Make your own free website on Tripod.com

MIMBARIL ISLAM

FATAWOYIN GOMAN FARKO NA WATAN BABBAR SALLAH DA LAYYA DA SALLAR IDI

Shafin Gida
Kaunar Manzon Allah (s.a.w)
Dogaro Da Kai da Kyautata Mu'amala
Halin Da Duniyar Musulunci Take Ciki
Hukuncin Hijira
Ramadan
Sheikh Ja'afar mahmud Adam
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Muhammad Nazeef Inuwa
FATAWOYIN LAYYA
Kiyaye Harshe Daga Alfasha
Musulunci, Imani da kyawawan Aiki
AIKIN HISBA A ZAMANIN ANNABI DA SAHABBAI
FATAWOYI AKAN WATAN RAJAB
FATAWA AKAN AZUMI
FATAWA AKAN HAJJI, UMRAH DA ZIYARA

 

FATAWOYIN
Falalar Goman Farko na
Watan Babbar Salla
Da Layya da Sallar Idi
BISA
FAHIMTAR LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR MANZON ALLAH (S.A.W.)
DA
FAHIMTAR MAGABATA NA kWARAI
NA
SHEIKH ABDUL WAHAB BN ABDALLAH
 

MAJLISIN AHLUSSUNNA WAL JAM'AH MASALLACIN IBN TAIMIYAH, SHARAdA PHASE II, KANO NIGERIA
mimbarilislam.tripod.com
All Rights Reserbed©
 
Abubuwan Da Suke Ciki

   SHAFI
 Gabatarwa  3
1.  Tambaya: Menene falalar ranaku goma na farkon Zul-hijjah, kuma wace irin ibada ya kamata mutum ya yi a cikin su?    4
2.  Tambaya: Menene Layya A Shari’an Ce? 
3.  Tambaya: Menene Hukuncin Layya? 
4.  Tambaya: Wacce irin Falala Ubangiji Ya Tanadarwa Mai Yin Layya? 
5.  Tambaya: Menene Matsayin Wanda Allah Ya bashi ikon Yin Layya, Amma Ya ki yi? 
6.  Tambaya: Wanda Allah Ya bashi damar yin layya amma iyayensa basu sami dama ba, shin ya kamata yayi ko kuwa zai bawa iyayen sa ne suyi? 
7.  Tambaya: Menene Sharuddan Layya? 
8.  Tambaya: Wadanne sunnoni ne da mustahabbai ya kamata mai nufin yin layya ya aikatasu da zarar watan Zul hijja ya tsaya? 
9.  Tambaya: Yaushe ya kamata a yanka dabbar layya ? 
10.  Tambaya: A ina ya kamata liman ya yanka layyar sa a sunnance? 
11.  Tambaya: Shin matafiyi an dauke masa yin layya kamar yadda aka yi masa rangwame na kasaru a salloli? 
12.  Tambaya: Shin akwai wakilci  a wajen Yanka dabbar layya? kuma ko  wakilin yanada wani kaso na musamman daga naman layyar? 
13.  Tambaya: Shin ya halatta mutane su yi  tarayya akan dabbar layya guda daya? 
14.  Tambaya: Shin watanda ko kakkawa na iya zama layya, kuma menene hukuncinta? 
15.  Tambaya: Shin hukuncin layya ya takaita ne akan magidanci ko kuwa ya shafi kowa da kowa? 
16.  Tambaya: Shin ya halatta Matar auren da take da hali ta yi layya? ko kuwa zata dogara ne da na mijinta? 
17.  Tambaya: Shin ya halatta a yi wa mamaci layya? 
18.  Tambaya: Menene hukuncin wanda ya cinye naman layyar sa baki daya, bai bada sadaka ba? 
19.  Tambaya: Menene hukuncin wanda ya sayar da fatar layyar sa? 
20.  Tambaya: Muna ganin ana wanke dabbar layya, shin hakan yana da asali a cikin shari'ah, ko aikin magabata na kwarai? 
21.  Tambaya: Wadansu basa wanke naman layyar su, shin aikata haka aikin magabata na kwarai ne? 
22.  Tambaya: Shin wanda Allah bai hore masa abin layya ba, ko abin suna, zai iya yanka kasa ko tuwo, yadda wadansu mutane suke aikatawa? 
23.  Tambaya: Shin idan mutum ya fara yin layya, ta lazimce shi kenan, koda kuwa bai samu hali ba wata shekarar? 
24.  Tambaya: Menene hukuncin wadanda suke yin bara da roko domin su sami abin layya? 
25.  Tambaya: Muna ganin mutane suna ajiye jelar dabbar layyar su, shin haka yana da asali a aikin magabata na kwarai ko kuwa al'ada ce mara tushe? 
26.  Tambaya: Shin mala'iku suna sa albarka a naman layya saboda an ajiye shi kwana daya ko biyu ko uku, kamar yadda wasu ke aikatawa? 
27.  Tambaya: Wadanne sunnoni da mustahabbai mai tafiya masallacin Idi ya kamata ya aikata a yayin tafiyar sa? 
 
MUkADDIMAR BUGU NA BIYU
Bismillahi, Wassalatu wassalamu ala Rasulillah, wa ala Alihi wa Sahbihi wa man Walahu.
Bayan haka:
Tun lokacin da aka buga littafin Fatawoyi akan layya na babban malamin mu Shaikh Abdul-Wahhab ibn Abdillah ibn Muhammad, mutane sun yaba da zurfin binciken da aka yi da salon amsa tambayoyi da aka bi wajen ba da fatawoyin. Wannan ya sa bukatuwar littafin ga jama’a ta yawaita.
Kasancewar watan Zul-Hijjah na wannan shekarar na kara kusantowa ne, muka ga dacewar a sake buga littafin don amfanin al’ummar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam).
Maimakon a buga shi kamar yadda yake a bugun farko, an ga dacewar a sake bibiyarsa don kara kyautata shi. Wannan ya sa aka gyara tsarin rubutun da kurakuransa, ta yadda zai dace da salon rubutu na Hausa, kuma aka kara wadansu mas’aloli, tare da tahakikin littafin baki daya. Sannan aka canja masa suna zuwa: Fatawowin Goman Farko na watan Babbar Sallah.
