Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Halin da Duniyar Musulunci Take Ciki

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

Hudubar Juma'a Ta  3

DA SUNAN ALLAH MAI GAMAMMIYAR RAHAMA MAI JIN KAI.

MAUDU’I- Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki A Yau

MALAMI- Sheikh Ja’far M. Adam

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa, kuma muna neman tsarin Allah daga mafi sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar, shi ne shiryayye, wanda kuma ya batar to babu wani mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa bisa ga cancanta sai Allah, shi daya yake ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne.

{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلاَ تَمُوتُنَّ إِلاَّ وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ} (آل عمران : 102)

{يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالاً كَثِيرًا وَنِسَاءً وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ وَاْلأَرْحَامَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَيْكُمْ رَقِيبًا} (النساء : 1)

{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلاً سَدِيدًا * يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا} (الأحزاب: 70-71)

Bayan haka, ya ‘yan uwa al’ummar musulmi a rayuwata ta yau shiga cikin wani hali mawuyaci daga cikin mawuyacin halin da ba ta taba shiga a dogon tarhinta ba. Masifu suna ta kewayeta, matsaloli sun kanannadeta, yake-yake sun kewayeta. Alal misali, Afghanistan ta shiga kulli na uku, tana cikin matsaloli da yake-yake, sama da shekara ashirin (20) tun shekarar 1978 zuwa yanzu.

Farkon matsala, mamanar da Rasha ta yi mata, wadda ta dauki kimanin shekaru tara a jere. Na biyu fada da juna, da kashe-kashe a tsakanin kungiyoyi wadanda a da suka hada karfi domin su kori Rasha ta fita daga Afghanistan. Fitar Rasha ke da wuya, suka ci gaba da yake-yake da juna a kan shugabanci da mulki. Faifai na hudu shi ne zuwan Taliban wadanda suka yaki dukkan wadannan kungiyoyi domin su kawar da kasar daga halin da take ciki na rushewa, da wargajewa da daidaicewa. Allah (M) ya basu nasarar daidaita al’amurra bisa ga tsari mai kyau, idon har aka kwatanta da tsarin da ya wuce a baya, suka sami nasarar mamaye fiye da kashi saba’in na fadin kasar Afghanistan, suka tabbatar da bin tsarin dokokin Allah a wannan kasa. Bayan wannan faifai na biyar shi ne dawowar Amerika da sojojin kawance domin kawar da gwamnatin Taliban da kokarin karya lagon kungiyar Al Qa’ida, kamar yadda kafofin yada labarai suka rika watsawa a waccan lokaci. Ko shakka babu sun sami nasarar kwace mulki daga Taliban, amma ba su ci nasarar korarsu daga Afganistan ba. Haka kuma sun ci nasarar kwace mulki na adalci wanda ya dan farfardo da zaman lafiya da rayuwa ta dan jin dadi ko yaya yake, wadda Taliban suka wanzar a Afganistan. Amma ba su ci nasarar tsarkake Afganistan ba daga ‘yan Taliban, ko Tanzimul Qa’ida, har ya zuwa halin da muke a cikin yanzu; domin har yau Afganistan ta yanzu tana cikin matsaloli, wadda kasace daga cikin kas ashen musulmi.

Sai matsalar Kashmir wadda ta wuce shekara hamsin (50) taki-ci taki cinyewa. A yayin da majalisar dinkin duniya ta yi kudurce-kudurce sama da shekara goma sha biyar (15); wanda take nuna lalle a baiwa ‘yan Kashmir abin da ake cewa "Hakkul takrirul masir" watau zabar abin da suke ganin ya fiye masu. Ko dai su ci gaba da zama cikin Indiya, ko kuwa su balle su hadu da Pakistan, ko kuma su hada kasa ta su, ta kansu, mai cin gashin kanta. Amma dukkan wadannan kudurce-kudurce sun zama tamfar rubutu a ruwa. Babu abin da aka zartar, suna cikin matsaloli, suna fuskantar barazanar rayuwa, daga gwamnatin Indiya, ana kashe su, da kona masu gidajensu.

Sannan sai matsalolin Piliphines, yau sama da shekaru arba’in (40) tun kafin shugaba Marcus har ya zuwa yau matsalar taki ci taki cinyewa. Ga matasalar wani wuri da ake cewa "Turkistan Ash Sharkiyya" wani yanki ne a yammacin kasar China, wanda yake iyaka da Turkistan ta yau, ko kuma wani bangare na Afganistan a yau; wanda yanki ne mai rinjayen musulmi, amma suke fama da matsaloli tun lokacin da aka kafa mulkin gurguzu a China har ya zuwa yau babu wani wanda ya kallesu da idon rahama, ko da majalisar dinkin duniya, ko Amurka, ko kasashen da suke iya hawa kujerar na]i domin a taimaka musu a warware masu matsalolinsu.

