Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM

 

    An haife shi ranar 12 ga watan Fabrairu shekarar1960, a garin Daura cikin jahar Katsina a Nijeriya.
    Yayi karatun Al-qur'ani a gidansu a wurin mijin yayarsa wato Malam Haruna. Daga nan sai aka kawo shi unguwar Fagge a Kano wurin Malam Abdullahi, ya fara haddar Alkur'ani a gida sannan ya kammala anan
Kano a 1978. Daga nan sai Malam ya shiga makarantar Arabic school karkashin cibiyar Egyptian Cultural Center dake Bello Dandago Road a 1981. A wannan lokaci, Malam yana zuwa makarantar Adult School dake Shahuci, da daddare, ita kuma Egyptian Centre da yamma.
    Ya kammala a shekarar 1984, wannan ya bashi damar shiga
Government Arabic Teachers College Gwale a 1984, ya kammala a 1988. Daga  nan ne kuma Malam ya samu shiga Jami'ar Musulunci ta Madina a 1989 zuwa 1993. Daga cikin Malamansa akwai Sheikh Abdul Rafi'i, Dr. Mahmud Abdul Haliq sai Dr. Khald As-Sabat.
    Bayan Malam ya dawo daga Madina ya cigaba da karatu a Jami'ar Bayero daga baya wasu matsaloli suka hana shi cigaba. Amma a halin yanzu yana yin digirinsa na biyu a '
International University of Africa', dake Sudan.
    Bayan Malam ya dawo daga Madina ne ya kafa Makarantar Usman Bin Affan daga nan ta samu  cigaba ta zama cibiya mai zaman kanta a 1995. Sai darussa da Malam yake gabatarwa anan Usman bin Affan, na farko akwai karatun tafsiri ya da yake gabatarwa a ranar jumma'a tsakanin magariba da isha'i, ranar asabar karatun nahawu da balaga da safe da misalin
8:00am zuwa 9:30am. Sannan kuma karatun sirah ranar lahadi a Masallacin Almuntada dake Dorayi tsakanin magriba zuwa isha'I, sai laraba kuma da yake gabatar da tafsiri a Masallacin Beirut, tsakanin magriba zuwa isha'i da kuma darussan da Malam yake gabatarwa a makaranta.
    Bayan haka, Malam yana gabatar da tafsiri a
Maiduguri a watan Azumi kuma shekara tara kenan da farawa.
    A halin yanzu Malam shine shugaban cibiyar Usman Bin Affan Islamic trust kuma limamin jumma'a na Masallacin Almuntada dake dorayi a
Kano.
    Malam yana cikin mambobin kwamitin Malamai wato "Ulama Consultative"
Zamfara State da Bauchi State. Haka kuma, Malam yana gabatar da shirye shirye a gidajen radio da talabijin da yawa, amma kadan daga cikinsu akwai na Radio Kaduna, Bauchi Radio corporation, CTV Kano, dana DITV Kaduna NTA Borno, OITV Damaturu, NTA Yola, da sauransu.
  Malam yana da iyali ( mata biyu) da 'yaya (biyar) kuma yana zaune ne a unguwar Gadon kaya cikin birnin
Kano.

 

Enter subhead content here

Enter content here

Enter content here

Enter content here

Enter supporting content here