Muna rokon Allah Ya sanya wa littafin albarka, kuma Ya kara wa malam lafiya da sararin yin bincike da karantar da al’umma sahihiyar Sunnar Ma’aiki (Sallallahu alaihi Wasallam) bisa fahimtar magabata na kwarai. Kuma Allah Ya albarkaci rayuwarsa da zuriyarsa da mu dalibansa, kuma Ya yafe mana kurakuran mu baki daya, amin.
Daga karshe, muna godiya ga `yan’uwa da suka taimaka ta kowace hanya wajen tabbatar da wannan aiki, musamman Ahmad Bello Dogarawa da Imam Khidir Muhammad Bello da kasim Muhammad Aminu da suka taimaka wajen bitar littafin da tsara rubutun Hausa da gyare-gyaren da suka dace a cikinsa. Allah ya sakawa kowa da alherin sa, amin.

daliban malam
Zul-ka’adah 26, 1425
 
MUkADDIMAR BUGU NA FARKO
O
???????? ????? ????? ??????? ??? ????????? ??????? ?????????? ???????????, ????????? ?????????? ????????
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM WASALLALLAHU ALAN NABIYIL KARIM
Dukkan yabo da girmamawa sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki, Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Shugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallamda alayenSa da SahabbanSa.  Bayan haka, wannan littafi mai suna "FATAWOYIN LAYYA", wanda Sheikh Abdul Wahab bn AbdAllah Ya rubuta ya kunshi bayanai akan abinda ya shafi hukunce hukuncen layya da falalar kwanaki goma na farkon watan Zul hijja, bisa fahimtar littafin Allah da Hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da kuma fahimtar magabata na kwarai.
Muna fatan Allah Ya karbi wannan aiki, Ya sa masa albarka, kumaYa amfanar da al'ummar musulmi da abinda ya ke kunshe a cikinsa, Amin.  
Wassalamu Alaikum Warahmatullah
  Shawwal 1424 AH
  December 2003 A.C.
 
??? ???? ??? ??? ??? ???
1. Tambaya:  Menene falalar ranaku goma na farkon Zul-hijjah? kuma wace irin ibada ya kamata mutum ya yi a cikin su?
Amsa: Hakika wadannan ranaku ne masu falala, domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Abbas (R.A) yace:  Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: "Babu wasu ranaku da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa a wajen Allah Subhanahu wata’ala kamar wadannan ranaku (goma na farkon Zul Hijja). Sai suka ce ya ma'aikin Allah Sallallahu alaihi Wasallamkoda jihadi fisabilillahi ne? Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: "Ko da jihadi fisabilillahi ne, sai dai mutumin da ya fita jihadi da ransa da dukiyarsa kuma bai koma gida da wani abu ba". (Ma'ana, ya yi Shahada  a fagen fama harda dukiya baki daya)” .
Haka kuma: An karbo daga Jabir bn Abdullah (RA) yace. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace: "Mafificin Ranakun duniya su ne ranaku goma (yana nufin goman farkon  Zulhijja). Sai aka ce da shi: Babu kwatankwacinsu ko a jihadi fi sabilillahi? Sai yace: "Babu kwatankwacinsu sai dai mutumin da aka turmuza fuskarsa a cikin turbaya (ma'ana yayi shahada a fagen fama) .
Domin haka Sa'id bn Jubair ya kasance, yayinda ranaku goma na farkon Zul hijja suka shiga yana yawaita ibada a cikin su. Saboda haka zai yi kyau ga dukkan mai kaunar Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) kauna ta hakika ya kasance yana kyautata ayyukan sa a cikin wadannan ranaku.
Ibadar da ya kamata  a yi cikin su.
(a) Mafi soyuwar aikin da aka fi so shi ne, azumin ranar Arfa. Saboda hadisin da ya tabbata a cikin Sahihu Muslim, a karshen hadisin da Abu katada ya ruwaito cewa Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) yace: "Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta wuce da wadda take gabanta" ..
(b) Yawan zikiri da addu'o'i da yawaita kabbara da hailala da hamdala ga Allah (SWT). “Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace: "Fiyayyar  addu'a, addu'ar ranar Arfa, kuma fiyayyen abinda na fada ni da Annabawan da suka gabace ni, ita ce:
((??? ?????? ?????? ????? ???????? ??? ??????? ????? ???? ????????? ?????? ????????? ?????? ????? ????? ?????? ???????))
Lailaha Illallahu Wahdahu La Sharikalah, Lahul Mulku Walahul Hamdu Wahuwa Ala Kulli Shai'in kadir(1)
Sannan hadisi ya tabbata a cikin Musnad daga Abdullahi dan Umar (RA) yace: Manzon Allah  (??? ???? ???? ?????)  yace: "Babu wasu ranaku mafiya girma a wurin Allah, kuma babu wasu ayyuka mafiya soyuwa a gareShi kamar wadannan ranaku goma (na farko Zulhijja), domin haka ku yawaita hailala, kabbarori da hamdala a cikin su" .
(c) Yawan yin sadaka: Dalilin yawaita sadaka kuma shine, Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) ya yanka rakuma dari na hadayarsa kuma yasa aka rabar da naman gaba daya harda akalar rakuman da fatunsu.
(d) Haka nan kuma ana son wadannan zikiran da za a kawo nan gaba ayi ta maimaitasu a bayan sallar farilla ko nafila, wannan ya shafi maza da mata baki daya. Ana son maza su daga murya, mata kuma su yi gwargwadon yadda za su jiyar da kawunan su. Dalili kuwa shi ne: Sayyidina Umar (RA) ya kasance yana kabbarori a hemarsa a Mina, sai mutanen masallaci suyi ta kabbarori idan sunji yayi. Mutanen kasuwanni kuma suna tayi har sai Mina ta girgiza da kabbarori. Ibnu Umar ya kasance yana kabbarori a wannan kwanakin da bayan salloli da cikin rumfar sa da mazaunin sa da matafiyar sa a wannan yinin gaba daya .
“Nana Maimuna (R.A) ta kasance tana kabbara a ranakun Mina, Haka kuma Mata sun kasance suna yin kabbara a bayan Abanu bn Usman da Umar bn Abdil-Aziz a ranakun Mina” (a masallaci)  .
