Kamar yadda muka haskaka da shi a aikin watan Ramadan wajen karanta shi, ko saurarensa ana karantawa ya kamata mu ci gaba da dosanar haskensa a ragowar watanni da kwanaki da ba Ramadana ba, wala alla wajen karanta shi ko kuma sauraron masu karanta shi ko da kuwa a kaset ne, wannan yana daga cikin muhimman darussa, yin haka ne zai sanya Alkur’ani ya cece mu, Alkur’ani ya zame mana haske, ya zama mana haske, ya zame mana shiriya, ya zame mana hujja a ranar tashin kiyama.

Darasi na biyar, yawan kyauta a cikin Ramadan, Manzon Allah ya kasance ya fi kowa kyauta kuma ya kasance kyautarsa tana bunkasa a cikin watan Ramadan lokacin da yake yawan kici\is da Mala’ika Jibril (Bukhari ya ruwaito shi).

Da yawanmu Ubangiji ta’ala ya musu gam da katar ya datar da su ba da dabararsu ba, sun zamto masu kyauta a cikin Ramadan, masu taimakon fa]irai, masu taimakawa gajiyayyu, masu ciyar da muyunwaci masu tufatar da huntaye, ya da ce kwarai da gaske ya kamata cigaba da irin wannan ayyukan na alheri ko da bayan shudewar Ramadan shi aikin alheri, ba wai yinsa ne kadai riba ba, a a ka yi shi ka dawwama a kai har ya zuwa ga mutuwa, saboda idan mutum yayi cikin alheri jiya ko shekaran jiya ma’ana banda yau, bara ko bara waccan, ban da bana watan jiya ko watan shekaran jiya banda watan da muke cikin abin jin tsoro, shi ne kar ya samu kansa a wani \angare na hadisin Manzon Allah (s.a.w) da ya ce:

" إن أحدكم ليعمل بعمل أهل الجنة حتى ما يكون بينها وبينها إلا ذراع فيسبق عليه الكتاب فيعمل بعمل أهل النار فيدخلها". . "

Dayanku, zai iya rayuwa cikin ayyuka na ‘yan aljannah, maganganunsa da ayyukasa, saura kiris, saura taki daya, sauran zira’i daya tsakanin shi da aljanna, kiris ya mutu, sai ya cika da mummunan aiki irin na ‘yan wuta, sai a tashe shi cikin ‘yan wuta ranar tashin kiyama". Ashe ba wai yin aikin ba, zarcewa a kan aikin, ba jiya na yi shekaran jiya na yi ba, in yi yau, tare da fatan da rokon Ubangiji ya sa gobe ma in yi har ya zuwa lokacin rayuwata har ya zuwa karshen ruyuwata. Wannan ita ce ribar dan Adam don haka idan mun yi kyauta a cikin Ramadan bai kamata ba bayan Ramadan mu zama marowata idon mun yi sadaka a cikin watan Ramadan bai kamata ba bayan Ramadana ya shude mu kame hannayenmu.

Darasi na shida, kame harshe Ramadan ya koya mana cewa, ba wai azumi bane kadai mutum ya daina ci ya daina sha’awar ‘ya mace, in har sai ya hada da wadannan din ya zama mai kare harshensa, mai kame bakinsa daga dukkan wani yasasshen zance, dukkan wani harigido, dukkan wani zance mara amfani na duniya ko a lahira, zance na batsa, zance na rashin kirki mutum ya tsarkake harshensa daga gare shi, wannan shi ne hakikanin Ramadan, ba wai wanda ya daina ci ya daina sha ya daina sha’awar ‘ya mace ba, sai ya daina yasasshen zance, maganganu na shirme, soki burutsu, jita jita, yi da mutane, ance- sunce, sai mutum ya nisanci wannan sannan ya zama cikakken mai yin azumin Ramadana. In ko ka yi haka, na yi haka muka yi haka, wannan na nuna kwanaki ashirin da tare da muka yi na Ramadan sun bamu darasi na musamman, na mu dore da kame bakin mu ko da bayan shudewar Ramadan. Dangane da hakkin ‘yan uwanmu dangane da dukkan wani yasasshen zance domin siffa ce ta muminai :

(suratul kasasi : aya ta 55).

"Idan sun ji yasasshen zance, sai su kawar da kai sai su rufe bakinsu, sai su bar wajen":

( Suratul Fur]an: aya ta 72).

"Idan ana magana ta shirme marar amfani, wucewa suke ba sa zama a wajen :

Sai ya zamto mun mayar da wannan ita ce siffar mu ko da bayan Ramadan. Manzon Allah (s.a.w) yace: " من كان يؤمن بالله واليوم الآخر فليقل خيرا أو ليصمت". Wanda ya yi imani da Allah da ranar karshe, to ya fadi alheri ko ya yi shiru.

Darasi na bakwai, hakuri da juriya, Ramadan ya koya mana hakuri da yunwa, hakuri da kishirwa, wani lokacin ga yunwa da kishirwa ga zafin rana, wani lokacin ga wani aikin na wahala da gajiya, wani lokacin ga bacin rai, tare da haka duk muka jure, tsawon awo goma sha biyu, ba mu ci ba, ba mu sha ba, muna da ikon mu ci mu sha din inda mun so, amma tsoron Allah ya hana mu, neman aljanna ya hana mu, sai muka yi hakuri, wannan na taimakon dan Adam wajen ya mayar da hakuri da juriya siffarsa ta dindindin a wajen shi a cikin rayuwarsa gaba daya a cikin dukkan bangaren rayuwa.

Wannan muhimman darussa guda bakwai, na lissafi su ne a matsayin misali ba wai don su ne ka[ai darussan da za a koya a cikin watan Ramadan ba. Ya ‘yan uwa Ramadan ya wuce ya nade shimfidarsa ya yi mana ban kwana, mai dogon kwana ne kadai, mai tsawon rabo, ne kadai zai iya kaiwa wani Ramadan din. Ramadan ya wuce amma wannan baya nufin azumi ya wuce ba, muna da abin koya cikin rayuwar Manzon Allah (s.a.w) ya yi wasici ga Abu Huraira da yin azumi guda uku a cikin kowanne wata, ya kwadaitar dangane da azumi ranar Arfa, ya kwadaitar dangane da azumin Tasu’a da Ashura, ya kwadaitar dangane da yin azumi a karshe wata, kamar yadda ya kwadaitar da yin azumi guda shida cikin nan cikin Shawwal ya ce da mu ciki hadisin da Imam Muslim ya ruwaito : "من صام رمضان ثم أتبعه ستا من شوال كان كصيام الدهر". Wanda duk ya azimci Ramadan ya bi bayansa da kwanaki guda shida a cikin Shawwal, to zai zamto kamar ya yi azumin shekara ke nan. Don haka ya [an uwa na musulmi, yi kwadayin azimtar wadannan kwanaki guda shida. Ya ‘yar uwa yi kwadayi ki azimci wadannan kwanaki guda shida, kana da damar azumtar su a jere ko a ware, duk wanda ka yi ya yi, ba lallai ba ne sai sun biyo bayan Ramadan dab dab, ka iya yin su cikin goman farko ko goman tsakiya ko goman karshe al muhim, ka azimce su cikin wannan wata na Shawwal suna da matukar falala, ba wajibi ba ne amma suna da dimbin falala wadda Manzon Allah (s.a.w) ya bayyana mana cikin hadisi.

Allah ya sa mu dace.