Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Hukuncin Hijira

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

HUDUBAR JUMA'A TA 2

  
    

DA SUNAN ALLAH MAI GAMAMMIYAR RAHAMA MAI JIN KAI.

MAUDU’I- Hukuncin Hijira

K/ WATA - 12/10/1424 H 5/12/03 M

MALAMI- Sheikh Ja’far M. Adam

Ya ‘yan uwa, yau zamu tattauna ne game da wata mas’ala ta addini mai matukar muhimmanci, wadda malamai sun tattauna a kanta, a cikin manya da kananan littattafansu. Wadansu ma sun kebance ta ta hanyar yin talifi a kanta ita kadai, ba tare da sun gwama ta da wata mas’alar ba. Malaman tafsiri da malaman fikhu da malaman hadisi da malaman akida duk suna da ta cewa a kanta, domin mas’ala ce da take shiga babuka masu dimbin yawa a cikin fikhu da tafsiri da tauhidi. Mas’ala ce wadda ake kallon ta ta mahanga daban-daban, a bangare daban-baban, sasanni daban-daban. Matsayinta kamar matsayin sauran mas’aloli ne na addini masu zurfi, wadanda ba su halatta wani ya tattauna a kansu ba tare da ilmi ba, ko ya ce zai fatawa a cikinsu ba tare da ilmi ba, sai da son zuciya. Ba zai halatta wani ya yi gaggawar zartar da hukunci a kansu, ko ya yi bayanin irin wannan mas’ala, ba tare da ya koma ya tattaro ayoyin da suka yi bayaninta ba, a cikin Alkur’ani ko ingantattun hadisai a cikin mashahuran littatafan hadisai na Manzon Allah (s.a.w) da suka tattauna wannan mas’ala, yana mai dofanar hasken maganganu na malamai magabata, cikin sahabbai da tabi’ai da tabi’ut tabi’ina, da malamai wadanda suke tabbatattu a cikin ilmi, ba wadanda sukai kutse a gonar ilmi ba, malamai wadanda suke da masaniya game da Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (s.a.w) da tarihin Annabi da sahabbansa, rayuwan Annabi da musulmi a Makka kafin hijira, rayuwar Annabi da musulmi a bayan hijira. Mas’ala ce wadda a yau, kowane kare da kowane doki yake tattaunawa a kanta, ‘yan kadan ne cikin mutane masu iya bayyana bangarorin gaskiya a cikin mas’alar, amma da yawansu, suna hayaniya ne, suna tattaunawa a kan mas’alar ba tare da ilmi ba, sai harigido, wanda ba su da alaka da ilmi, alaka ta kusa ko ta nesa. Wannan mas’ala ita ce mas’alar HIJRAH.

Hijrah babban mas’ala ce, kuma ita hijira reshe ne na akida ta Al الولاء والبراء , (Al wala wal bara’) kaunar Allah da Manzon Allah (s.a.w) da muminai, kin kafirai da kafircin da suke kai. Wannan akida ta الولاء والبراء , yin hijrah reshe ne nata, mutum zai fahimta ne idan ya fahimci asalinta. Mas’ala ce mai girman gaske, saboda hijrah ne al’ummar musulmi a karon fari, suka kauracewa garinsu, biranensu, suka dauki kewar zama a garin bakunci, da nesa da iyalensu, nesa da asalinsu, suka kauracewa dangin ababan da suka saba na ci, ko na sha, ko na sutura, kona matsuguni, suka canza abokanen da ba nasu na da ba, ‘yan uwan da ba nasu na da ba, makobtan da ba nasu na da ba, suka sami kansu cikin kewa ko bakunci da kewa ta rashin sanin mene ne zai faru a yammacinsu ko a washe garinsu, gobe ko jibinsu .

Ubangiji (M) yayi alkawarin tarin lada ga masu hijrar farko tun lokacin Manzo (s.a.w) Allah ya ce:

(WADANDA SUKA YI HIJRAH DON ALLAH BAYAN AN ZALUNCE SU (an hana su yin adddininsu, ko bayyana addininsu) ZAMU TSUGUNAR DA SI (zamu zaunar da su, masaukar da su) ANAN GIDAN DUNIYA A KYAKKYAWAN MATSAYI A KYAKKYAWAR MASAUKI, AMMA LADAN DA AKA YI MUSU TATTALI A LAHIRA ( ko gobe Kiyama) SHI NE MA FI GIRMA INDA A CE MUTANE SUNA DA SANI".

