Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

 

DA SUNAN ALLAH MAI GAMAMMIYAR RAHAMA MAI JIN KAI.

 

MAUDU'I- Musulunci, Imani da Kyawawan Aiki (Al-birru)

K/ WATA - 12/11/1424 H         24/12/04 M

MALAMI-           Sheikh Ja'far Mahmud Adam

 

         

'Yan uwa, addinin musulunci addini ne ckakke, kamulalle, babu tawaya tattare dashi, babu cikas a cikin hukunce-hukuncensa. Addini ne day a kunshi dukkan bangarorin rayuwa, rayuwar dan Adam tsakaninsa da mahaliccinsa, da rayuwarsa tsakaninsa da bil Adama 'yan uwansa.

Addini ne day a kunshi dukkan kai kawo na dan Adam, abinda yakamata ya kudurce a zuci da abinda yakamata ya aiwatar da gabbansa. Addini ne cikakke bayab bukatar karashe. Addini ne wanda ya kunshi kowane bangare na rayuwa, musulmi bas a bukatar aro, ciko daga wurin waninsu. Ubangiji ta'ala yace:

 

          "A yau na cika muku addininku, kuma na cika ni'imata a        gareku, kuma na yardarm muku Musulunci ya zama shine         addiniku."

Cika addini na nufin baya bukatar kari, domin babu ragowa ko cikas a cikinsa. Cika ni'ima-wato ni'ima ta addinin Musulunci wadda babu ni'ima mafi girma da Allah ya ni'imtamu da irinta.

Ubangiji yace:

 

          "Mun saukar da littafi akanka don yin bayanin komai (komai na       akida da shika-shikan ibada, mu'amalolin rayuwa, na abinda      dan Adam zai bukata) don ya zama shiriya da rahama kuma ya   zama bushara ne ga Musulmi."

Musulunci ya kunshi akidu, ibada, ladubban zaman tare, jinkai da mawadaci zai yi ga talaka da mutuntawa, kyakkyawar zuciyar da talaka zai kullace game da wanda yafi shi wadata ko yafi shi matsayi. Ubangiji ta'ala ya fada a cikin wata gamammiyar aya cikin gamammumn ayoyi na Alkur'ani mai girma.

          "A cikin alheri bay a takaituwa akan a juyar da fuskokinku inda mahudar rana take ko mafadarta, (ma'ana, kallon gabas, ga wanda gabas ce alkiblarsu ko kallon yamma ga musulmin dake gabashin dakin Allah tunda alkiblarsu tana yamma) wannan kadai ba shine kadai ayyukan da Allah yayi umarni ba. Ma'ana yin Sallah kadai, ba itace addini ba. Idan kana son dunkulallun ayyuka na alheri, ibada- farko dai "Man aamana billahi wal yaumil akhir wal mala'ikati wal kitabi wannabiyin"- wadannan sune shika-shikan Imani cikin shika-shikan Imani shida, cikon na shidansu Allah ya fade shi a cikin Suratul Qamar:

"Inna kulli shay'in khalaqnahu bi qadar,wama amruna illa wahidatun kalamhin bil basar."

1.       Imani da Allah

2.       Imani da Mala'iku

3.       Imani da Manzanni

4.       Imani da Littattafai

5.       Imani da ranar (lahira) tashin kiyama

6.       imani da Kaddara

 

          A samu mutum yayi Imani da wadannan cikakken Imani gwargwadon yadda ayoyin Alkur'ani suke yi bayani, gwargwadon yadda hadisan manzon tsira, annabi Muhammad (s.a.w) suka yi sharhi. Wannan daya ne daga cikin abinda ake cewa 'Al-birru' koma ace shine shugaba, sauran suna biye dashi.

          Abu na gaba, "Wa'atal mali ala hubbihi" - mutum ya bayar da dukiya alhalin yana sonta. Abinci ne, suttura, dukkan abinda mutum zai bayar ga wani don ya bukace shi, ya zamanto ya bayar dashi a daidai lokacin da yana bukatarsa. Kada ka bayar da lalataccen abu, matattun tufafi, lalataccen abinci, wanda ya lalace ya zama taki, sannan kace zaka bayar a matsayin sadaka. Aikin alheri ka bayar da abinda kake so. Shine 'Wa atal mali ala hubbihi' - wa zai bawa abincin sune-:

 

          "Zawul qurba wal yatama, wal masakin wab-nussabil,                          wassa'ilina wa fir-riqab."

 

          Wadannan sune ake ciyarwa, ciyarwa ta wajibi ko ta mustahabi. Zamu ga ciyarwa wadansunsu ta mustahabi ce, wadansu kuwa ta wajibi ce.