(e) Haka kuma ana son mutum ya nemi kusanci da Allah Subhanahu wata’ala da yin layya ga Wanda baije aikin Hajji ba. Wanda kuma ya je aikin Hajji, sai ya yi hadaya.
2. Tambaya:  Menene Layya A Shari’an Ce?
Amsa: Layya a Shari’a ita ce yanka daga cikin  Bahimatul an'am  (wato dabbobin ni’ima), tun daga bayan sallar idi har zuwa faduwar ranar sha uku ga watan Zul Hijja, saboda neman kusanci da Allah Subhanahu Wata'ala. Dalili kuwa shine: fadin Allah ta'ala cikin suratul hajj.
((???????????? ?????????? ?????? ???????????? ????? ????? ??? ?????? ?? ??????????? ???? ??? ?????????? ???? ?????????  ???????????...)) [???? ????: 28].
Ma'ana:  “Domin su halarci abubuwan amfani a gare su, kuma su ambaci sunan Allah a cikin  kwanuka sanannu, saboda abinda Allah ya azurtasu dashi na daga dabbobin ni'ima…”  (Hajji, aya ta: 28).
 An karbo daga Abdullahi Ibn Abbas  (RA) yace:  Kwanaki sanannu sune:  kwanaki goma na farkon Zul Hijja, ya sake cewa: ranar layya, da kwanaki uku da suke bayanta. Yaci gaba da cewa:  hakika Allah Subhanahu wata’ala ya sanya wannan lokaci ne domin ambaton SunanSa. Bukhari ya ambace shi ta'alikan. Hafiz yace isnadinsa sahihi ne .
 Haka Kuma hadisi ya tabbata a cikin  Silsila Sahiha daga Jubairu Ibn Mud'im yace: “Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace:  "Dukkan ranakun tashrik  ranakun yanka ne ". A kan haka ne kuma magabata suka tafi kamar su Imam Al-Shafi'i,  da Auza'I, da Hasanul Basri, da  Imam Ahmad,  da Imam Malik da Abu Hanifa Allah ya yarda da su baki daya .
Haka kuma ya tabbata cewa sahabbai suna yin yanka  acikin wadannan ranaku.
3. Tambaya:  Menene Hukuncin Layya A Shari’ah?
Amsa:  “Hakika layya sunna ce mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah (??? ???? ???? ?????). Ubangiji (SWT) ya umarci AnnabinSa (??? ???? ???? ?????) da yinta a cikin Suratul Kauthar inda yake cewa:
((??? ??????? ??????. ??? ???? ??????)) [??????: 1-2].
Ma'ana: Hakika Mun ba Ka Al-Kausara, saboda haka ka yi Sallah ga Ubangijinka, kuma ka soke (hadayarka ko layyarka).” [Kauthar 1 – 2]. 
 Haka kuma Allah Madaukakin Sarki Ya kara da cewa:. 
((???? ????? ???????? ????????? ??????????? ?????????? ??????? ????? ????????????. ??? ???? ??? ???? ?????????? ???????? ??????? ??????? ??????????????)).
Ma'ana:  "Kace! hakika Salla ta da yanke-yankena, da rayuwa ta, da mutuwata, duk suna ga Allah Ubangijin talikai, ba Shi da abokin tarayya, kuma da haka aka umarce ni, kuma nine farkon masu mika wuya"  [An ' Am 163].
 Kuma Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) Ya umarci alummar sa da suyi layya mutukar suna da ikon yi, dalili kuwa shine hadisin daya tabbata a cikin Sunan Abu Dawud, Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) yace: "Ya ku mutane hakika yana kan kowanne magidanci da iyalan sa yin layya a kowacce shekara. Manzon Allah ya fadi haka ne alhali yana tsayuwar Arfa .
Haka kuma hadisi ya tabbata daga Abu Hurarira (RA) cewa Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) yace: "Duk wanda Allah ya bashi yalwar yin layya bai yi ba, to kada ya kusanci wurin sallar idinmu" . 
 An karbo daga Anas dan Malik (R.A) yace: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yanka raguna biyu masu kahonni guda biyu farare tas da hannunsa mai albarka, a matsayin layyar Sa, sannan ya ambaci sunan Allah, Ya girmama shi (watau a lokacin yin yanka ya kasance yana cewa: (Bismillahi Allahu Akbar)
Kuma Malamai sun hadu akan cewa ita layya tana daga cikin Ibada, amma ga wanda Allah Ya bashi iko kawai.
4. Tambaya: Wacce irin Falala Ubangiji Tabaraka wata’ala Ya Tanadarwa Mai Yin Layya?
Amsa: Ubangiji Tabaraka wata’ala Ya tanadarwa Mai yin layya alherai da dama, amma ga kadan daga cikin su kamar haka:
(1) Allah Ta’ala Zai sa shi daga cikin masu tsoronSa  idan har ya kyautata niyya, Saboda Allah Subhanahu wata’ala yace:
((???? ??????? ????? ????????? ????? ?????????? ???????? ????????? ?????????? ????????))
Ma'ana: "Naman ta ko jininta, ba sune suke isa wajen Allah ba,   sai dai tsoron Allan ku shine ya ke isa wajenSa". [Hajj: 37]
(2) Haka kuma Allah Ta’ala zai sanya shi ya kasance  daga cikin managarta, domin a karshen ayar Allah Subhanahu wata’ala yace, “ka yiwa managarta bushara.” Wannan ya nuna cewa mutane managarta ne kadai suke iya yin layya.
(3) Haka Kuma Allah Ta’ala Zai sa a rubuta masa ladan masu raya sunnar Annabi  Ibrahim  (AS) da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam matukar ba da kudin haram ya yi layyar ba.
(4) Haka Kuma Allah Ta’ala Zai sa shi daga cikin masu tausayawa fakirai da makwabta, in dai har ya raba layyar yadda sunna ta koyar.
(5) Imam Darakudni ya ruwaito hadisi daga Ibnu Abbas (RA) yace: Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) yace: "Babu wata dukiya da aka ciyar mafificiya sama da dukiyar da aka yi layya da ita" (Imamu Hakim ya inganta shi, kuma Imam Zahabi yayi muwafaka da shi akan haka) .