(Suratul Nahli: aya ta 41).

Ubangiji Ta’ala ya yi alkawarin rahama da gafara ga masu HIJRAH din, ya ce : " LALLAI WADANDA SUKA YI IMANI SUKA YI HIJRAH SUKA YI JIHADI DON YADA KALMAR ALLAH A BAN KASA, IRIN WADANNAN SU NE MASU NEMAN YARDAR ALLAH, KUMA UBANGIJI MAI GAFARA NE KUMA UBANGIJI MAI JIN KAI NE".

(Suratul Bakarah : aya ta 218).

A saboda matsayin Hijrah ne ma Ubangiji Ta’ala ya yanke alaka ta taimakekeniya da juna tsakanin muminai da suka yi Hijrah da wadanda suka zauna suka ki yin Hijrah. Allah ya ce;

" BABU TAIMAKEKENIYA DA JUNA A TSAKANINKU".

Allah ya ce :

"LALLAI WADANDA SUKA YI IMANI SUKAI HIJRAH SUKA YI JIHADI DA DUKIYARSU DA KAWUNANSU DON YADA KALMAR ALLAH, DA WADANDA SUKA KARBI BAKIN DA SUKA ZO HIJRAH DIN SUKA BAYAR DA MASAUKI GA MASU HIJRAH DIN, SUKA TATTARO SU A

GARINSU SUKA TAIMAKE SU, IRIN WADANNAN SASHENSU DANGI NE GA SASHE".

Ta fuskar matsayi a duniya, da matsayi a lahira, da matsayi a gidan aljannah. Sai kuma Allah ya ce :

"AMMA WADANDA SUKA YI IMANI SAI BA SU YI HIJRAH BA, SUKA GWAMMACE ZAMA A CIKIN KAFIRAI, (a garin da ba sa iya bayyana addininsu, ba su iya bayyan adawa da duk wata akida da ta yi taho mu gama da akidar musulunci, irin wadannan mutane) BABU KU BA TAIMAKONSU (ko wane irin nau’i na taimako) HAR SAI SUN YARDA SUN YI HIJRAH (matukar sun zauna duk imaninsu, duk akidarsu, duk kyawu da tsarkin zuciyarsu, tun da ba su yi hijra ba, ba ku ba taimakonsu har sai sun yi hijrah) IN SUN NEMI TAIMAKONKU DA AGAJINKU TA BANGAREN ADDINI KADAI (Ba ta bangaren rayuwa ba) SA’ILIN NAN YA ZAMA WAJIBI KU TAIMAKA MUSU, SAI FA IN SUNA FADA NE DA WADANSU MUTANE DA SUKE KAFIRAI NE, AMMA KU KUNA DA ALKAWARIN ZAMAN LAFIYA TSAKANINKU DA SU" ( Suratul Anfal : aya ta 72).

To idan za su yi fada da wadancan da suka ki yin hijrah, ba za ku taimakawa wadancan muminai a kan kafiran da ku ka yi sulhu tsakaninku da su ba. Sai ku kyale su tasu ta fishshe su, tun da ba su yi hijrah ba, in da sun yi hijrah da hukuncinku da su duk daya ne. ka ga duk wadannan na nuna illa ta rashin yin hijrah idan mutum ya yi imani, kuma yana da ikon ya yi hijrah din, laifi ne amma bai kai girman kafirci ba.

Ubangiji Madaukakin Sarki ya yabi Muhajirai ya yabi Ansar a cikin Al kur’ani irin wadannan su ne muminai na gari in ji Allah, masu imani da hijrah da suka yi jihadi, da al Ansar wadanda suka ba da masauki ga masu hijrah, su ne muminai na gari suna da gafara kuma suna da lada mai girma (lada mai gwabi) a wajen Allah.

