Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

HUDUBA
4 ga Jumada Awwal 1425
8 ga Juli 2005-07-09
                 DOGARO DA KAI DA KYAUTATA MU'AMALA   

     Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halitta duka, kuma tsira da aminci su tabbata ga manzanmu, Muhammadu (saw). Bayan haka ya 'yan uwa, mu sani cewa Allah ya halitta Aljani da mutum ba domin komai ba face bautarsa, kuma ya hore mana dangin ni'imomi da zamu yi amfani dasu, domin jin dadi a duniya da kuma yin bautarsa. Fadarsa madaukaki:

"Allah wanda ya halicci sammai da kassai, kuma ya saukar da ruwa daga sama, sai ya fitar da tsirrai dashi, arziki a gare ku, kuma ya hore muku jiragen da suke shawagi a cikin teku da umarninsa, kuma ya hore muku koramu, kuma ya hore muku rana da wata, kuma ya hore muku dare da rana kuma ya baku dukkan abinda kuka tambayeshi....."

    Ya 'yan uwa, duk da irin wadannan ni'imomi da Allah yayi mana, yanzu muna fama da manyan matsaloli guda biyu:-

    1. Matsalar zaman kashe wando, rashin aikin yi, rashin sanin manufa tsakanin matasanmu da wasau magidanta, wadda kullum take ta kara yawa a cikin al'umarmu.

    2. Matsalar cuta, algushu, da rashin manufa a cikin mu'amalolinmu, misali, in dauki bangaren kasuwanci kadai muga yadda yake ciki da algushu, na tauye ma'auni, ko cakuda abu mai kyau da mara kyau a cikin kayan abinci, ko yadin sutura, da tauye nagartar kayayyakin, wanda har kayan da ake shigowa dasu, misali daga China zaka ga 'yan kasuwarmu sun tafi har kasar da ake yin kayan su sanya a tauye nagartarsa (quality) suzo su sayar dashi a matsayin mai kyau ta hanyar karyar da farashinsa kadan domin su kasha kasuwar masu sayar da mai nagarta. Haka kuma, gauraya kayan abinci, kamar lalataccen gero da , tauye kilo na buhun shinkafa, hada kasa da masara, ko totonta da hada taki da yashi da sauran nau'uka na algushu.
    Haka kuma a sauran ayyuka kamar aikin gwamnati, kafinta, gyaran motoci da babura, da sauransu. Jama'a a yanzu sun kasu kashi biyu, na daya masu zaman banza da kashghe wando, sai kuma masu abinyi amma suna hadawa da algushu, karya da cin amana, da sauransu, face kadan kawai masu tsoron Allah. Saboda haka, a yau zamu yi nazarin hadisai biyu ne:-
     Hadisan da suke nuna cewa musulmi yakamata ya zama mai sana'a babba ko karama ba tare da ya raina ba, kuma ya guji zaman kashe wando da maula. Hadisi na farko a wannan bangare; An tambayi manzon Allah a cikin arziki, wanne yafi. Sai yace: "Dukkan sana'ar da mutum yayi da hannunsa itace arziki kuma tafi  kusa da zama halal (indai ba'a yi ha'inci a ciki ba)."         (Imam Hakim ne ya rawaito.)
    A hadisin Zubairu Ibn Awwam, manzon Allah yace:
"Dayanku ya dibi igiyoyi ya tafi daji ya yiwo itace ya doro a gadan bayansa, yazo ya sayar domin ya kare kimar fuskarsa, wannan shi yafi alheri gare shi fiye da ya roki mutane, ko sun bashi ko basu bashi ba." (Bukhari ya rawaito shi.)
    An karbo daga Ka'ab Ibn Ujurah yace: "Wata rana manzon Allah na tare da sahabbansa sai wani mutum yazo ya wuce, wanda a jikinsa akwai alamar karsashi da kuruciya, sai sahabbai suka ce; 'ina ma wannan yana fagen jihadi fisabilillah (Musulunci ya fa'idanta da kuzarinsa). Sai annabi yace: "Fitowar nan da yayi daga gida, idan dai har ya fito ne domin neman abinda zai ciyar da kananan yara, to daidai yake da fisabilillah. Haka kuma, idan ya fito ne domin ya nemo abinda zai ciyar da iyayensa guda biyu tsofaffi da suka gajiya, to daidai yake da yaki fisabiliilah. Haka kuma idan ya fito ne domin zai kare mutuncinsa daga rokon mutane, to daidai yake da yaki fisabilillah."  (Dabarani ya rawaito)
    Saboda haka, dole ne mu dage wajen sana'a babba ko karama, tare da dagewa wajen inganta ta, da bata muhimmanci, ba kamar yadda muke rikon sakainar kashi ba. Mu rika bude wurin kasuwanci da wuri, da kuma kiyayewa.
    Manzon Allah yace: "Allah ka sanya albarka ga al'umata a cikin jijjifinsu." Sakhab Ibn Wada'a da yaji wannan hadisi sai yayi aiki dashi ta hanyar fita ko tura fataucinsa da jijjifi (sassafe / sammako), sai Allah yayiwa dukiyarsa albarka."  (Abi Dawud ne ya rawaito.)
    Ya 'yan uwa sai bangare na biyu, sune hadisai da suka hana karya da algushu a cikin kasuwanci:-
(a)   Bukhari ya rawaito hadisi daga Abi Hurairah (r.a) yace: "Manzon  (s.a.w) Allah  yace "wani zamani zai zo, jama'a basa kulawa da me yazo hannunsu (na haram ko halal)." Wannan kuwa shine yanayin da muke ciki yanzu.
(b)   An karbo daga Jabir Ibn Abdillah yace: "Manzon Allah yace da Ka'ab Ibn Ujurah; "Babu yadda za'ayi mutum ya shiga Aljanna matukar naman jikinsa ya tsiro daga haram ne." Ibn Hibban ya rawaito shi, a ruwayar Muslim ya kara da cewa "Wuta itace tafi cancanta dashi."
(c)   Manzon Allah yace: "Dukkan wanda yayi mana algushu, baya tare damu (cikinmu) musulmi."
    Saboda wadannan hadisai da suka gabata dole mu kiyaye.   
Allah ya taimaki musulunci da musulmi, kuma ya karya kafirci da kafirai.

 

Enter content here

Enter supporting content here