Duk da irin falalar da layya take da ita akwai hadisai da aka kago akan falalar layya, inda suke cewa, wai Zaidu bin Arkam yace: "…suka ce ya Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) mecece wannan layyar ne? Sai yace: Ai sunnar babanku  Ibrahim ce (AS), sai suka ce: Me zamu samu idan mun yita? Sai yace: Ko wane gashi daya na dabbar lada ne". To wannan hadisin maudhu'i   ne, domin a cikin sanadin sa akwai Nufail Bin Harith, wanda malamai suke tuhumar sa da kaga hadisai na karya, kuma ire-iren wadannan hadisai suna da yawa.
 Akwai wani hadisi dha'ifi (mai rauni) shima da ake cewa wai Nana Aisha ta ruwaito cewa Manzon Allah (??? ???? ??????? ?????) yace: "Babu wani aiki da dan Adam zai yi a ranar idin babbar sallah kamar zubar da jinin dabbar layya, Yace wai hakika dabbar zata zo da kahonta da kofatonta da gashinta, hakika jininta zai isa wurin Allah kafin ya zuba kasa, saboda haka ku yi ta da dadin rai" .
5. Tambaya: Menene Matsayin Wanda Allah Ya bashi ikon Yin Layya, Amma Ya ki yi?
Amsa: Hakika wanda Allah Ta’ala ya ba shi ikon yin layya amma ya ki yi ya sabawa sunnar Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) da aikin magabata na kwarai, kuma ukubar sa itace kada ma ya kusanci masallaci, yayi zaman sa a gida, saboda hadisin daya tabbata daga Abu Huraira (RA) yace: Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) yace: "Wanda Allah ya bashi yalwar yin layya, amma bai yi ba kada ya kusanci wajen sallar idin mu" .
6. Tambaya: Wanda Allah Ya bashi damar yin layya amma Iyayen sa basu sami dama ba, shin ya kamata ya yi, ko kuwa zai bawa iyayensa ne su yi?
Amsa: Yakamata a fahimci cewa a wajen sha’anin addini yi wa Allah da ManzonSa biyayya shi ne gaba da komai.Saboda haka tunda ya ke, ita layya Ibada ce, wanda duk Allah ya bawa dama, yakamata ya fara gabatar da tasa layyar. Amma idan yana da iko sai ya gabatar da tasa, sannan kuma  ya sayawa Iyayen sa abinda za su yi tasu.
7. Tambaya: Menene Sharuddan Layya?
Amsa:
(1) Yana daga cikin Sharuddan Layya, abinda za a yanka, lallai ya kasance daga cikin Bahimatul an'am  (Dabbobin Ni’ima), irin su Rakuma, Shanu, Awaki, da Tumaki). Domin haka baya cikin sharuddan layya , a yi ta da  namun daji, kuma ba za'a yanka kaji ba kamar yadda wasu daga cikin yan Zahiriyya su ka tafi akai, dalili kuwa saboda  fadin Allah Subhanahu wata’ala. cewa:-
((????????? ??????? ????????? ????????? ???????????? ????? ????? ????? ??? ?????????? ???? ???????? ????????????))
Ma'ana: “Ko wacce al'umma Mun sanya musu Ibadunsu, domin su ambaci sunan Allah a bisa abinda Allah Ya arzuta su dashi daga cikin dabbobin ni'ima". (Hajj 34).
 Wannan Aya ta nuna cewa, Allah Ta’ala ya ambaci dabbobin ni'ima ,kuma Ya nuna cewa lallai ne idan za a yanka su a ambaci sunan Sa. Haka kuma ayar bata ambaci cewa ana iya layya da namun daji ba ko tsuntsaye kamar kaji da sauran su.
(2) Kuma ba a yanka dabba sai wacce ta cika wadannan sharuddan:
• Shanu: Sai sun cika Shekara biyu zuwa sama,
• Rakuma: Kuma sai sun cika Shekara biyar zuwa sama.
• Tumaki da Awaki: Kuma sai sun cika Shekara daya zuwa sama. Sai dai idan ya ta'azzara ba'a samu shekararriya ba, to babu laifi a yanka wacce bata shekera ba cikin Raguna Ko Awaki (watau Jaz'a).  Saboda hadisin da Muslim ya rawaito cewa, "Kada  ku yanka sai shekararriya, sai dai idan ya ta'azzara agareku, sai ku yanka wacce ake kira jaz'a daga raguna" [Muslim (1963) sharhin Khadi Iyadh.]
(3) Haka kuma ana so dabbar da za a yi layya da ita, ta kasance kubutacciya daga aibu. Saboda ba a yin layya da dabba mai larura kamar haka:
• Ba a yanka ramammiya wacce ramarta ta bayyana,
• Ba a yanka gurguwa wacce gurguntakarta ta bayyana.
• Ba a yanka mara lafiyar da rashin lafiyarta ya bayyana.
• Ba a yanka mai yankakken kunne wacce yankan kunnenta ya bayyana
• Ba a yanka mai karyayyen kaho in dai yana jini, amma Imamu Malik (Allah Ya kara masa yarda), yace idan karyewar kahon ya riga ya warke, to babu laifi a yi da ita. 
• Ba a yin layya da wacce hakoranta suka zube saboda tsufa.
• Ba a yin layya da mai ido daya.
• Ba a yin layya da mai hujajjen kunne wacce hudar take da girma.
Wadannan siffofin dabbobin da ba a layya da su ne,  duka ana iya ganin su a cikin hadisin da ya tabbata  na Bara'u dan Azib (R.A) .
(4) Ba a yanka abin layya, sai lokacin da Shari’a ta kebance, watau ba a yanka sai bayan sallar idi.
(5) Abinda zaka yanka na layya ya kasance mallakarsa a ka yi ta hanyar halal, bata hanyar haram ba. Watau wajibi ne ya kasance ba na sata ko kwace ba ne, ba kuma dabbar da aka ba ka jingina ba ce.
8. Tambaya: Wadanne sunnoni ne da mustahabbai ya kamata mai nufin yin layya ya aikata su da zarar watan Zul hijja ya tsaya?
Amsa: 
(1) Hadisi ya tabbata daga Ummu Salama (RA) tace: "Manzon Allah Sallallahu alaihi WasallamYace: "Idan kuka ga jinjirin watan babbar sallah kuma daya daga cikin ku yana son yayi layya to ya kame daga  yin aski da yanke farce" .