Ga matsalar Iraqi a yau, wadda da yawa daga cikin mutane masu fashin bakin abubuwa da suke zuwa su dawo (cikin musulmi ko kafirai) tsamaninsu da zarar ana karya Saddam Hussain, ko aka kore shi, aka shiga Bagdad shi ke nan matsalar IraqI ta kare. Alhali ba su sani ba daga wannan ranar ne ake dora dan ba na bude sababbin matsalolin Iraqi, wadanda Amurka a yau da kanta take ba da shaida game da su.

Dukkan wadannan yankuna ne na musulmi, wadanda suka shafe mu, shafa ta addini, wanda ya kamata mu rinka ji a jikinmu, saboda ayoyi na Alkur’ani Mai Girma da suka zartar na dangataka da ‘yan uwantaka a tsakaninmu da su, duk da bambancin yare, fadin kasa, ko launin fata bisa ga ka’idar " Lalle muminai ‘yan uwan juna ne".

{ إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ} (الحجرات: 10)

Sai matsalolinmu na gida Nijeriya, yau a ji rigima a can gobe a yi a can, a yankin Pankshin ko Langtan da sauransu. Ana kona gidaje da karkashe musulmi, amma babu abinda Jami’an tsaro suke yi wajen kwantar da wannan matsala. Dukkan wadannan matsaloli ne da suka ki ci suka ki cinyewa ga al’ummar musulmi. Abinda ya kamata mai tambaya ya yi tambayar a kansu shi ne: - Me ya kawo wadannan matsaloli? Kuma wadanne hanyoyi za a bi domin warware su? Wannan shi ne abin da dukkan wani mai hankali ya kamata ya tambayi kansa, ko wanda yake a gefensa, wanda ya fi shi fahimtar addini ko abubuwan da kanje su komo na rayuwa, domin su yi masa bayanin dalilan wadannan matsaloli, ko kuma akalla hanyoyin da za a bi domin warware su. Amma kun ga wadannan dalilan suna da yawa.

Ya al’ummar musulmi, daga cikin dalilan da suke kawo matsala a yanzu, da wadanda za su ci gaba da kawo matsaloli a fahimce su, kuma mu nisance su, sun hada da : -

1- SABANI: Sabanin da yake kasa al’umma gida- gida, wanda yake sanya al’umma ta shagalta da kanta, a maimakon ta shagaltu da abokin gabarta. Ta yadda ‘ya’yan al’umma daya, masu addini daya suke kullawa junansu zagon kasa, irin wanda basu kullawa Kirista, kafirai ko Bamaguje. Bayan kuwa Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: "

Kar ku yi jayayya sai ku karye, karfinku ya zamo babu shi".

{وَلاَ تَنَازَعُوا فَتَفْشَلُوا وَتَذْهَبَ رِيحُكُمْ} ( الأنفال:46)