Ya ‘yan uwa ! asalin kalmar HIJRAH, idan an ce Hijrah a larabci a bin da take nufi kaucewa, barin wani wuri, da zakudawa gaba kadan, tashi daga nan ka koma can, daga can ko koma can. A cikin harshen shari’ar musulunci idan an ce hijrah tana daukar ma’anar tashi daga garin kafirci da shirka zuwa garin imani da musulunci. Sannan ita hijrah ma’anarta bata tadaita ba a kan wannan kadai, tana da matukar fadi kwarai da gaske. Al Imam Ibnil Qayyim ya ce: ita asalin hijrah iri biyu ce: -

1. Mutum ya yi hijrah da gangar jikinsa, ya daura kacokan da gangar jikinsa, daga wannan garin zuwa wancan garin, daga wannan wuri zuwa wancan wurin; wannan ita ce hijrah ta farko.

2. wadda ita ce asalin hijrah, wadda muka ambata dazu, bi mata take yi, wato ainihin ita ce hijrah zuwa ga Allah, hijrah zuwa ga Manzon Allah (s.a.w). Manzon Allah yace:

WANDA HIJRARSA TA KASANCE ZUWA GA ALLAH DA MANZONSA, TO LADAN HIJRARSA NA GA ALLAH DA MANZONSA, WANDA KUWA HIJRARSA TA KASANCE DON DUNIYA DA YA SAME TA, KO WATA MACE DA YA AURETA, TO LADAN HIJRARSA NA GA ABIN DA YA YI HIJRAR D0MINSA". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ibnil Qayyim ya ce: ita hijrah zuwa Allah da Manzon Allah, ta kunshi hijrah ne daga wuri kaza zuwa ga wuri kaza, mutum ya daura da zuciyarsa ba da gangar jikinsa ba kadai, ya kaura daga me? Daga kaunar wunin Allah zuwa ga kaunar Allah da Manzon Allah, daga bautar wanin Allah, zuwa ga bautar Allah shi kadai, daga jin tsoron wanin Allah zuwa ga fatan samu a wurin Allah shi kadai, daga dogaro a kan wanin Allah zuwa dogaro da Allah shi kadai, daga kiran wani, ko rokon wanin Allah zuwa ga rokon Allah shi kadai, daga kaskantar da kai da takwarkwashewa a gaban wanin Allah zuwa ga kaskantar da kai da takwarkwashewa da nuna bautuwa a wurin Allah shi kadai. Ibnul Qayyim yace: Wannan ma’anar da na bayyana maka, shi ne hakikanin abin da ake nufi da gudu a sukwane zuwa ga Allah, da Allah yace:

" KU TSERE A GUJE (KU FITA A SUKWANE) ZUWA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI".

Daga sa masa kishiya zuwa kadaita Shi, daga bautar waninsa zuwa ga bautata maSa, daga sa\a maSa zuwa ga yi maSa da’a, daga bin dokokin waninSa zuwa ga bin dokokinSa, daga jin kunyar waninSa zuwa ga jin kunyarSa, daga tsoron waninSa zuwa ga tsoronSa, kauracewa zuwa ga Allah kocokan dinka da zuciyarka, idan zuciya ta sami wannan, ta koshi da wannan, sai gabbai su amsa mata. Yayin da zuciya ta talauta daga wannan, ko ya kasance akwai kanfar wannan, da yunwa da kishirwar wannan, babu yadda za a yi gabbai su iya amsa mata. Wannan ita ce hakikanin hijrah wadda ake bukata bawa ya yi ta a karon fari har kafin hijrah ta zo a karo na biyu. Ibnul Qayyim ya yi dogon bayani, wanda nan ba wurinsa ba ne ba. Ko shakka babu, yana daga cikin hijrah tashi daga garin da ake tsoron zuwa garin aminci. Sahabbai sun bar Makka zuwa Habasha, ba wai don Makkah kafirai ne Habasha muminai ba, sai don Makkan akwai tsoro da firgici a cikinta, Habasha kuwa akwai walwala da kwanciyar hankali da wani ‘yanci na bautar Allah a cikinta, makamancin wanda babu shi a Makka. Amma in ba haka ba a wannan lokacin, yadda Makka ta ke kafirai Habasha kuma suma kafirai ne, illa iyaka nau’in kafircin da ke Habasha jinginawa Allah da da da’awar alloli guda biyu ne, ko uku ne, ko sama da haka ko kasa da haka. Addinin kiristoci, murgudadden addini, karkatacce makamncin yadda na Makka yake karkatacce. Amma tare da haka Manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni ga muminai su tashi daga Makka su je Habasha din, har sau biyu.