(2) Haka kuma an fi so wanda ya yi layya, ya fara cin wani abu daga naman layyar sa, amma ba cewa akayi ya yi azumi ko rikon baki ba, domin haka, ba a hana shi shan abin sha ba. Wannan shine ya tabbata daga Manzon Allah (??? ???? ???? ?????).  Dalili kuwa  hadisi ya tabbata: “An karbo daga Jabir (R.A) yace: Hakika Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yi umarni da a yanki tsoka a kowane rakumi cikin rakuman daya yi layya da su, a sa a tukunya. [a dafa masa]. Sai suka ci naman,  kuma suka  sha romon .
9. Tambaya: Yaushe yakamata a yanka abin layya?
Amsa: Jumhurun Malamai sun tafi akan cewa, ana yanka a bin layya ne, bayan sallar idi ko da liman bai yanka ba. Dalili kuwa shine fadin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya cewa: "Wanda ya yanka abin layyar  sa kafin sallar mu, to ya sake yanka wata dabbar maimakon ta bayan sallar idi, wanda kuma yake so ya yanka bayan sallar mu to ya yanka da sunan Allah" .
Haka kuma Imamu Malik ya tafi akan cewa: "Ba a yanka abin layya, sai bayan Liman ya yanka na sa." Dalilin sa kuwa shi ne, hadisin da aka karbo daga Jabir  dan Abdillahi  (R.A) yace:  "Munyi Sallah tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama  a Madina sai wasu mazaje suka je suka yi  yanka, suna tsammani Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yi yanka, sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace:  "Duk wanda ya yi yanka kafin na yi,  to ya sake yankan sa,  "ya kara da cewa kada ku yi yanka kafin Annabi" .
Wannan shine zance mafi rinjaye, don haka sai mutum ya hakura har liman ya yanka.  Idan kuma mutum yana nesa da gari ne, sai ya kintaci lokacin da ya kamata ace liman ya yanka dabbar layyar sa, sai ya yanka tasa. Wanda kuma ya yanka kafin Sallah, to naman sa ba na layya ba ne, ya zama naman miya kenan, ko ya sani ko bai sani ba. Saboda haka sai ya sake yanka wata maimakon ta. Dalili kuwa shi ne, wani sahabi ya taba yanka dabbar layyar sa kafin sallar idi sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace: "Ya sake yanka wata a maimakon ta . A nan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam bai tambaye shi koya sani ko bai sani ba.  Wallahu A'alam.
10. Tambaya: A ina ya kamata liman ya yanka abin layyar sa a sunnance?
Amsa: A bisa koyarwa irin ta Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) liman zai  yanka abin layyar sa ne a filin idi, domin al'umma su shaida, kuma su sami damar yin ta su layyar ba tare da wani kokwanto ba  .Dalili kuwa shine hadisin Jabir (R.A) yace: "Na halarci idin babbar Sallah tare da Manzon Allah (??? ???? ???? ?????). Bayan ya gama hudubar sa, sai ya sauka, ya je wajen ragon layyar sa. Sai ya yanka shi da hannun sa (mai Albarka) .
 Haka kuma An karbo wani hadisin daga Abdullahi bn Umar (R.A) yace: Hakika Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance yana yanka abin layyar sa a filin idi. Saboda haka ni ma na kasance ina aikata hakan .
11. Tambaya:   Shin an daukewa matafiyi yin layya kamar yadda aka yi masa rangwamen kasaru a sallah?
Amsa: Hakika matafiyi zai iya yin  layya, matukar yana da ikon yi. Dalili akan haka shine hadisin da ya tabbata  acikin Sunanu Ibn Majah kamar haka : An karbo daga Abdullahi Ibn Abbas (R.A) yace:  "Mun kasance muna tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a cikin tafiya, sai babbar Sallah ta same mu akan hanya, sai muka hadu mu goma akan rakumi daya, (a matsayin abin layyarmu).  Mutum bakwai kuma su ka hadu akan Sa guda daya" .
Haka kuma hadisi ya tabbata acikin Abu Dawuda kamar haka: An karbo daga Sauban yace:  "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yi layya da rago ko akuya,  muna cikin tafiya, Sai  Ya ce: "Ya  Sauban ka gyara mana wannan naman"  (Watau dabbar da Ya yi layya da ita), sai Sauban ya ce;  ban gushe ba ina ciyar da shi daga cikin wannan naman layyar, har sai da mu ka iso Madina" .
12. Tambaya:  Shin ko akwai wakilci a wajen Yanka dabbar layya kuma ko wakilin yana da wani kaso na musamman daga naman layyar?
Amsa: Hakika abinda aka fi so shi ne, mutum ya yanka dabbar layyar sa da hannunsa, amma idan ya wakilta wani ya yanka masa babu  komai.  Dalili kuwa shine Hadisin Anas Ibn Malik (R.A) cewa: "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yanka Raguna guda biyu da hannunsa mai albarka, a matsayin layyar sa, wadanda su ke da launin fari tas, kuma masu kaho biyu.  Sayyindina Anas (R.A) yace: "Na ganshi ya yanka su da hannunsa. A lokacin da zai  yanka sai ya ambachi sunan Allah Ta’ala ,kuma Ya Girmama Shi  … (watau yace: Bismillahi Allahu Akbar). Dalili na biyu kuma hadisin da ya tabbata acikin a cikin Sahih Muslim cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi WasallamYa yanka abin hadayarsa guda dari, sai Ya yanka sittin da uku da hannunsa mai albarka, sannan ya wakilta sayyindina Ali (R.A) ya karasa sauran (watau talatin da bakwai) . Haka  Kuma Abu Musal-Ash'ari ya umarci '`ya'yan sa mata da su yanka abin layyar su da hannunsu .
 Wannan hadisi na Abu Musal-Ash'ari yana kwadaitar damu cewa; Ya halatta mata ma su yanka abin layyar su da hannun su idan zasu iya, idan kuwa ba za su iya ba, babu laifi su wakilta wani ya yanka musu a mai makon su. 