2- TSANANIN SON DUNIYA: - tsananin son duniya da fifita ta akan lahira. Irin son duniyar da ke sanya daya ko wasu daga cikinmu su kasance suna jin a shirye suke su yi kawance da kafiri domin a cutar da dan uwansu musulmi. Wannan shi ne halin da yawa daga cikin kasashen musulmi suke ciki. Sun bayar da gudunmawa mai yawan gaske ga Amurka lokacin yaki da Afganistan. Har ila yau kuma, suna ba da irin wannan gudummawar ga Amurka a yakin da take yanzu da Iraqi. Wannan ita ce babbar matsalar, watau fifita duniya a kan lahira, da fifita mulkinsu a kan lahira, da fifita bukatunsu na duniya a kan Aljannah. Wannan shi ne abin da ake samu tsakanin hukumomin da suke da’awar musulunci, ko daidaikun mutane daga cikin manya-manyan mutane, da ‘yan kasuwa da ministoci da gwamnoni, kwamishinoni, da ‘yan boko, da talakawa na kasa. Har ya kai halin da musulmi zai daurewa kafiri gindi domin ya ci mutuncin musulmi, ko kuma ya ci mutuncin wani bangare na ‘yanuwansa musulmi. Wannan yana daga cikin abin da ke karawa kafirai kwarin gwiwa su ga lagonmu, su kuma rinka kokarin cutar da mu a ko da yaushe. Manzon Allah (s.a.w) ya bada labari a hadisinsa ingantacce yana cewa : " Saura kiris al’umomi su yi taro a kanku, kamar yadda majiya yunwa suke taruwa a kan akushin abinci" sai Sahabbai suka ce : Ya Manzon Allah (s.a.w) me yasa za a taru a kanmu, shin don mun zama ‘yan kadan ne? Sai ya ce : " A’a kuna da yawa a wannan lokacin, sai dai da yawanku tamfar yawan yayi ko karmami ne a yayin da gulbi ya kawo ( ba yadda za a yi ya tare gulbin) sai ya ce : " Allah zai cire kwarjininku da tsoronku daga zuciyar kafirai" a da kamar shekaru ashirin (20) da suka wuce, kafirai suna tsoronmu da kwarjininmu, hatta carbinka yana tsoro, ballantana rawani ko babbar rigarka. Amma a yanzu sai kayi kiliya da arne ko dai ka kauce ko kuma ya banke ka ya wuce. Domin ganin da ya yake maka a wulakance, babu kima babu daraja. Wannan ya gaskatar da fadin Manzon Allah (s.a.w) cewa :- " Allah zai cire kwarjininku daga cikin zuciyar kafirai, ya jefa maku rauni". Sai Sahabbai suka ce mene ne rauni da zai kanannade zukata. Sai ya ce : " tsananin son duniya da jin tsoron mutuwa". Wannan shi yake gadar mana a raina mu cikin al’umma, ta yadda musulmi sun zama al’umma mafi arha a kasuwar ciniki ta yadda kowance talaka sai ya taya mu.

3- RAUNIN IMANI DA LALACEWAR AKIDA: - Lalle tunani na gari da akida ingantacciya sune injin da yake motsa musulmi ya kai ya komo ba tare d jin tsoron kowa ba sai Ubangiji. Imani na gari shi ne idan ya tabbata a zuci tasirinsa yake bayyana a gabbai da maganganu da ayyuka na dan Adam. Wannan ya sanya Allah (M) ya ke fada:

 

{وَلاَ تَهِنُوا وَلاَ تَحْزَنُوا وَأَنْتُمُ اْلأَعْلَوْنَ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ} (آل عمران :139)

" Ka da ku wulakanta, kada ku razana, ku ne madaukaka idan kun zama muminai".

Ka’idar a nan ita ce sai idan mun zama muminai na gaskiya. Kihsiyar wannan shi ne idan ba mu zama muminai ba ba zamu taba zama madaukaka ba. Amma yanzu babu ingantacciyar Akida, sai shirka da bidi’o’i, da bautar kabari da sauransu duka sun yi katutu a zuciya da ayyuka na wasu musulmi. Wasu rashin (ثقة ) da Allah madaukaki, rashin amintuwa da abin da ke daga wurin Allah madaukaki, sai dogaro da dabarunmu, da sanin ya kamata namu fiye da amintuwa da dabarar Ubangijinmu da kariyarSa da agajinSa.

4- RAUNIN ‘YAN UWANTAKA DA IMANI:- a yanzu musulmi sun zama babu ‘yanuwantaka ta imani sai ta wani abu daban. Kamar ‘yan uwantaka ta kabilanci, ‘yan gari, ko launin fata, jam’iyyar siyasa, ko kungiyar addini. Muna ganin wanda duk ba mu hade wadannan ba, a matsayin ba dan uwanmu ba, duk da kasancewarshi dan uwanmu musulmi, wanda ya amince da kalmar shahada, yake aiki da Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (s.a.w) lalle wannan yana kawowa musulmi matsalolin da muka lissafa a baya.