          Ubangiji yace:

'Wa atal mali' - mutum ya ciyar da dukiya.

'ala hubbihi' - alhalin yana so;b ga wa?

'Zawil qurba' - wadanda suke dangi makusanta. Yayye ko kanne, 'ya'yan yayye ko kanne, dangin uwa ko na uba, wadanda suka bukatar abincinka, ko sutturarka ko kudin makarantarka, ko maganinka, ko tallafinka ko hannunka ko wucewa gaba dinka wajen wani abu da ya shafi al'amuran rayuwarsu.

          Wannan yana daga cikin abinda ake kira 'Al-birru'. Yin sallah kadai ba tare da ka hada da wannan ba, birru dinka ko aikin alherinka ya zamanto takaitacce, tawayayye, ragagge. Dole sai ka bayar, ka tallafa ga wadannan 'Zawil qurba'.

Manzon Allah (s.a.w) yace:

          "Idan ka baiwa miskini sadaka, to wannan sadaka ce guda daya. Amma idan ka baiwa dan uwanka sadaka(wa ko kani, ko ire-irensu), sadaka ce kuma sadar da zumunci ne. lada biyu za'a baiwa mutum."

Sannan 'wal yatama'- Mutum ya tallafawa marayu wadanda ska rasa mahaifa tun kafin su kai ga balaga.

Sannan 'Wal masakin' - da talakawa miskikai. Wato miskini ba wai nakasashshe ba, ba kuturu ko gurgu ko makaho ake kira miskini ba. Miskini shine mabukaci. Yakasance gabbansa lafiya ko basu da lafiya. Don ka iya samun kuturu ko gurgu ko makahon da yake da wadata amma ya dauki bara a matsayin sana'a ko addini don haka yake yi. Wannan bai halatta ka bashi sadaka ba mutukar kasan mawadaci ne. amma idan kasan kasashshe ne bashi dashi, yakasance nakasashshe ne, ba nakasashshe bane zaka bashi, wannan shine Al-masakin.

Sannan 'wassa'ilin' - da wadanda tilas tasa sukayi tambaya, tilas tasa suka yi rook, ba wadanda suka mayar da roko sana'a ba, ba 'yan maula da tumasanci ba, a'a wadanda tilas ce, basu mayar da abin sana'a ba-sune 'As-sa'ilin'.

Sai 'wa fir-riqab' - sannan ka ciyar da mutumin da aka rubutawa fansa, yake so ya fanshi kansa. Bawa da yake neman 'yanci - shine 'Wafir-riqab'. Kaga wadannan suna cikin 'Al-birru'.

Farko anyi bayanin shika-shikan Imani, alaka ce tsakaninka da mahaliccinka, kyautatawa da ihsani zuwa ga halittu, yakasance akwai dangantaka ta jinni ko babu, wanda shima duk ya shiga cikin 'Al-birru'.

Sannan sai Ubangiji ta'ala yace:

"Wa aqamas-salata wa-ataz-zakat."

Sai mutum ya tsayar da Sallah ya bada Zakka. Kaga sai aka jinkirtar da sallah a wajen ambato ita da Zakka. Duk da cewa sun dara wani abinda aka ambata kafinsu muhimmanci, amma don idan an ambace su karan fari kila sai su mantar da kai muhimmancin sauran ababan da aka ambata. Shi yasa aka fara lissafa mana su don mu rike su da kyau. Don ita sallah da wahala mutumin day a san wajibanta ya manta da ita.

 

Amma mutum na iya sakaci da danginsa suna cikin halin kaka-ni-kayi. yana iya sakaci da makwabcinsa, talakawa da suke cikin haln kaka-ni-kayi, amma Sallah da wuya kaga yayi sakaci da ita. wani ma har kudi yake biya ya sayi tikiti ya hau jirgi yaje Makka yayi Sallah, amma ga talakawa makwabtansa suna cikin halin kaka-ni-kayi, ga danginsa suna cikin halin wayyo ni 'yasu. Don haka sai Ubangiji ya fara ambaton wadancan, sannan sai aka ambaci Sallah da Zakka.

Sannan sai wani abu da yake ciko ne, mu'amala ta gari, hali na gari. Wato ainihin 'Wal mufuna bi ahdihim iza ahadu' - wadanda suke cika alkawari idan sunyi 'Wassa-birina fil ba'atha'i wadh-dharra'i wahinal ba'ath'-da masu yin hakuri da jajurcewa (idan an fita filin yaki), wato idan suna cikin talauci, ba masu yin raki ko kai karar Allah wurin bayinsa ba.

Enter supporting content here