Hakika wakili bashi da wani kaso na musamman da shari’a ta tanadar masa daga cikin naman layya, ko da kuwa da sunan ladan wakilci ne (kamar yadda a wasu guraren ake bada makogwaro ko kai da kafafuwa da makamantan su a matsayin ladan yanka).  Haka shima mahauci, ba a bashi wani kaso daga naman layyar a matsayin ladan aikin sa.  Sai dai a biya shi da kudi a matsayin ladan aikinsa.  Saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Ya hana a bai wa mahauci wani kaso daga naman layya, a matsayin ladan aikin sa.  Dalili kuwa shine hadisi ya tabbata daga Sayyidina Ali (R.A) yace: "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umarce ni da na raba naman hadayar Sa, da fatar baki daya, da  akalar rakuman ga fakirai da talakawa sadaka,  amma kada a bai wa mahaucin daya yi aikin fidar  wani kaso daga ciki, amatsayin ladan sa. Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Ya kara da cewa mu zamu bashi daga wajen mu" .
13. Tambaya:  Shin ya halatta mutane su yi tarayya a kan dabbar layya guda daya?
Amsa: Na'am, hakika ya halatta mutane su yi tarayya akan dabbar layya guda daya. Domin kuwa ya tabbata cewa: Mutane bakwai za su iya haduwa akan rakumi ko Sa da niyyar shi ne abin layyar su, saboda hadisin da aka karbo daga Jabir bin Abdillah (RA) yace: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umarce mu a shekarar da aka yi yarjejeniyar Hudaibiyyah cewa kowane mutum bakwai daga cikin mu, za su iya yin tarayya akan rakumi guda ko sa a matsayin hadayar su" . Dalili na biyu kuma shine hadisin daya tabbata daga Ibnu Abbas (RA) yace: "Mun kasance tare da Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) a cikin tafiya, sai layya ta same mu (wato babbar salla) sai muka hadu mu goma a kan rakumi daya, kuma muka hadu mu bakwai a kan sa guda daya" .
Amma mutane ba za su hadu akan Rago, Tunkiya, Akuya ko dan akuya ba, sai dai magidanci zai iya tarayya da iyalan sa a cikin ladan, sai dai ba a matsayin kamar kowa ya yanka ba ne. Dalili kuwa shine: hadisin daya tabbata daga Ada'u bin Yasar  yace: "Na tambayi Abu Ayyubal Ansari (R.A) cewa ya ya layya ta ke a zamanin Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) "? Sai yace:  Mun  kasance a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) mutum zai yanka rago ko dan akuya da niyyar neman ladan kansa da iyalan gidan sa , sai su ci daga cikin naman, sauran kuma su bayar  sadaka" ..
Kuma a cikin wani hadisin wanda ya tabbata daga Nana Aisha (R.A) cewa: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yanka abin layyar sa, a lokacin da zai yi yankan sai yace: 
"?????? ?????? ?????????? ???????? ???? ????????? ????? ?????????? ?????? ??????? ?????????"
"Bismillahi Ya Ubangiji ka karba daga Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) da iyalan Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam da al'ummar  Muhammad" .
 Saboda haka wannan hadisi idan a ka  lura za a ga cewa an sanya iyali ne  a cikin niyyar  lada, domin su ma su sami ladan, amma ba yana nufin kamar  suma sun yi  yanka bane. A kan haka Imam Malik da Imam Ahmad da Ishak bin Rahawaihi suka tafi, kamar yadda Imam Tirmizi ya ciro a cikin littafin sa babin layya, hadisi na (1557).
14. Tambaya:  Shin watanda (kakkawa) layya ce, kuma menene hukuncin ta?
Amsa: Hakikanin gaskiya watanda ba layya ba ce. Saboda ita layya ana tarayya ne akan sa ko rakumi da adadin mutanen da basu wuce bakwai ba akan sa, ko goma akan rakumi. Ita kuma watanda akan sami akalla sama da mutane goma sha biyar akan sa daya. Kuma su kansu masu yin watanda suna yi ne da manufar taimakawa junan su, wajen canja miya. Watau ya zama sun sami canjin dandanon miyar da ba su saba ci yau da gobe ba, a ranar Sallah. Saboda naman miya yana da matukar tsada a dai-dai  wannan lokaci, shi ya sa wasu mutane su ke haduwa domin nema wa kan su sauki. Saboda haka naman watanda, naman miya ne kawai.
Haka kuma zai zame wa mutane bakwai alheri idan za su rika haduwa suna yin layya da sa ko rakumi. Domin samun ladan layya yafi musu watandar da suka yi domin miyar ranar idi.
15. Tambaya:  Shin hukuncin layya ya takaita ne akan magidanci kawai ko kuwa ya shafi kowa da kowa?
Amsa: Layya dai ba ta takaita akan magidanci kawai ba. Saboda layya Ibada ce da ta shafi kowa da kowa, yaro da babba, mace da namiji, mai aure da mara aure, matukar dai a kwai ikon yin ta.
Domin an karanta a baya cewa; Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yanka layyar sa, ya fada yace: "Allah ka karbawa Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) da iyalan Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) da al'ummar sa". Saboda haka wannan ya nuna cewa, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam ) ya hada kowa da kowa wajen samun lada, ba tare da togaciya ba,  ina kuma ga wanda ya samu iko?
Dalili na biyu kuma shine, hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa:
"?????????? ???????? ????? ????? ????? ?????? ?????? ??? ????? ????? ???????????..."
 "Layya tana kan kowanne magidanci da iyalan gidan sa kuma ko wacce Shekara" .
16. Tambaya:  Shin ya halatta Matar aure da take da hali ta yi layya? ko kuwa zata wadatu ne da layyar mijinta?
Amsa: Hakika ya kamata matar aure, mai hali ta yi layya da kanta, kada ta dogara da ta mijinta. Saboda sunnar Manzon Allah ce wadda ta shafi kowa da kowa. Kuma hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (RA) yace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: "Duk wanda Allah Ya bashi damar yin layya, bai yi ba kada ya kusanci filin idin mu" .
Idan aka lura za a ga cewa Annabi  (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi amfani da lafazin "kowa da kowa" bai kebe wani jinsi ba. Haka kuma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umarci Ummu Adiyya da sauran mata da su fito da mata zuwa sallar idi,  ko da kuwa suna cikin jinin al'ada ne, sai dai ba za su kusanci wajen yin sallar ba, za su je ne kawai, domin su shaida alkhairin wannan ranar da  kuma addu'oin musulmi . 