Wannan wani nau’i ne daga cikin nau’ikan hijrah, yana daga cikin nau’in hijrah tashi daga garin da bidi’a ta yi kaka gida zuwa garin da sunnah ta yadu ta yi kaka gida a cikinsa.

Al Imam Malik bin Anas yake cewa : "Ba shi halatta ga musulmi ya zauna a garin da ake zagin Sahabban Manzon Allah a cikinsa". Ma’ana dukkan garin da ya kasance abin da ya shahara a garin kashi saba’in zuwa sama da haka cikin dari na garin shi ne la’antar Sahabban Manzon Allah, ya zama wajibi mutum ya yi kaura ya je garin da ba hakan garin yake ba. Duk garin da bidi’a ta yi kaka gida, sai a kaurace a je garin Sunnah. Sannan yana daga cikin nau’ika na hijrah tashi daga garin da haram ya yi rinjaye a cikin zuwa garin da halal ne ke da rinjaye a ciki. Sannan yana daga cikin nau’ikan na hijrah, gujewa daga garin da kake ganin za a cuceka a gangar jikinka zuwa garin da ba za a cuce ka a garin ba. Annabi Ibrahim ya yi hijrah da mutanensa suka yi kokarin kashe shi. Ya ce:

" NI INA MAI YIN HIJRAH ZUWA GA UBANGIJINA". Yace:

" NI NA TAFI ZUWA GA UBANGIJINA DA SANNU ZAI SHIRYAR DA NI". Annabi Musa ya yi hijrah lokacin da aka yi kokarin kashe shi.

" SAI YA FITA DAGA (ALKARYAR) YANA MAI JIN TSORO YANA SAUNA. YA CE: YA UBANGIJINA KA TSERAR DA NI DAGA MUTANE AZZALUMAI". (Suratul kasasi: aya ta 21).

Yana daga cikin nau’ika na hijrah tashi daga garin da kake jin za kwace maka dukiyarka a hana ka walwalar kasuwancinka zuwa ga garin da za ka sami ‘yancin na walwalar kasuwancinka, ko zuba jarinka a inda kake so ta hanyar da ta dace a shari’a, wannan ya halatta, don haka wannan nau’ika ne na hijrah. Abin da ya sa duk na kawo mana wannan, don saboda mu san cewa hijrah tana da fadi ko wane nau’i daya in zamu daukeshi mu yi magana a kai, Khutuba daya ta yi mana kadan mu tattauna a kansa. To idan hijrah tana da wannan fadin tana da wannan yalwar, hijrah tana da na ayoyin cikin Alkur’ani da hadisai na Manzon Allah (s.a.w) don me kowane jahili, ko mai karamin sani sai ya tattauna a kan hijrah? Ko wane mutum sai ya bada fatawa a kan hijrah irin yadda ya ga dama, ba tare da goyon bayan wata aya ba da ya kiyaye lafazanta, ko ya san ma’anarta, ingantacciyar ma’ana? Ba tare da sanin wadansu hadisai ba, da zai iya rarrabe tsakanin ingantattu ta hanyar bayanai da zakakuran malamai suka yi a dogon tarihin wannan al’umma ta Annabi Muhammadu (s.a.w) don me? Da wane dalili? Da wace hujjar zai tattauna akan abin da ba shi da ilmi a kai? Har ya sa wani ko shi ya sa kansa ko ya yi rubutu, ko da Hausa ko da turanci, ko ya zuga ko a zuga shi ya zugu, haka kawai a kan abin da bashi da masaniya a kai a cikin addinin. Mai zai fadawa Allah ranar tashin kiyama idan ya tsaya a gabanSa? Mai zai fada a cikin kabari idan mala’iku sun tambaye shi? Mene ne hujjar da zata kare shi a gaban Allah?