5- RASHIN RIKO DA SABUBBA NA NASARA: Lalle Ubangiji ya tsara rayuwa ta yadda sai ka yi wani abu ne zaka sami wani abu. Misali: Duk wanda aka yi ruwan sama aka sanyawa gona taki, ko takin da albarka, in dai har bai dauki sungumi ya je gonar ya sara, ya yi shuka, ya yi noma, ya yi maimai, da sauran ayyukan gona ba, babu yadda za a yi ya samu amfanin gona. Al’ummar musulmi a yanzu ta yi riko da sababi daya ne kawai daga cikin sabubban cin nasararta. Wannan sababi kuwa shi ne addu’a. Kowa ka gani shi dai addu’a kawai yake yi. Alhali ita addu’ar nan daya ce daga cikin sabubba fiye da dubbai da Allah ya gitta cewar sai mun bisu ne zamu ci nasara. Lalle mun iya addu’ar Allah ya rusa Amurka da Rasha da sauransu a ce amin da karfi. To a yanzu idan har Allah (s.a.w) ya karya wadannan gaba daya, kuma mu musulmi muna cikin wannan hali a yanzu, ba tare da canji a cikin akidarmu da imani da ayyukanmu ba lalle ba yadda za a yi mu karfi shugabanci. Shin yanzu da Amurka za ta rushe muna jin cewa musulmi suna cikin matakin da za su iya daukar shugabancin duniya ne (watau maye gurbin Amurka)? Wato abin nufi ta fuskar matakin imani, da akida, amana, ilmi, sanin ya kamata da sauransu. Tabbas mun sani cewa akwai wani dan motsi da yunkuri daga wasu samarin musulmi da mata, saida har yanzu bai kai ta yadda zai cike ka’idar Allah ba da ya yi alkawari cewa :

{إِنَّ اْلأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ...} (الأعراف:128)

"Lalle kasa ta Allah ce yana gadar da ita ga bayi (muminai)". Saboda haka lalle akwai bukatar mu yiwa kanmu juyin juya hali a cikin akidarmu, ayyukanmu, da mu’amalolinmu na rayuwa. Mu dora su bisa sikelin fadar Allah (M) da fadar Manzon Allah (s.a.w).

6- HAUHAWAR JAHILCI NA ADDININ DA NA RAYUWA:- Lallai hauhawar jahilci na addini yana kawowa musulmi matsala, haka kuma jahilcin rayuwa; rashin masana a bangaren mulki, likitoci, tattalin arziki, injiniyoyi da sauransu yana kawowa al’ummar musulmi matsala ta dogaro da wata al’umma (wadda ba musulma ba) domin samun wadannan abubuwa, wadanda a yanzu rayuwa ba ta inganta sai da su. Wadannan kadan ne daga cikin matsaloli.

Sannan akwai wani abinda ba za a manta da shi ba. Wannan abin kuwa shi ne fa[ar Allah cewa zai jarrabi muminai. Ko da mun cika wadannan sharudda, mu sani cewar akwai jarrabawar lokaci zuwa lokaci. Domin fadarsa madaukaki Sarki Allah:

{ألم *أَحَسِبَ النَّاسُ أَنْ يُتْرَكُوا أَنْ يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لاَ يُفْتَنُونَ}

"Alif. Lam. Mim. Shin mutane suna tsammani za a kyalesu ne domin sun ce mun yi imani, ba za a jarrabe su ba…". (Ankabut 1-2).

Da fadarsa: -

{كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ وَنَبْلُوكُمْ بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَةً} (الأنبياء: 35)

"Kowace rai za ta dandani mutuwa, kuma za mu jarrabeku da sharri da alkhairi…".

Da fadarsa :

{وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّى نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنْكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ أَخْبَارَكُمْ} (محمد: 31)

" Kuma za mu jarrabe ku har sai mun sani (su wane ne) mujahidai daga cikinku, kuma za mu binciki labarinku".

Da fa[ar Manzo (s.a.w) : "Mafi tsananin jarraba (Ibtila’i) ta kan kasance ne kan Annabawa, sai kuma wadanda suka fi kusa da tafarkinsu".

"أشد الناس بلاء الأنبياء ثم الأمثل .... "

Abubuwan duk da mu ka yi bayani a baya lalle sune suka kawowa musulmi matsaloli. A yanzu abin da muke nema shi ne mafita. Hanyoyin fita kashi biyu ne, akwai :

1) hanyar fita a jumlace da kuma

2) hanyar fita a filla -filla

1) Hanyar fita a jumalace ita ce komawa zuwa ga Allah. Wannan ita ce hakikanin mafita. Domin fadarsa Madaukaki :

{فَفِرُّوا إِلَى اللَّهِ} الزاريات : 50

" Ku fita (a sukwane) zuwa ga Allah…".

Da fadarsa :

{وَأَنِيبُوا إِلَى رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ} الزمر : 54

" ku koma zuwa ga Ubangijinku, ku mi]a wuya gare shi tun kafin azaba ta zo muku sannan ba za a taimakeku ba".