Domin haka wacce take da hali amma bata yi ba tana cikin wadanda za'a hana su zuwa masallaci  kamar yadda hadisi ya gabata.
 
17. Tambaya:  Shin ko ya halatta a yi wa mamaci layya?
Amsa: Hakika Layya Ibada ce, wacce Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kwadaitar da al'ummarsa yinta. Kuma  Shima da kansa ya aikata, sahabbai ma sun yi layya, amma ba a taba jin ya yiwa Nana Khadija matar sa ko Hamza Baffan sa ko kuma wadansu `yan uwan sa da suka mutu acikin musulunci ba.  Amma idan mutum ya yi layyar sa yace Allah Ya kai ladar ga iyayen sa ko dan ginsa da suka mutu babu laifi. Dalili kuwa shi ne, wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yace:  "Mahaifiyata ta rasu, amma ba ta sami damar yin wasicci ba. Kuma ina zaton da ta sami damar yin magana, da ta ba da umarnin ayi mata sadaka. Shin tana da lada idan na yi ma ta sadaka? Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yace: "Na'am." (watau ta na da lada) . Dalili na biyu shine wani hadisi da Sheikh Albani ya inganta shi a cikin Sahih Sunan Al-Tirmizi wanda yayi tahkikin sa, inda aka ruwaito cewa Sayyidina Ali (RA) ya kasance yana yin layya da rago biyu, daya nasa, dayan kuwa na Manzon Allah (??? ???? ???? ?????), sai aka tambayeshi dalilin yin haka, sai yace: "Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) ne ya umarceni kuma bazan bari ba fau-fau .
18. Tambaya:  Menene hukuncin wanda ya cinye naman layyar sa baki daya, bai bada sadaka ba?
Amsa: Duk wanda ya cinye naman layyar sa ba tare da ya ba da sadaka ba, ya sabawa umarnin Allah da sunnar Manzon Allah (??? ???? ???? ?????), da kuma aikin magabata na kwarai. Ana yin layya ne domin neman kusanci da Allah ta hanyar bada sadaka da yalwatawa fakirai a wannan ranaku masu alfarma. Saboda fadin sa madaukakin sarki:
((???????? ??????? ???????????? ?????????? ??????????)) [???? ????: 28]
Ma'ana: "… kuci daga cikinta, kuma ku ciyar da mabukata, fakirai…"[Hajji=28].
Haka Kuma An karbo daga Sayyadina Aliyyu (R.A) yace: "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umarce ni, da na raba naman hadayar sa da akalar da fatar ga fakirai…" .
Amma wannan bai hana mutum ya kyautatawa makwabtan sa da yan uwan sa da sauran musulmi wadanda suke da wadata ba.  Abin mamaki shi ne, wasu lokuta sai aga  mawadata sun yanka shanu da raguna, wasu ma har da rakuma, amma abin takaici sai dai makwabta da sauran fakirai su ji kanshi na tashi. Hakika irin wadannan Mutane wajibi ne suji tsoron Allah su canza halayen su, kuma su kyautatawa wadanda basu dashi domin ko ba komai akwai hakkin makwabtaka. Muna fatan Allah Ta’ala Ya shiryi irin wadannan mutanen, Amin.
19. Tambaya:  Menene hukuncin wanda ya sayar da fatar dabbar layyar sa?
Amsa: Bai halatta ga wanda ya yi layya ya sayar da wani sa shi na abin layyar sa ba.  Haka Kuma ba za'a ba mahauci fata a maimakon ladan sa na fida ba. Fatar layya ana bayar da ita ne sadaka ga wanda Allah Ya nufa aka baiwa. Domin mutum yana iya baiwa matar sa ko ‘ya’yan sa sadaka.  Kuma shi kan sa ya na iya yin amfani da ita ta wata hanyar, amma ba a yarda ya sayar ba. Dalili kuwa shi ne; Hadisin Sayyidina Ali(R.A) daya gabata.
20. Tambaya:  Muna ganin ana wanke dabbar layya, shin yana da asali a shari'a ko aikin magabata na kwarai?
Amsa: Wanke dabbar layya ba ya cikin koyarwa irin ta Manzon Allah (??? ???? ???? ?????), haka kuma magabata na kwarai.  Saboda haka tunda ya rasa asali daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da magabata na kwarai, ya zama kagaggen aiki kenan, (watau yin hakan Bidi'a ce kawai).  Sai dai idan bukatar hakan ta kama saboda dauda ko annakiya babu laifi.
21. Tambaya:  Wadan su basa wanke naman layyar su yayin da zasu dafa, shin aikata haka yana daga cikin aikin magabata na kwarai?
Amsa: Babu wani dalili a cikin littafin Allah ko sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ko aikin magabata na kwarai da ya nuna ba'a wanke naman layya. Yin hakan al'ada ce kawai mutane  suka kago.
22. Tambaya:  Shin wanda Allah bai hore masa abin layya ba, ko abin suna, zai iya yanka kasa ko tuwo, kamar yadda wasu mutane suke yi a yanzu?
Amsa: A gaskiya yanka kasa ko tuwo a maimakon abin layya ko suna,  yayin da aka rasa abin layya bashi da wani dalili, al'ada ce kawai da wasu mutane suke aikatawa. Saboda haka zai yi kyau ga masoya Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) da su rika daurewa suna tambayar yadda Annabi (??? ???? ???? ?????) ya aikata wani aiki, kafin su yi tunanin kansu. Hakika yin koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam shi ne nuna kauna da soyayya gareshi
23. Tambaya:  Shin idan mutum ya fara yin layya, ta lazimce shi kenan, ko da kuwa bai samu hali ba wata shekarar?
Amsa: Layya dai sunna ce ga wanda Allah Ya bashi iko. Saboda haka layya ta na wajaba ne kawai idan da halin yin ta. Domin  Allah Madaukakin Sarki yace:
((?????????? ????? ??? ?????????????)) [???????: 16]
Ma'ana "Kuji tsoron Allah dai dai gwargwado" (Tagabun. 16)
24. Tambaya:  Menene hukuncin wadanda suke yin bara ko roko ko maula domin su sami abin layya?
Amsa: Bai halatta ga mutum ya yi bara ko roko ko maula ba. Domin yin haka ya sabawa sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) kamar yadda ya tabbata a hadisin kabisa Alhilali yace: “Manzon Allah Sallallahu alaihi WasallamYa hana yin bara, ko roko ko maula, face ga mutum uku kawai …" .  Wanda mai neman abin layya baya daga cikinsu.  Domin ita layya Ibada ce, a Ibada kuwa Allah baya kallafawa bawansa abinda bawa ba zai iya ba.