Akwai hadarin gaske, akwai ganganci, tattaunawa a kan irin wannan matsala, har wa[ansu su fito su rin]a kafirta musulmi, cewa duk wanda ya shiga cikin gwamnati kafiri ne, wanda ya shiga cikin soja kafiri ne, mai aikin dan sanda kafiri ne, mai aikin gwamnatin da take ita ma bata aikin da قال الله قال رسوله

( Kalal Lahu, Kala Rasulul Lahi) shi ma kafiri ne, haka duk dalibin da yake karatu a jami’a ko wata babban kwaleji shi ma kafiri ne, mai karatun boko kafiri ne, wannan jahilci ne, wannan rashin sanin makama ne, wannan wauta ce da rashin sanin ya kamata.

Wannan ya zama wajibi ga malamai da daliban ilmi su yiwa al’ummar Manzon Allah (s.a.w) bayani karara, kan yadda za a yi a game da wannan mas’ala, a gane ta a santa, da dalilanta cikin kur’ani da hadisi, kuma ya zama wajibi ga dukkan wani wanda bai sani ba ya yi tambaya. " KU TAMBAYI MA’ABOTA SANI IN BAKU DA SANI". Allah ya wajabta a kan duk wanda bai sani ba ya yi tambaya, don me zaka zauna ka za\arwa kanka a saka cikin jerin mutanen da Manzon Allah ya ce : " duk wanda ya yi kururuwa sai su bi shi, a yi da kai nan dama; wata rana a yi hagu da kai; wata rana a jefaka ramin kura, wata rana a ramin gafiya, wata rana ramin bera; don me? Zaka zabarwa kanka tafarkin bata? Ka ratayawa kanka akala ka zargawa kanka igiya da kanka ka mika a hannun wadannan jahilai marasa sanin ya kamata, su kai ka inda suka ga dama, su kai ka su baro? Wannan akidar ta bullo ne a Borno, wadansu ‘yan watanni da suka wuce a baya, a kai rigima a ka kare, mun tattauna a kanta da wadansu daga cikin ‘yan uwa da suke da sun fahimceta ba daidai ba, da yawa daga cikinsu Allah (M) ya ganar da su, ba don zabin harshen mu ba, a a sai don Ubangijin ya yi musu taufiki yana son su da gaskiya, sai don ikhlasi a cikin zukatansu, sai don suna fifita gaskiya a kan waninta, suka fahimta ba gwanintar magana ba ne, ba azancin magana ba ne, ba dabarar zance ba ne, son su da gaskiya ne ya sa suka gane. Amma wadansu suna nan sun taurare, sun kangare, wa[ansu sun yi hijrah sun tafi wani gari wai shi Darus Salam a cikin Jihar Niger (Neja) wa[ansu kuma suna je can wata karamar hukuma a cikin jihar Yobe kusa da iyaka da Niger sun zauna da bukkokinsu. Wadandsu yara suna karanta Medicine a University ta Maiduguri suka bari, wadansu suns karanta engineering, wadansu suna karanta Political science, wadansu suna karanta Islamic studies, wadansu mahaddatan al kur’ani ne, wadansu maza, wadansu mata, wai har ma shaidan ke kawata musu wai tunda garin duk kafirai ne, idan mace ta fahimci haka, to ya kamata ta yi hijirah ta kauracewa mijinta. Wani bawan Allah ya zo min daga nan cikin garin Takai ya ce min matarsa ta yi hijirah, ta barshi ta je wancan garin, kuma an daura mata aure da wani muhajirin wai ita almuhajirah shi kuma