Komawa zuwa ga Allah ta hanyar gyara akida da imani, domin farkon abin da ya wajaba ga baligi shi ne inganta imaninsa. Sannan karkade zuciya daga dukkan wani datti na gurbatacciyar a]ida wadda ta yi taho mu gama da ayar Alkur’ani da ingantattu hadisan Manzon Allah (s.a.w). Tare da kyautata ayyuka ta yadda ibadarmu ta zama ibada ce tsantsa bisa sunnar Manzo (s.a.w) , ba tare da wani sirki na bidi’a ba. Mu gina akida ta son Allah da ManzonSa (s.a.w) da gyara dabi’ummu da halayenmu da cikakkiyar soyayya ta Annabi (s.a.w) fiye da son kowa a duniya, sannan son ‘yan uwanmu musulmi da karfafa dangantaka ta imani a tsakaninmu da su a ko’ina suke kuma komai bambancin kasarmu da su, ko yarensu, ko launin fatarmu, da sauransu. Sannan kin kafirai da kowane nau’i na kafirci (ko Yahudawa, Kirista ko Majusawa da sauransu) da yi musu bara’a ta hanyar yin fito na fito da su da kyamatarsu. Bayan wannan sai zage dantse wajen riko da sabubba na cin nasara.

A cikin sabubban cin nasara akwai sababi na ruhi da kuma sababi na rayuwa duniya. Ya kamata kowane daga cikinmu mazanmu da matanmu ya rinka jin cewa akwai nauyi a kansa a matsayinsa na mai gida, ko yaron gida, shugaba; sarki ko gwamna. Kuma mu sani cewa lalle zamu tsaya a gaban Allah muna abin tambaya game da wadannan nauye-nauye da aka dora mana. Kuma mu rika yarda da kason da Allah ya bamu a duniya komai kankantarsa. Ya kasance a koda yaushe muna kallon kasanmu ne (wanda muka fi) ba wanda suka fimu ba, ta kowace fuska na daga ni’imomi na rayuwar duniya, dalili kuwa shi ne duba zuwa ga wanda suka fimu zai sanya mu kasance masu ganin karancin ni’imar da Allah (M) ya yi mana, wanda hakan yake haifar da rashin godiya a gareshi. Amma duba zuwa ga wanda muka fi ta kowanne fanni zai sanya mu fahimci irin girman ni’imar da Allah ya yi mana, kuma mu gode masa. Mu daina hadama, da babakere, da son zuciya, mu yi kokarin ha[a kan musulmi bisa kur’ani da Hadisi ba bisa son zuciya ba. Mu kasance muna goyon baya ga wanda akidarsa ta sami goyon bayan Alkur’ani da Hadisi, sannan mu bijirewa duk wanda akidarsa da ayyukansa da maganganunsa suka sa\awa Alkur’ani da Hadisi. Mu rika yin nisa da bin abubuwa da aka gada kaka da kakanni wanda suka sa\awa shari’a. Hakika wannan ita ce hanyar komawa zuwa ga Allah a jumlace.

Amma hanyar komawa zuwa ga Allah filla-filla, lallai tsayuwa a mimbari ba za ta wadatar ba. Saboda haka ya kamata ‘yan uwa mu sani cewa Allah ya yi mana alkawari kamar haka :

{وَلَيَنْصُرَنَّ اللَّهُ مَنْ يَنْصُرُهُ إِنَّ اللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ} (الحج : 40)

" Da sannu Allah zai taimaki wanda duk ya taimaiki addininsSa".

" Idan kuka taimaki addinin Allah zai taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku".

{وَكَانَ حَقًّا عَلَيْنَا نَصْرُ الْمُؤْمِنِينَ} (الروم : 47)

{وَكَانَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنْجِي الْمُؤْمِنِينَ} (يونس : 103)

{وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِينَ * إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنْصُورُونَ * وَإِنَّ جُنْدَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَ} (الصافات : 171-173)

{وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُو ا مِنْكُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي اْلأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضَى لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُمْ مِنْ بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا يَعْبُدُونَنِي لاَ يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا وَمَنْ كَفَرَ بَعْدَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ} (النور : 55)

Sai dai mu sani kafin wannan abin da Allah yake bukata a garemu shi ne mu kasance kamar yadda ya fada:

{يَعْبُدُونَنِي لاَ يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا وَمَنْ كَفَرَ بَعْدَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ} (النور : 55)

"Suna bautawa Allah ba sa hada shi da wani abu a wurin bauta wanda kuwa ya kafirce bayan wannan to, wadannan sune asararru.

Ya Allah kar ka kama mu da abin da wawaye daga cikinmu suka aikata, Allah ka gafarta mana, kuma ka taimaki musulunci da musulmi.

Wassalamu alaikum

 

Enter supporting content here