25. Tambaya:  Muna ganin mutane suna ajiye jelar dabbar layyar su har zuwa watan cika-ciki, shin haka yana da asali cikin addini ne, ko kuwa al'ada ce mara tushe?
Amsa: Ajiye jelar dabbar layya, sai wani lokaci ba shi da asali daga Sunnar Manzon Allah (??? ???? ???? ?????), Haka kuma yin hakan ba aikin magabata na kwarai ba ne. Yin haka al'ada ce kawai wadda bata da tushe ko asali a shari'a.
26. Tambaya:  Shin mala'iku suna sanya  albarka a naman layya, idan aka ajiye shi kwana daya ko biyu ko uku kamar yadda ake cewa?
Amsa: Wannan da'awa ce da ba ta da wani dalili kai tsaye daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ko kuma aikin magabata na kwarai. Saboda haka irin wannan  ita ma al'adace kawai. Amma idan mutum ya ajiyeshi ne domin ya sami sukunin rabawa a hankali ba tare da riya cewa mala'iku zasu sa masa albarka ba, wannan ba zai zama laifi ba.
27. Tambaya:  Wadanne sunnoni ne da mustahabbai mai tafiya masallacin Idi zai aikata yayin tafiyar sa?
Amsa: Abinda ya kamata a sunnace Musulmi ya yi lokacin tafiya masallacin idi shi ne:  abinda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yayi a lokacin da Ya ke tafiya masallacin idi. Ya kasance Sallallahu alaihi Wasallam yana koya mana maimaita kabbara da hailala a lokacin tafiya masallacin idi kamar haka:
• Allahu Akbar, Allahu Akbar,
• La'ilaha illallah Allahu Akbar, Allahu Akbar, walillahil hamd.
• Allahu Akbar kabiran, walhamdulillahi kasiran, wa subhanallahi bukratan wa'asilah,
• La'ilaha illallah, wala na'abudu illa iyah mukhlisina lahuddin walaukarihal kafirun.  WaSallallahu ala nabiyyina Muhammad wa'ala alihi wasahbihi wasallam tasliman kathira.
Haka mutum zai ta maimaitawa, har ya isa masallacin idi. Idan ya isa masallacin kuma, ba zai daina yin irin wannan kabbarar da Hailalar ba, har sai liman ya fito. Bayan idar da Sallah, kuma yana da kyau mutum ya tsaya ya saurari huduba.  Daga nan kuma sai mutum ya dawo gida yana kara maimaita irin wadannan kabbarori. Haka kuma Yana daga cikin sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa, mutum ya canja wata hanya idan zai koma gida.
 Wadannan kabbarori za a ci gaba da yin su bayan kowacce sallar farilla tun daga Azahar ta ranar Sallah har zuwa Asubar din karshen kwanakin Mina, watau 13 ga watan Zulhijja.
 Yana da matukar muhimmanci idan aka sauko daga masallacin Idi ayi wa juna barka da addu'ar Allah ya karba mana, Allah ya maimaita mana kamar yadda magabata na kwarai suke yiwa junan su. Idan ya kama a ziyarci `yan uwa da abokan arziki, domin sadar da zumunci, yin hakan yana da kyau. Babu laifi ga mata da kananan yara su nuna farin cikin su, saboda ni'imar da Allah yayi musu a wannan rana, kamar yin gada, kidan kwarya, shantu, ko wakoki wadanda babu batsa a cikin su, ba tare da cudanya da maza ba. Domin hadisi ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari da Muslim cewa Nana Aisha (R.A) da wasu kuyangi guda biyu sun kasance suna wakoki na nuna farin ciki, da ambaton irin ni'imomin da Allah ya yiwa al'ummar Manzon Allah (??? ???? ???? ?????), kuma Annabi (??? ???? ???? ?????) yana ganin su bai hana suba .
 Haka nan maza suma zasu iya warewa su nuna nasu farin cikin, kamar yadda mutanen Habasha suka yi a zamanin Manzon Allah (??? ???? ???? ?????) inda suka hadu suna wasanni na nuna dabarun yaki da tsalle-tsalle wandanda basu sabawa shari'a ba, kuma Annabi (??? ???? ???? ?????) bai hana su ba .
NASIHA
A nan muna nasiha da jan hankali ga `yan uwan mu Musulmi dangane da irin abubuwan da wasu suke yi a yayin bukukuwan Sallah, wanda ya sabawa koyarwa irin ta addinin Musulunci, kamar:
Wakoki irin na Indiya, da kade-kade irin na Turawa da fito da tsiraici, da cakudedeniya tsakanin maza da mata. Wadannan duk basu dace da koyarwa irin ta shari'a ba.
Haka nan halartar wuraren da ake fitsara, da rashin kunya, da shaye-shayen kwayoyi, wani lokacin ma hard a giya, da zinace-zinace. Wanda wannan fito-na-fito ne da Allah, da sabawa umarninSa. Saboda haka muna kira ga shugabanni da su dauki tsauraran matakai a kan irin wadannan abubuwa, ba tare da jin tsoro ko zargin mai zargi ba. Domin shiriyar al'ummar su shine zaman lafiyar su.
Muna rokon Allah Mai Girma da daukaka ya shiye mu da shugabannin mud a matasan mu baki daya.
Wannan shine abinda Allah Ta’ala Ya kaddara mana rubutawa a wannan dan littafi, game da bayani akan abinda ya shafi layya, da sallar idi. Muna fatan Allah Ya karba mana. Allah Ya sa wannan dan littafi ya amfane mu duniya da lahira.  Allah kuma ya karbi Ibadarmu Amin.
Fasubhanaka la ilma lana, illa ma allamtana, innaka antal alimul hakim. subhanakallahumma wabihamdika, nash hadu an la ilaha illa anta, nastagfiruKa, wana tubu ilaika..
WaSallallahu alannabiyina Muhammadin wa alihi wasahbihi wasallam.
  AbdulWahab Abdallah