muhajiri, akwai almuhajirun wal muhajirat duk a cikinsu. Wani ya same ni ya ce min ‘ya’yansa suna karatu a Jami’u amma suka rabu da shi sun gudu sun barshi. To anan wurin ka ga ya zamo wajibi ga daliban ilmi yin bayanin gaskiya da dalilanta, domin mutane su fahimce ta, kuma ya zama wajibi ga hukuma daukar matakan da suka dace na tsaro a kan masu irin wannan akida, masu wannan mummunar tunani, kuma ya zama wajibi ga ‘yan uwa Ahlus Sunnah su sani cewa asalin tarihin wannan mutane sune جماعة التكفير والهجرة (Jama’atuk Takfir wal Hijrah) wadda ta kunno kai a Misira da Sudan kuma duk inda suke ba ruwansu da masallaci sai masallatan Ahlus Sunnah, duk inda suke suna yada akidarsu ne a cikin Ahlus Sunnah, don suna ganin a nan ne ake samun zaratan samari da son gaskiya ya kawo su da son aiwatar da ita, to amma kuma da yake yawancinsu ba su da ilmin adddini, sai a sami wani wanda ya karasu a ilmin shi fa ba malami ba ne, abin da da ya sani bambancinsa da su kila awa biyu da sani ko bambancinsa da nasu kila yini [aya, ya sani a yau kafin gari ya waye shi ya sanar da su abin, ba shi da abin da zai sanar da su gobe sai ya nemo a yau din da daddare gobe ya sanar da su ta]in da ke tsakaninsu dan karami ne, sai ya sanar da su shi ke nan. To abin da yake bani takaici da ban haushi shi ne; ma’aikatan tsaro duk sun san irin wannan amma ba su daukar matakin da ya dace a kansu, yanzu ‘yan tatsine suna nan a Maiduguri, in ka raba masu sana’o’in kananan sana’o’i tura (Wheel barrow) (Shoe shiner) yankan farce da wa[ansu ]ananan sana’o’I, kusan rabi da rabinsu ( kashi hamsin cikin dari) ‘yan tatsine ne, kuma suna shiga cikin manya-manya sana’o’I, suna da manya-manyan gidajen burodi wanda kusan sulusin biredin da ake ci a Maiduguri ‘yan tatsine ne suke yi, kuma hukumomin tsaro sun san wannan, kuma ba a yi komai ba. ‘Yan tatsine da sanadiyyarsu ne a ka yi asarar rayuka a Kano, a ka yi a Borno, a ka yi a Jihar Adamawa tun tana tsohuwar Jihar Gongola, da Bauchi, da Jos, da sauran wurare da Kaduna har yanzu, kuma an zuba musu ido ana kallonsu, Jam’atut Takfir Wal Hijrah idan ma’aikatan tsaronmu ba su san su ba, su tambayi (Intelligence) na Egypt ko su tambayi na Sudan su ji sharrinsu. Saboda haka, mu dai mun riga mun fadakar, ba mu da hukunci a hannunmu, amma muna da ayoyin Al kura’ni da hadisan Manzon Allah (s.a.w) da zamu yi bayanin gaskiya da dalilanta. Ganin damar ka ne ka kama tafarkin gaskiya in kana son haduwa da Allah lami lafiya gobe kiyama, ganin damarka ne ka dakile a kan bata ka biyewa son zuciyarka ka bi shaidaninka, ka kangare, ka kafirce, sannan kuma ka tanadi abinda za ka fadawa Mahallicinka ranar tashin kiyama. Sannan wadannan mutane sukan yi amfani da shubuhohi, su kawa ayoyin da suke maganar hijrah su kafirta mutane. Su ce Allah ya ce:

"WADANDA MALA’IKU ZA SU KASHE SU SUNA ZALUNTAR KAWUNANSU" (suratul Nisa’I aya ta: 97)

Ma’ana: wadanda ba su yi hijrah ba ke nan, sai ka ji kai din nan da kake unguwar Dorayi azzalumi ne, in ba ka yi hijrah ba, ka tafi Darus Salam. To ita kuma asalin hijrah din daga ina zuwa ina? Ya kamata ka tambayi kanka, ga dai nau’ikan hijrah na ambata a baya, kai wacce za ka yi cikin wadannan? Kuma mene ne madogararka cikin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (s.a.w)?

Sannan mun san mutanen da suka zauna a garin kafirai (a dauka ma cewa garin kafirai ne tsantsa) ba su yi hijrah ba har suka mutu, mene ne hukumcinsu kai a wajenka? Kafirai ne ko musulmai? Ilmi na hukunta cewa " Mu kasa su gida uku".

1- Daga cikinsu wasu kafirai ne tsantsa

2- Wasu Musulmi ne masu sabo

3- Wasu Musulmi wadanda ba su da wani sabo ba su da wani laifi (don ba su yi hijrah ba).

1. Kashi na farko: - wadanda sun zabi su zauna a garin kafirai don suna son kafirci sama da imani, suna taimakawa kafirai akan muminai, taimako da dukiya, taimako da harshe, taimako da baki. Irin wadannan kafirai ne, da su ake magana cikin

" KA DA MUMINI YA YARDA YA SO KAFIRAI YA KYALE MUMINAI, WANDA DUK YA YI HAKA SHI BA KOWA BANE A WAJEN ALLAH" (Suratu al Imran: aya ta 28).

Ibnu Jarir Attabari ya ce: " ya kafirta idan ya yi haka".

2. Kashi na biyu: - wadanda su musulmi ne, ba sa taimakawa kafirai, ba sa aibata muminai ‘yanuwansu, ba su yarda ba su taimakawa kafirai da dukiya ko da komai, amma sun zabi zama a garin kafirai. Imma saboda wani son zuciyarsu ko don saboda dukiya ko don saboda jin dadin duniya ko wata rayuwa ta duniya. Sun kasa bayyana addininsu a garin, amma duk da haka sun yarda da su zauna a garin. Abin da ake nufi bayyana addini " fitowa fili su yi bara’a da kafirci, su ce ba su yarda da shi ba, sun kasa bayyana haka. To irin wanda suka zauna cikin wannan hali, sune wanda idan sun mutu, Ubangiji na masu barazana da azaba. Abin da suke yi kaba’ira ce, kabira ce cikin kaba’ir, kaba’iruz zunub, ana yi musu barazana da gidan wuta sai fa in Allah ya ga dama ya yafe musu. Tun da kuma :

"YANA GAFARTA KOMAI BAYAN WANNAN (SHIRKA) GA WANDA YA SO".(suratun Nisa’I aya ta : 48)

kuma ko sun shiga wuta ba za su dawwama a cikinta ba, tunda ba kafirai ba ne su.

3. Kashi na uku:- wadanda suka zauna ba su yi hijrah ba, saboda daya daga cikin dalilai guda biyu.

i. Imma sun zauna suna bayyana addininsu don su kalubalanci kafirai, ko a baki, ko a rubutu, su ce a bu kaza kafirci ne, abu kaza shirka ne, abu kaza bai dace ba, abu kaza ya sabawa Allah ya sa\awa Manzon Allah. Suna zaune a garin, sun ki tafiya suna da wannan ‘yanci na su fada, kuma sun fada kowa ya ji. Ko a rubutu ko a baki, irin wadannan ba su da laifi ko sun zauna a garin kafirai har sun mutu, don zamansu Jihadi ne, gwagwarmaya ne, da kafirai a garinsu. Su kalubalance shi a garin, a kafar watsa labaran shi a jaridunsa da talabijin dinsa da rediyonsa, su lakuce wa kafirci hanci a gidansa. Wannan zamansu a garin jihadi ne in suna da ikon yin haka.

ii. Kashi ne biyu, wadanda suna so su yi hijrah ba su da ikon yin hijrah, garin da zaa je hijrah nesa ne, ba za su iya tafiya ba shi ne Allah ya ce: " SAI WADANDA SUKE MASU RAUNI AN RAUNANA SU CIKIN MAZA DA MATA DA YARA K ANANA WADANDA SUKE ALLAH YA YI MUSU RANGWAME DON ALLAH YA KASANCE MAI AFUWA NE MAI JIN KAI". (Suratun Nisa’i aya ta:) saboda haka wannan shi ne kashe-kashen su a ilmance yadda ayoyin Al kur’ani suka ce da su.

Su da suka ce: ‘ wai aka ce’ " ظالمي أنفسهم " sai suka ce kafirai ne, bayan Allah ya ambaci "ظالم لنفسه " cikin ‘yan aljannah, to amma saboda jahiltarsu da Alkur’ani ko hadisi sai su dauki ayoyin da ba su kamala haddace su ba ballantana sanin ma’anarsu, su kafirta muminai da su. Ya Ubangiji ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.

Assalamu alaikum.

 

 

 

Enter subhead content here

Enter content here

Enter supporting content here